NCN Hausa

NCN Hausa VOICE OF THE NORTH

16/07/2026

Hon. Mustapha Bala Dawakin Kudu ya samarwa sama da matasa 500 aiki a KH D/kudu da warawa-Anas Abdu Gogel

Da Dumi-Dumi...Hukumar Hisbah a Kano ta haramta sana'ar tura finafinai ta 'download' a duk fadin jiharMataimakin Kwamand...
16/07/2026

Da Dumi-Dumi...
Hukumar Hisbah a Kano ta haramta sana'ar tura finafinai ta 'download' a duk fadin jihar

Mataimakin Kwamandan Hisbah a jihar Dr Mujahid Aminuddeen ya sanar da cewa hukumar ta dauki wannan matakin ne saboda ta gano yadda wasu masu sana'ar suke taimaka wajen yada faya-fayan bidiyon batsa da hakan ke yin lahani ga tarbiyyar matasa.

Ɗan Majalisar wakilan Nijeriya Yusuf Gagdi ya soki tsarin gyaran hali ga tubabbun masu tada kayar baya, yace kawar da su...
06/07/2026

Ɗan Majalisar wakilan Nijeriya Yusuf Gagdi ya soki tsarin gyaran hali ga tubabbun masu tada kayar baya, yace kawar da su ne dai-dai

Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Pankshin/Kanke/Kanam a Jihar Plateau, Yusuf Gagdi, ya bayyana adawarsa da shirin gyaran hali da sake mayar da masu tada kayar baya da sauran masu aikata manyan laifuka cikin al'umma, yana mai cewa duk wanda ya hallaka wani da gangan kamata yayi a yanke masa hukuncin kawar dashi daga duniya.

Gagdi ya ce mutanen da kotu ta samu da laifin ajalin wasu ya kamata a zartar musu da hukunci maimakon a yi musu gyaran hali, kamar yadda Jaridar Daily trust ta ruwaito.

A cewarsa bai dace a rika kashe kuɗaɗen jama'a wajen gyaran halin mutanen da ake zargi ko aka samu da laifin hallaka bayin Allah marasa laifi ba, yana mai cewa irin wannan tsari tauye adalci ne kuma ba ya hana aikata laifuka.

Jagoran Kwankwasiyya Sanata Kwankwaso ya sauka a jihar Kano ya juma’a.
03/07/2026

Jagoran Kwankwasiyya Sanata Kwankwaso ya sauka a jihar Kano ya juma’a.

FAGEN WASANNI...Kasar Portugal takai matakin zagayen 'yan 16 a gasar cin kofin duniya da ake gabatarwa na shekarar da mu...
03/07/2026

FAGEN WASANNI...

Kasar Portugal takai matakin zagayen 'yan 16 a gasar cin kofin duniya da ake gabatarwa na shekarar da muke ciki.

Ƙungiyar Amnesty International a Najeriya ta zargi gwamnatin shugaba Tinubu da gaza kare ƴan Najeriya daga matsaloli na ...
02/07/2026

Ƙungiyar Amnesty International a Najeriya ta zargi gwamnatin shugaba Tinubu da gaza kare ƴan Najeriya daga matsaloli na ta’addanci da na tattalin arziki da ake fama da shi.

Da Dumi-Dumi...Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutum miliyan 17 ne suke fuskantar matsananciyar ...
02/07/2026

Da Dumi-Dumi...

Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutum miliyan 17 ne suke fuskantar matsananciyar yunwa a faɗin jihohin arewacin ƙasar tara, tana mai gargaɗin cewa rikici da janye tallafi na sa wa matsalar abinci ta yi munin da ba ta taɓa kai wa ba a kusan shekaru 10 da s**a gabata.

Jaridar Trt Arfica Hausa ta rawaito cewa "nazarin baya bayan nan a kan matsalar ƙarancin abincin ya nuna yawan mutanen da ke fusknatar matsalar, da yanayin gaggawa da ake ciki da yadda waɗanda ke cikin matsananciyar yunwa s**a ƙaru da kusan miliyan biyu idan aka kwatanta da hasashen da aka yi na baya, in ji hukumar ta WFP a wata sanarwa."

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da halaccin shugabancin Sanata David Mark a jam'iyyar ADC, tare da yin wats...
02/07/2026

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da halaccin shugabancin Sanata David Mark a jam'iyyar ADC, tare da yin watsi da ƙarar ɗan Majalisar Wakilai, Leke Abejide, da ya ƙalubalanci naɗin Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakataren jam'iyyar na ƙasa.

Mai shari'a Musa Liman ya ce kotun ba ta da hurumin shiga harkokin cikin gida na jam'iyya, sannan ya bayyana cewa Abejide bai nuna cewa an tauye masa wata doka ko haƙƙi ba, kuma bai fara amfani da hanyoyin sasanta rikici na cikin jam'iyyar ba kafin ya garzaya kotu.

Kotun ta kuma yanke cewa miƙa shugabancin jam'iyyar daga Ralph Nwosu zuwa David Mark bai saɓa wa kundin tsarin mulkin ADC ba, tare da tabbatar da cewa zaɓen Mark da Aregbesola ya gudana bisa tanadin kundin tsarin mulkin jam'iyyar, Dokar Zaɓe ta 2026 da kuma sa ido na hukumar INEC.

Haka kuma, kotun ta umarci Abejide ya biya tarar Naira miliyan biyu ga kowane ɗaya daga cikin waɗanda ake ƙara, sannan ta ci tarar lauyansa Naira miliyan 10 bisa tanadin Dokar Zaɓe ta 2026.

Idan kana maganar wa ye shugaban Gandujiyya a Kano ai Gwamna Abba ne a wurin mu~Sanata Kwankwaso
01/07/2026

Idan kana maganar wa ye shugaban Gandujiyya a Kano ai Gwamna Abba ne a wurin mu
~Sanata Kwankwaso

Majalisar Kano tayi karatu na biyu kan sabuwar dokar masarautar jiharMajalisar Dokokin Jihar Kano ta yi karatu na biyu a...
01/07/2026

Majalisar Kano tayi karatu na biyu kan sabuwar dokar masarautar jihar

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi karatu na biyu a ƙudirin dokar kafa Hukumar Majalisar Masarautun Jihar Kano, wadda ake sa ran za ta haɗa dukkan masarautun jihar ƙarƙashin tsari guda.

Majiyar mu ta rawaito cewa idan ƙudirin ya zama doka, Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ne zai jagoranci hukumar tare da haɗin gwiwar Sarakunan Gaya, Ƙaraye da Rano.

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Lawan Hussaini Dala, ya ce rage wa masarautun gargajiya iko a baya na daga cikin abubuwan da s**a taimaka wajen taɓarɓarewar harkokin tsaro a jihar.

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when NCN Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to NCN Hausa:

Shortcuts

Share