LESMA TV HAUSA

LESMA TV HAUSA Labarai da Rahotanni cikin Aminci, Gaskiya Daidaito Cikin Kwarewa da Sanin Makamar Aikin Jarida
TEL : 08082080123 E-MAIL: [email protected]

Yan bindiga sun sace Malamai 6 daga cikin malaman da s**a halarci taron yiwa Shugaba Tinubu addu'ar tazarce da gwamna aj...
13/09/2026

Yan bindiga sun sace Malamai 6 daga cikin malaman da s**a halarci taron yiwa Shugaba Tinubu addu'ar tazarce da gwamna ajihar zamfara, a hanyar dawowarsu daga wajen da aka gudanar da taron.

Me zakuce?

A bayanan da ya wallafa Cikin harshen turanci, Ɗanbilki Kwamanda yace an kai masa harin ne a kusa da sabuwar Jami'ar Bay...
12/09/2026

A bayanan da ya wallafa Cikin harshen turanci, Ɗanbilki Kwamanda yace an kai masa harin ne a kusa da sabuwar Jami'ar Bayero da ke birnin Kano.

Mezakuce?

“Babu Wani Ɗan Siyasa Da Zai Iya Yaƙar Kwankwaso A Kano” — Sanata Victor UmehSanata Victor Umeh ya bayyana cewa, a halin...
12/09/2026

“Babu Wani Ɗan Siyasa Da Zai Iya Yaƙar Kwankwaso A Kano” — Sanata Victor Umeh

Sanata Victor Umeh ya bayyana cewa, a halin yanzu, babu wani ɗan siyasa da zai iya fuskantar ko fafatawa da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, a fagen siyasar Kano.

Sanatan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan tasirin Kwankwaso da kuma irin karfin da yake da shi a siyasar jihar Kano.

’uMusaKwankwaso

Ɗan Takarar Majalisar Wakilai a Karamar Hukumar Nassarawa Mustapha Alkassim Danhajiya,Ya Kai Ziyarar Girmamawa Ga Dakta ...
11/09/2026

Ɗan Takarar Majalisar Wakilai a Karamar Hukumar Nassarawa Mustapha Alkassim Danhajiya,Ya Kai Ziyarar Girmamawa Ga Dakta Nasiru Yusuf Gawuna.

Ɗan Takarar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Nassarawa, Hon. Mustafa Alkassim Ɗan Hajiya, ya kai ziyarar girmamawa ga Mai Girma Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, Ɗan Takarar Sanatan Kano ta Tsakiya.

Ziyarar ta kasance wata dama ta tattaunawa da musayar ra’ayoyi kan al’amuran siyasa da kuma ƙarfafa haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar NDC a jihar

Tawagar Sanatoci Ta Ziyarci Sarkin Gumel Domin Ta’aziyyaTawagar sanatocin Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shug...
11/09/2026

Tawagar Sanatoci Ta Ziyarci Sarkin Gumel Domin Ta’aziyya

Tawagar sanatocin Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ta ziyarci Mai Martaba Sarkin Gumel, Dakta Lawan Ahmad Muhammad Sani III, domin miƙa saƙon ta’aziyya bisa rasuwar Mai Martaba Sarkin Gumel na baya, Alhaji Ahmad Muhammad Sani.

Tawagar ta kuma taya Mai Martaba Sarkin Gumel murnar hawa karagar mulkin masarautar, tare da yi masa fatan samun nasara da zaman lafiya wajen gudanar da al’amuran masarautar.

ƊAN TAKARAR MAJALISAR JIHAR KANO YA RABA MASHINA 5 GA SHUGABANNIN NDC A DORAYIƊan takarar Majalisar Jiha mai wakiltar Ƙa...
11/09/2026

ƊAN TAKARAR MAJALISAR JIHAR KANO YA RABA MASHINA 5 GA SHUGABANNIN NDC A DORAYI

Ɗan takarar Majalisar Jiha mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Gwale, Aminu Abdullahi Warkal, ya rabawa shugabannin Jam’iyyar NDC na Mazabar Dorayi mashina guda biyar (5).

Rabon mashinan na daga cikin ƙoƙarin ɗan takarar na tallafa wa shugabannin jam’iyyar tare da ƙarfafa harkokin jam’iyya a matakin mazaba.

An gudanar da rabon ne a Dorayi, inda shugabannin jam’iyyar s**a karɓi mashinan tare da bayyana godiyarsu ga Aminu Abdullahi Warkal bisa wannan tallafi.

Wani Mai bincike da hasashe kan siyasar Najeriya ya yi ikirarin cewa kusan kashi 85% na ’yan Arewa na karkata wajen zaɓe...
10/09/2026

Wani Mai bincike da hasashe kan siyasar Najeriya ya yi ikirarin cewa kusan kashi 85% na ’yan Arewa na karkata wajen zaɓen tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Rahoton ya ce matsalar tsaro, rashin aikin yi, tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki na daga cikin manyan dalilan da ke sa wasu daga cikin masu zaɓe a yankin karkata ga Atiku.

Haka kuma, rahoton ya danganta wannan ƙarin goyon baya da alƙawarin Atiku na dawo da tallafin man fetur idan ya samu nasarar lashe zaɓen 2027.

Me zakuce?

Wannan tafiya mun shige ta tsakani da Allah da kuma mutumtaka.Bamu da wani tunani sai abinda Allah yayi ~ Dakta Nasiru Y...
09/09/2026

Wannan tafiya mun shige ta tsakani da Allah da kuma mutumtaka.

Bamu da wani tunani sai abinda Allah yayi

~ Dakta Nasiru Yusuf Gawuna

Shugaban majalisar Dattawa Nigeria Sanata Godswill Akpabio yace muddin 'yan Nigeria s**a bari Shugaba Tinubu ya fadi tab...
09/09/2026

Shugaban majalisar Dattawa Nigeria Sanata Godswill Akpabio yace muddin 'yan Nigeria s**a bari Shugaba Tinubu ya fadi tabbas sune zasu sha wuya

Me zaku ce ?

Atiku Ya Gana da ‘Yan Takarar Gwamnoni na ADC a Arewa Maso Yamma.Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugab...
09/09/2026

Atiku Ya Gana da ‘Yan Takarar Gwamnoni na ADC a Arewa Maso Yamma.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC Atiku Abubakar, ya gudanar da wata ganawar sirri da ‘yan takarar gwamnonin jam’iyyar na yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa ganawar na daga cikin shirye-shiryen ƙarfafa tsarin jam’iyyar da kuma shirya tsaf domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Ana kallon wannan zama a matsayin wani mataki na haɗa kai da tsara dabarun siyasa a yankin, yayin da jam’iyyun siyasa ke ƙara mayar da hankali kan shirin neman goyon baya gabanin zaɓen ƙasa mai zuwa.

Sai dai ba a bayyana cikakkun bayanai kan abubuwan da aka tattauna a ganawar ba, ko kuma ko an fitar da wata sanarwa a hukumance bayan kammalawarta.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when LESMA TV HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share