Usman Tukur journalist

Usman Tukur journalist Librarian,
Journalist,
Painter,
Truck Driver
Comrd

12/10/2024

Nasara tana tare ga masu haquri

YADDA MAMACI ZAI GANE SHI MATACCE NE,mamaci ba zai gane shi matacce ba ne a karon farko, saboda abun zai masa kamar a ma...
12/04/2024

YADDA MAMACI ZAI GANE SHI MATACCE NE,

mamaci ba zai gane shi matacce ba ne a karon farko, saboda abun zai masa kamar a mafarki, zai ga yana kuka yana shure shure yana kaiwa da komowa har ya kai ga anamishi wanka, a kuma ɗaukeshi zuwa magabarta duk zai na ganin abun kamar a mafarki,

Bai yadda cewa ya zama gawa ba,
sai bayan an bun ne shi yanaji ana cewa kutura ƙasa ta ɓangaren can, ganan baiji ƙasa ba, ku kawo ɗanyan kasa ta bangarennan, a wannan lokacin zai ringa cewa mutane mai kuke kokarin yi ne,

Bayan kowa ya bar maƙabarta, anbarshi shi ka dai a cikin kasa, sai Allah yasa a dawo masa da ransa ya ɓude idon sa ya farka a cikin matattu,

Daga lokacin zai fara murna ya farka daga mummunan mafarki,

A Wannan lokacin sai ya godewa Allah
ya yi yun ƙurin miƙewa sai yaji ansuturtashi, an daddamkeshi da wata riga marar hannu, babu aljihu ba wuya, sai ya fara mamaki da tambaya a karon farko,

A ina nake haka? Ina ne nan? ba wutar lantarki, ba AC, ba fanka, an rufeni ta kowani ɓangare,

Mai na ke yi a nan ?

To a nan ne zai gane lallai yana cikin kasa,zai kuma tabbatar cewa lallai yanzu ba mafarki bane mutuwace ta gaskiya,

A wannan lokacin zai yi wani sauti mai karan gaske, yana kiran yan uwansa kamar yadda ya ke yi anan duniya
idan yana bukatar dauki

Zairinka kiran sunayen ƴan uwansa,
Amma zai ji babu mai amsa masa, to daga nan zai soma fahimtar cewa allah ne ka ɗai zai agaza masa, to a lokacin zai din ga fadan astagfirullah,

Allah natuba ka agaza mini kaji kaina,

Ya na furta haka a cikin tsoro mai tsanani,

Idan mutumin kirki ne a lokacin mala'iku biyu zasu bayyana a gareshi cikin kyakkyawan fuska, sai su tallafeshi s**e kwantarda hankalinka daga nan zai fara samun kyakkyawan agaji,

Jama'a mu tuba zuwa ga Allah, mu gyara ayyukan mu, musani cewa babu makawa sai mun riski mutuwa, ya Allah ka sa mu cika da imani

01/03/2023

Allah shi yake bada mulki ga wanda yaso, Allah kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shattima su zamo Alkhairi ga al-ummar Arewa da Najeriya baki daya.

Hakika naso mai girma wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar soyayya ta gaskiya tare da mishi fatan ya zama shugaban kasar Najeriya, amma Allah bai kaddari hakan ba.

Don wanda nike so bai zama shugaban kasa ba hakan ba zaisa na yiwa kasar mu bakar Addu'a ko yankin mu na Arewa ba. Saboda ban dauki siyasa ko a mutu ko ayi rai ba saboda ita siyasa ra'ayi ce wacce kowane dan kasa yana da damar yin nasa ra'ayin.

Hausawa s**a ce wanda aka yiwa haihuwa to wata rana dole a mishi mutuwa, ba kowane lokaci ake yin Nasara ba.

Ina taya Bola Ahmad Tinubu da Kashim Shattima murna, tare da Addu'ar Allah yasa suyi fiye da ayyukan Alkhairan da muke tunanin Atiku Abubakar zai yi.

Allah ya kawo mana karshen matsalar rashin tsaron da ya addabi yankinmu na Arewa dama kasar Najeriya baki daya. Duk mai niyyar tada fitina a kasar Allah kayi mana maganinshi.

Rubutawa ✍️
Comr Abba Sani Pantami
Marubuci, Mai Fashin Baki,
Dan Jarida Mai Yada Labarai A Kafofin Sada Zumunta.

01/03/2023

Erik ten Hag akalla yana son sanya hannu akan manyan 'yan wasa biyu a Manchester United a bazara, tare da Victor Osimhen da Mohammed Kudus na Ajax. [MEN]

Daga: [Usman Tukur]

01/03/2023

Kungiyar AA. Zaura Babies ta shirya tunkarar mahimman wasanni biyu anan gaba, kuma kungiyar ta bayyana sunayen yan wasanta da tayiwa rajista da su dawo daukar horo a Yau, ko.kuma su fuskanci doka mai tsanani, Domin babu karbar wani uzuri ga jerin 'yan wasanan:

Masu tsaron raga:

1- Ibrahim Veldes [GK]
2 Jadda (GK)
3 Mamud (GK)

4- Lurwanu Gaida
5- Yusuf Neymar
6- Abdullahi S Gandu
7- Kankiya
8- Halifa Karami
9- Umar Ghana
10- Umar Dan kolli
11- Suleman Brown
12- Yusuf officer
13- Idris Ja en
14- Yazid Ja en
15- Sahabi Chairman
16- Umar kurna
17- Madu Magashi
18- Abdullahi Getso
19- Inyasi chiwo
21- Musa Gero

Shugaban kungiyar AA. Zaura Babies, Kabiru Haruna Mahuta {KB Mikel Me Sallah} yana bukatar ganin dukkan wadannanan yan wasan a filin kungiyar.

Daga: Usman Tukur

01/03/2023

Kar ku yi tsammanin matata zata dawo Majalisar Dattawa. A'a Za ta zama mai dakina ne, cewar-Tinubu

28/02/2023

Ba nida masaniya akai, zamu jira INEC ta kammala sanar da sauran jihohi hudun sai ya yanke hukunci.

28/02/2023

Manchester City za ta yi kokarin siyan Mateo Kovacic idan ba za su iya cimma yarjejeniyar daukar Jude Bellingham a bazara mai zuwa ba, in ji Daily Mail.

Manchester City zata fita kasuwa domin sayo yan wasan da za su maye gurbin Ikay Gundogan da Bernardo Silva wanda Ake sa ran za su bar kungiyar zuwa Barcelona.

Daga: [Fagen Wasanni]

Send a message to learn more

Address

Kano

Telephone

+2347019120335

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Usman Tukur journalist posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Usman Tukur journalist:

Share