06/08/2025                                                                            
                                    
                                                                            
                                            Yadda Mahaifiyar Gwarzuwar Muƙabala Ta Duniya Ta Shiga Cikin Tarihi
Hajiya Fatima Umar Mairiga, mahaifiyar gwarzuwar muƙabala ta duniya, RUKAYYA MUHAMMAD FEMA, ta taka gagarumar rawa wajen tabbatar da nasarar diyar ta tun tana ƙarama. Hajiya Fatima ba wai kawai ta tsayu wajen tarbiyya da karfafa gwiwa ba, har ma ta rungumi addu’a a matsayin hanya mafi muhimmanci wajen ganin ɗiyarta ta cimma nasara a rayuwa.
Tun tana ƙarama, Rukayya da mahaifiyarta ke tashi cikin dare domin gabatar da Sallar Tahajjud, suna roƙon Allah ya azurta ta da ilimi mai amfani, hikima, da fasaha. Wannan kyakkyawar alaka da Allah da kuma tsantsar jajircewa ya kasance ginshikin nasarar da ta samu.
A cikin gagarumar gasa ta duniya – TeenEagle Global Finals 2025 da aka gudanar a birnin London, ƙasar Ingila, Rukayya, ‘yar shekara 15 daga Jihar Yobe, ta zama Gwarzuwar Duniya a Fannin Muƙabala (Debate).
Ta rinjayi dubban mahalarta daga ƙasashe fiye da 69, inda ta kayatar da alkalai da jama’a da irin kwarewar ta wajen fassarawa, gabatar da hujjoji cikin basira, da fahimtar manyan batutuwan duniya. Wannan nasara ba wai kawai ta tabbatar da ƙwarewar Rukayya ba ce, har ila yau alamar ci gaban matasa a Najeriya, musamman daga arewacin ƙasar.
Rukayya ta wakilci makarantar Nigerian Tulip International Colleges (NTIC) dake garin Potiskum a Jihar Yobe Kuma mallakin Gwamnatin Jihar Yobe , inda ta yi zarra a fagen da ke ɗaya daga cikin mafi ƙalubale a gasar. Abin alfahari ne cewa irin wannan hazaka ta fito daga yankin da a da, ana kallon sa da buƙatar karin kulawa a fannin ilimi.
Nasarar Rukayya ta zo ne a lokaci guda da ta Nafisa Abdullahi Aminu, wadda ita ma daga NTIC Yobe ce, wadda ta zama Gwarzuwar Duniya a Fannin Ƙwarewar Harshen Turanci a cikin wannan gasar. Wannan ya sa Yobe State ta samu lambar yabo sau biyu a cikin gasar da ta fi kowacce girma a fannin ilimi a duniya.
Wannan tarihi yana daga cikin abubuwan da za su ci gaba da tunawa da su a Najeriya – inda iyaye, makarantu, da gwamnati s**a haɗa hannu wajen gina matasa masu hangen nesa da kwazo.
HAUSA YOUNG TV