
02/02/2025
MATASAN AREWA SHUWAGABANNIN GOBE KO MABARATAN GOBE?
Professor Usman yusuf Katsina mutum ne da a yanzu ya shiga rukunin mutanen da za ka kalla ka kira su dattawa.
Sannan dole ka saka shi cikin rukunin dattawan da suke kaunar goben matasan Arewa ta yi kyau,saboda shi dai ya gina rayuwar sa mai inganci.
A shekarar 1982,wanda yayi dai-dai da Shekaru Arba'in da uku (43 years)kenan yau,ya gama digirin sa na farko a matsayin Likita(MBBS)daga Jami'ar Ahmed Bello University a Zaria.
A shekarar 1989 ya zama kwararren likitan yara(Consultant Paediatrician)
Yayi nasarar cin jarrabawar Scholarship a University of Liverpool a London inda yayi Postgraduate course dinsa a Tropical Medicine.
Daga nan ya koma Fred Hutchison Cancer research centre a Washington,US.
A shekarar 2000 ne ya zama Associate Professor.
A shekarar 2008 ne ya zama Full Professor a fannin ilimin halittar jini(Haematology)da kuma ilimin gano da magance cutar cancer(Oncology).
Yayi aiki a nahiyoyi(Continent)guda uku,Afrika,Turai da Arewacin Amurka.
Yanzu mai wannan matakan me yake nema a duniya?
Gida?
Abinci?
Muhalli? Ko
Riga?
Duk Allah ya bashi.
Gwamnatin Nigeria 🇳🇬 ce karkashin mulkin Buhari ta nemi da ya dawo gida ya bayar da gudunmawa a hukumar inshora ta lafiya(NATIONAL HEALTH INSURANCE SCHEME)NHIS.
Bayan dawowar sa ya fara aiki a matsayin Executive secretary na hukumar ta NHIS,sai ya fahimci kudaden da ake rabawa jihohi daga hukumar a matsayin inshora na lafiya ana tura su ne ta asusun wani tsohon Sanata,shi tsohon Sanatan shine zai rarrabawa jihohin da aka bawa wanann kudin bayan ya cire duk abinda s**a tsara shi da wasu azzalumai a kasar.
Da kuma wasu tarun badakala.
Professor Usman yusuf yace ba karkashin office din sa kuma akan idon sa za'ayi wannan ba.
Daga nan ya fara fuskantar barazana daga masu amfana da kudaden na inshora,har ta kai ga an dakatar da shi na tsawon wata goma sha daya,sannan hukumar ta ce ta kafa kwamitin bincike akan sa,bayan ya dawo bakin aiki takaddama taki karewa,daga karshe dai s**a yi nasarar korar sa daga ofishin Ministan lafiya,aka kaiwa Shugaban kasa ya saka hannu✍️.
Bayan korar sa da s**a yi daga hukumar ne ya dawo ya fara kiraye kirayen Nigeria tana cikin wani hali,Arewa mu farka,goben matasan su da ya'yan su ba ta da kyau a hannun mutanen can,a haka har gwamnatin Buhari ta shude.
Wannan gwamnatin ta zo ta jefa mutane cikin halin yunwa da ukuba,bai yi kasa a gwiwa ba ya cigaba da kiran ta cikin ilimintarwa,sai su ka dauke shi a matsayin makiyi wanda dole sai sun saka shi yayi shiru.
Cikin satin da muka yi bankwana da shi sai ga sanarwar cewa hukumar EFCC ta k**a Professor,mun kashe kunne mu ji laifin sa,sai aka ce ya bayar da wata kwangila ne ba bisa ka'ida ba a lokacin yana office din sa a matsayin Executive secretary na hukumar NHIS,kwangilar ta kudi Naira dubu dari bakwai da wasu ya'n kai,ba fa Miliyan dari bakwai ba.
Abin kuma da yafi kona min zuciya har nake wannan rubutun shine,matasan da Professor yake wannan rigimar a kansu,a cikin satin da aka k**a shi,a satin ne wani abin banza da sunan Tik toker wanda ni Wallahi summa tallahi ban ta6a sanin sa ko ganin hoton sa ba sai satin nan,shine matasan s**a shagala da batun wai yayi aure.
Prof yana can tsare a Kuje prison a dalilin halin da kuke ciki.
Duk Azabar nan dai mune da iyayen mu ake ganawa ita,babu wanda a gidan su zai bigi kirji yace kasar nan ana cikin kwanciyar hankali,amma ko a jikin ku.
Wannan ce ta sa nake kaunar mutanen kudu,domin yau da ace irin wannan mutumin na su ne aka k**a,to duk wata hukumar kula da hakkin dan Adam,hukumomin walwala da jin kai,International communities duk sai sun ji hakin da ake ciki.
Goben mu a hannun mutanen nan ba mai kyau ba ce,ni dai da ace Arewa riga ce,da tuni na cire ta na jefar na fara yawo tsirara tunda yanzun ma tsirara ake kallon mu.
🤦♂️✍️.