25/07/2025
KANA SO ƊAN ADAM YA DINGA GANIN DARAJAR KA???
1. Ka dinga yin magana kadan, ko a halittar dan adam kunne ne a bude, Baki a rufe yake sai an bude shi
2. Ka koyi cewa "A'a" idan kaga zaka matsawa kanka kan bukatar wani, daukar alkawari mai nauyi ke kawo sa6a alkawari
3. Kada ka dinga bada amsa da wuri idan an tambaye ka, ka ɗan dinga yin "Jimmm", kayi tunani, ita magana in ta fita bata dawowa
4. Kayi tunani kafin yanke hukunci, gaggawa aikin shaidan ne, Mai garaje yafi saurin yin tuntu6e
5. Kada ka yarda a yawaita ganinka a idan ba wajen aiki ko sana'ar ka ba, araha ke kawo tayin wulakanci, ka tsare mutumcin ka a wurin da kafi kima da daraja
7. Kada ka dinga gardama da kowa, har da abokin ka ko matar ka, yawan musu rashin daraja ne, musu na jawo kiyayya da raini
8. Ka dinga saka tufafi Masu Tsabta ko da kuwa tsofaffi ne. Shiga ta kamala itace dattaku, daga sutura ake fara gane martabar kowa
9. Kada ka dinga Saka baki akan kowane zance ko da kuwa an tambayeka, baki shike yanke wuya, ka da kayi karya ko kato6ara don ka huce haushi ka burge wani
10. Ka kware wajen iya wata sana'ar, sannan ka da ka zama Rago wajen neman halal, Wanda ya Mika hannu a gidan wani baya iya mike kafa... Maula da bani bani suna zubar da mutumci
11. Kada ka taba shan wani abu da zai gusar maka da hankali, maye masifa ne, Mai Shan kayan kari baya karewa lafiya
12. Ka da ka zama mai buduwar zuciya, biyewa sha'awa ke kawo fasikanci da aukawa tarkon zina, luwadi ko madigo... Wadda karshen su nadama ne da halaka a duniya da lahira