Northern Culture Hub

Northern Culture Hub Celebrating the rich culture, traditions, and stories of Northern Nigeria. Join the journey and stay connected with the heart of the North

From art, music, and food to inspiring people and events, we bring the best of Arewa to the world.

'Yan sanda a gabashin birnin El Marj sun k**a mata biyu bayan sace jaririya. Rahotanni sun ce an kwace jaririn daga maha...
26/04/2026

'Yan sanda a gabashin birnin El Marj sun k**a mata biyu bayan sace jaririya. Rahotanni sun ce an kwace jaririn daga mahaifiyarta jim kaɗan bayan haihuwa a wani asibiti da ke yankin.

Kadan Daga Cikin Rayuwar Bawa Jan-Gwarzo Bawa Jan-Gwarzo sarki ne da ya mulki masarautar Gobir daga shekarar 1777 zuwa s...
06/04/2026

Kadan Daga Cikin Rayuwar Bawa Jan-Gwarzo

Bawa Jan-Gwarzo sarki ne da ya mulki masarautar Gobir daga shekarar 1777 zuwa shekarar 1795.

Asalin sunansa Malam Umar, amma an fi saninsa da laƙabin Bawa Jan-gwarzo, lamarin da masana tarihi suke alaƙantawa da jajircewarsa wajen yaƙi da ƙoƙarin tabbatar da abin da ya dace.

Bawa Jan-Gwarzo ne sarkin Gobir na 55, "sunan mahaifinsa Malam Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Gobir Babari, wanda shi ne Sarkin Gobir na 53." Ba a iya tantance asalin ranar da aka haifi Sarki Bawa Jan-Gwarzo ba, "amma dai ya zama sarki ne bayan rasuwar mahaifinsa da shekara shida.

Sarkin ya yi mulki a garin Alƙalawa, wato babban birnin ƙasar Gobir a wancan lokacin. "Mahaifinsa Sarki Babari ne ya kafa garin. Asalin gonar hutawar Sarkin Zamfara ce a lokacin, amma Sarki Babari ya aura wata ƙanwar sarkin na Zamfara, sai sarkin ya mayar masa da garin a ƙarƙashin Gobir."

A garin ne Bawa Jan-Gwarzo ya rayu, ya yi sarauta, kuma a garin ya rasu, sannan aka binne shi.

"Amma yanzu garin ya zama kufai bayan da aka ci garin da yaƙi. Amma yanzu haka hukumar adana tarihi na yunƙurin mayar da shi garin tarihi mai muhimmanci.

Sarkin ya samu yabo daga mutanensa, "saboda ya kwatanta mulki na adalci. Ya yi amfani da diflomasiyya da haɗin kai wajen jawo wasu da zama lafiya da wasu ƙasashen, amma ya yi amfani da ƙarfin soja a wuraren da ake buƙatar hakan."

Ƙarin iko da tasirin da Gobir ya samu a lokacin mulkin Bawa ya ba shi damar zama kasar Hausa da ta ƙi aika haraji ga Daular Bornu, tana tabbatar da 'yancin kanta.

A rayuwar Bawa ta karshe ya ci nasara a kan Sarkin Katsina Agwaragi a wajejen 1795. Bawa ya mutu daga rauni kwanaki arba'in bayan yaƙin.

A lura ba hotonsa bane, kwatance ne kawai.

Marigayi Sarkin Kano (Sarkin Musulmi) Muhammadu RumfaCikakken sunan sa shi ne Muhammadu Rumfa ɗan Yaƙubi, sunan mahaifiy...
23/03/2026

Marigayi Sarkin Kano (Sarkin Musulmi) Muhammadu Rumfa

Cikakken sunan sa shi ne Muhammadu Rumfa ɗan Yaƙubi, sunan mahaifiyarsa Faɗimatu.

Muhammadu Rumfa nagartaccen mutum ne, adali, malami, wanda ba za a samu wani tamkarsa ba a cikin sha’anin mulkin Kano. Ya mulki Kano daga wuraren 1463 zuwa 1499, wato a ƙarni na goma sha biyar.

A cikin zamaninsa sharifai su ka zo Kano, wato su Muhammad Abdulkarim Al Maghili ko Abdurrahmani tare da jama’arsu.

An ce shi Shehu Al Maghili, Annabi Muhammad (SAWW) ne yazo masa a cikin barci, ya ce masa “Tashi ka tafi wajan yamma ka ƙarfafa Musulunci”. Da ya tashi daga bacci sai ya ɗebi ƙurar Madina ya zuba a sanho ya zo da ita ƙasar Hausa. Kowane gari ya shiga sai ya ɗebi ƙurarsa ya gauraya ta da ta Madina, sai ya ga ba su haɗu ba, sai ya wuce. Haka ya rinƙa yi har yazo kano, ya ɗebi ƙurarta ya gaurayata, sai yaga ta zamo abu ɗaya, sai yace “Wannan gari shi ne na gani cikin barcina” (amma akwai bambace-bambance masana tarihi akan haka wasu sun ce daga kasar Aljeriya ya tafi kano).

Al Maghili ya zauna a wani gari da ake kira Fanisau, wanda yake daf da kano, sannan ya aikewa sarkin Kano Muhammadu Rumfa buƙatarsa ta shiga birni. Sarki Rumfa ya tafi izuwa gareshi tare da jama’arsa irinsu Hantari, da Gemun dodo, da Gadangami, da Alfagi, da sauransu, ya taho dashi cikin birnin kano.

Al-Maghili ya zauna a kano ya ƙarfafa Musulunci cikin wannan gari. Shi ne yazo da littattafai masu yawa ya umarci Rumfa ya gina masallacin Juma'a. Da nan addini ya kara zauna daram a Kano, sai ya wallafa wani littafi mai suna ‘Taj al-din fi ma yajib ‘ala I-muluk’ wanda zai taimakawa Sarki Rumfa gudanar da sha’anin mulki bisa tafarkin Islama daga nan ya yi ƙaura zuwa Misira tare da barin Na’ibinsa mai suna Sidi Fari a Kano yana cigaba da karatar da mutane addini.

An ce Sarkin Kano Rumfa ya nemi Shehu Al Maghili yayi masa adduoi guda tara waɗanda ana ganin har yau suna da tasiri a Kano. Daga cikin adduoin; an roƙa masa cewa duk wanda yazo Kano har kuma ya samu arziki a Kano, to ya zauna a Kano ba tare da ya koma garinsu ba.

Sannan an roƙa masa cewa duk cikar da garin Kano zai yi ka da a sami yunwa. Wata addu’ar da aka yi masa itace duk wanda ya zo Kano dare ko rana to ya sami abincin da zai ci. Sarkin Kano Rumfa shi ne ya fara abu goma sha biyu a ƙasar Kano. (Madogara littafin Kano ta Dabo tunbin Giwa).

Shi ne ya gina gidan sarautar kano da har yau ake kiransa da suna GIDAN RUMFA.

Da shekara ta zagayo kuma ya faɗaɗa ganuwar birni tun daga ƙofar dagaci zuwa ƙofar Mata, zuwa ƙofar gyarta-wasa, zuwa ƙofar ƙawaye, zuwa ƙofar Na’isa, zuwa ƙofar kansakali.

Da wata shekarar ta sake zagayowa sai ya tare a sabon gidansa.

Haka kuma shine ya kafa kasuwar kurmi, shi ne ya fara dawakin zage domin yaƙi da Katsina.

Shi ne sarki na farko wanda ya fara kulle. Shi ne ya fara Tara-Ta-Kano da kakaki da figini da takalmin jimina.

Shi ne wanda ya fara bai wa Babanni sarauta; na farkon su Ɗan kusubi, da Ɗan jigawa, da Ɗan turbuna, da sarkin Gabas da sarkin Tudu da sarkun Ruwa da Ma'aji da sarkin Bai da sarkin ƙofa. Har gobe ana ambatar duk wanda za a naɗa sarkin kano da suna ‘Magajin Rumfa’.

A zamaninsa ƙasar kano ta yi yaki da ƙasar Katsina, wanda sai da aka shekara goma sha ɗaya ana fafatawa a tsakaninsu ba tare da ɗaya ta rinjayi ɗaya ba.

Sarki Muhammadu Rumfa ya sarauci Kano tsawon shekaru talatin da bakwai.

Ana masa kirari da ‘Balaraben sarki ya gyara ƙasa!’

Allah ya jikan maza. Babban malami kuma inginiyan gini. Shi ya zana kuma ya gina gidan Rumfa a Kano wato gidan sarkin Kano na yanzu wanda hatta turawan
Ingila sunyi mamakin wannan tsarin gidan da fadin sa da kuma kwarewa wajen daidaita lissafin ginin. Rumfa ya gaji wannan fasaha da basira wajen kakaninsa Hausawa da s**a fito daga daular Kusch bayan rushewar misran fir'auna.

Muhammad cises

Trump ya dage kai hare-haren soji kan tashoshin samar da wutar lantarki na IranShugaba Donald Trump ya ce a ranar Litini...
23/03/2026

Trump ya dage kai hare-haren soji kan tashoshin samar da wutar lantarki na Iran

Shugaba Donald Trump ya ce a ranar Litinin Amurka ta yi tattaunawa mai kyau da Iran kuma zai umarci sojoji da su dage duk wani hari na soja kan tashoshin samar da wutar lantarki da kayayyakin more rayuwa na Iran na tsawon kwanaki biyar.

Matakin Trump ya biyo bayan barazanar da Iran ta yi na kai hari kan tashoshin samar da wutar lantarki na Isra'ila da kuma kasashen da ke da sansanonin Amurka a yankin Gulf idan Amurka ta kai hari kan hanyoyin samar da wutar lantarki na Iran.

Za a ci gaba da tattaunawa da Iran a tsawon mako guda, in ji Trump a wani rubutu da ya yi a shafukan sada zumunta.

"NA UMARCI MA'AIKATAR YAKI DA TA DAKATA DA DUK WANI HARIN SOJA DA AKA SHIRYA AKAN MANYAN TASHOSHIN SAMAR DA WUTAR LANTARKI TA IRAN DA KAYAN AIKI NA MAKAMASHI NA KWANA BIYAR, DOMIN SAMUN NASARA A TUNTUƁA DA TATTAWAR DA AKE CIKI.

Alarabiya English: An buga:23 Maris, 2026: 03:10 PM GST

A cewar rahotanni, Hukumar Kwallon Kafa ta Senegal ta mayar da kofin AFCON Dataci Ake Neman Kwacemata Zuwa Ga Sansanin S...
19/03/2026

A cewar rahotanni, Hukumar Kwallon Kafa ta Senegal ta mayar da kofin AFCON Dataci Ake Neman Kwacemata Zuwa Ga Sansanin Soj0ji.

Big shout out to my newest top fans! 💎 Kabir Sa'eed Na FuntuaDrop a comment to welcome them to our community,  fans
16/03/2026

Big shout out to my newest top fans! 💎 Kabir Sa'eed Na Funtua

Drop a comment to welcome them to our community, fans

Kafin Wannan Muƙabala Ta Zama Hatsari: Saƙo Zuwa Ga Fulani da “Hausa-Fulani”A kowace al’umma akwai lokuta da tarihi ke d...
16/03/2026

Kafin Wannan Muƙabala Ta Zama Hatsari: Saƙo Zuwa Ga Fulani da “Hausa-Fulani”
A kowace al’umma akwai lokuta da tarihi ke dawowa cikin tattaunawar jama’a. A irin waɗannan lokuta, mutane s**an fara sake duba asalinsu, tarihin da aka gada, da kuma tsarin siyasar da aka saba ɗauka k**ar ba za a taɓa tambayarsa ba.
A yanzu, Arewa maso Yammacin Najeriya na shiga irin wannan lokaci.
Akwai mutane da dama da ke fara bayyana kansu a matsayin Hausa kawai, suna sake duba tarihin da aka dade ana taƙaita shi da kalmar “Hausa-Fulani.” Wasu suna kallon wannan tattaunawa da sha’awa, yayin da wasu ke mayar da martani da musantawa ko kuma kariya.
Amma tarihi ya nuna cewa idan al’umma ta ƙi tattauna batutuwa masu wahala da wuri, sau da yawa sai su dawo daga baya cikin yanayi mafi hatsari.
A wasu lokuta, martanin da ake samu daga wasu masu bayyana kansu a matsayin Fulani ko Hausa-Fulani na bin wani tsari mai k**a da juna:
Musantawa — cewa wai babu wata ainihin al’ummar Hausa.
Rainawa — a ce masu wannan ra’ayi masu tada hankali ne kawai.
Kaucewa magana — a ce “Hausawa ma na iya nuna wariya.”
Amma al’umma mai haɗin kai tana buƙatar wani ƙwarewa mai wahala: ikon sauraron magana mai ɗaci game da ƙungiyarka ba tare da gaggawar kare kai ba.
Tarihin Arewa ya ƙunshi al’ummomi da dama — Hausa, Fulani, Kanuri, Tuareg, da sauransu. Wannan haɗin al’adu ne ya gina wayewar yankin.
Saboda haka tattaunawa game da tarihin Daular Sakkwato da sauye-sauyen da s**a biyo bayan jihadin Usman ɗan Fodio bai k**ata a hana su ba. Ya fi kyau a yi nazari cikin gaskiya, domin al’umma na samun kwanciyar hankali idan ta fahimci tarihinta, ba idan ta mayar da shi tatsuniya ba.
Ainihin haɗarin ba wannan muhawara ba ce.
Haɗarin shi ne yin shiru da guje mata.
A yawancin lokuta, matsalolin al’umma ba sa fara da babbar ƙara. Suna fara ne a hankali, daga gefen tattaunawa. Idan aka yi watsi da su, s**an girma har su zama rikici.
Saboda haka abin da ya fi muhimmanci shi ne al’umma ta koya yadda za ta tattauna irin waɗannan batutuwa cikin natsuwa, fahimta da girmama juna.
Al’umma mai ƙarfi ba ita ce wadda ke guje wa tattaunawa mai wahala ba — ita ce wadda za ta iya fuskantar su cikin hikima da kwanciyar hankali.
— Abdulrazak Ibrahim
Fassara Northern Culture Hub

France da Italy sun fara tattaunawa da Iran domin neman yarjejeniya da za ta ba jiragen ruwansu damar wucewa lafiya ta m...
13/03/2026

France da Italy sun fara tattaunawa da Iran domin neman yarjejeniya da za ta ba jiragen ruwansu damar wucewa lafiya ta mashigar Strait of Hormuz.
Rahotanni sun ce tattaunawar na zuwa ne yayin da rikici a yankin ke kara tsananta, abin da ke barazana ga safarar mai da kayayyaki a duniya.
Sai dai gwamnatin Italy ta fito ta musanta rahoton cewa tana tattaunawa kai tsaye da Tehran.

Shugaban Iran Ya Halarci Gangamin Ranar Quds a TehranShugaban ƙasar Masoud Pezeshkian ya fito cikin jama’a a birnin Tehr...
13/03/2026

Shugaban Iran Ya Halarci Gangamin Ranar Quds a Tehran
Shugaban ƙasar Masoud Pezeshkian ya fito cikin jama’a a birnin Tehran yayin gangamin Ranar Quds.
Rahotanni sun nuna cewa yayin taron, shugaban ya shiga cikin masu goyon bayan Jamhuriyar Musulunci, har ma aka gan shi yana hawa babur tare da wani matashi daga cikin mahalarta gangamin.
Ranar Quds wata rana ce ta musamman da ake gudanarwa a Iran domin nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu da kuma nuna adawa da manufofin Israel.

Shugaba Donald Trump ya ce ya k**ata ya kasance yana cikin waɗanda za su zaɓi sabon shugaban jagoran addinin Iran.Trump ...
05/03/2026

Shugaba Donald Trump ya ce ya k**ata ya kasance yana cikin waɗanda za su zaɓi sabon shugaban jagoran addinin Iran.

Trump ya bayyana haka ne a zantawarsa da kafar yada labarai ta Axios, inda ya ce yana kyautata zaton jamhuriyar Musuluncin ta Iran za ta zaɓi ɗan marigayi Ayataullah Khamna'i, wato Mojtaba Ali Khamna'i a matsayin sabon jagora, amma Trump ya ce lamari ne da ba zai taɓa amincewa da shi ba.

Har yanzu cibiyar ƙwararru, wadda ita ce ke da alhakin naɗa sabon jagoran, ba ta sanar da wanda zai gaji Ayatollah Ali Khamna'i ba, wanda harin Amurka da Isra'ila ya kashe a ranar Asabar a birnin Tehran.

Kawo yanzu ba a sanar da ranar da za a yi jana'izar marigayin ba, bayan ɗagewar da hukumomi s**a yi a farkon makon nan saboda fargabar turmutsutsu a sanadiyar tururuwa ake tunanin mutane za su yi a wajen binne marigayin.

Rahoto: Amurka ta yi asarar kusan dala biliyan 2 na kayan soja tun 28 ga FabrairuRahotanni sun nuna cewa United States t...
04/03/2026

Rahoto: Amurka ta yi asarar kusan dala biliyan 2 na kayan soja tun 28 ga Fabrairu
Rahotanni sun nuna cewa United States ta yi asarar kusan dala biliyan 2 na kayan aikin soja tun daga ranar 28 ga Fabrairu, yayin hare-haren hadin gwiwa da Israel s**a fara kan Iran.
Tun bayan fara hare-haren, Tehran ta mayar da martani ta hanyar kai hari kan akalla sansanonin sojin Amurka guda bakwai a Gabas ta Tsakiya. Wadannan sun hada da wurare a Bahrain, Kuwait, Iraq, UAE da Qatar. Haka kuma, an ce wasu ofisoshin jakadancin Amurka a Saudiyya, Kuwait da UAE sun fuskanci hari.
Bugu da kari, a cikin awanni 24 na farko kacal na fara farmakin, an kiyasta cewa sojojin Amurka sun kashe kusan dala miliyan 779 — wanda ya kai kusan kashi 0.1% na kasafin kudin tsaro na shekarar 2026.
Rikicin na kara daukar sabon salo, yayin da tasirinsa ke yaduwa a yankin da ma duniya baki daya.
Za mu ci gaba da kawo muku sabbin bayanai.

A dazu da yake tattaunawa a tashar Television ta Iran, General Sardar Bahman Kargar ya bayyana cewa a duk sanda dakarun ...
03/03/2026

A dazu da yake tattaunawa a tashar Television ta Iran, General Sardar Bahman Kargar ya bayyana cewa a duk sanda dakarun Iran s**a harba mak**ai to dai dai lokacin injiniyoyin Iran suna can a karkashin kasa suna kera wasu sabbin mak**an...

Don haka yan'uwa musulmi na duniya su dena tunanin mak**an Iran zasu kare, adduar nasara muke fatan cigaba da samu daga yan'uwa..

Injiniyoyi cikin sauri suke samar da sabbin manyan mak**ai musamman a wannan lokacin da muke cikin yaki...

To Madallah...

Address

Kano

Telephone

+2348168828730

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Northern Culture Hub posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Northern Culture Hub:

Share