06/10/2026
ZUWA GA:
Hon. Yusuf Ahmed Badau
Dan Majalissar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Bagwai da Shanono Federal Constituency.
MAUDU’I: GAYYATAR HON. YUSUF AHMED BADAU ZUWA BUDE MASALLACIN JUMA’A
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.
Mai girma Hon. Yusuf Ahmed Badau, muna rubuto wannan wasika ne cikin girmamawa da fatan kana cikin koshin lafiya.
Muna farin cikin gayyatarka zuwa wajen bude Masallacin Juma’a, wanda za a gudanar a ranar 9 ga Oktoba, 2026.
Mai girma Hon., wannan gayyata ba wai saboda matsayinka na dan majalissar tarayya kawai ba ce, a’a, muna son kasancewarka a wannan wuri ne saboda kai mutum ne da muke girmamawa kuma muke son mu samu damar ganinka tare da yin wannan muhimmin aiki na addini a tare da kai.
Mun san cewa samun damar ganinka kai tsaye ba abu ne mai sauki ba a wasu lokuta, shi ya sa muke rokonka da ka karɓi wannan gayyata ta musamman, ka ba mu wannan dama ta zuwa wajen bude masallacin tare da jama’ar wannan al’umma.
Kasancewarka a wannan rana za ta kasance abin farin ciki da karramawa ga al’ummar da za su halarci wannan taro.
Muna rokon Allah Ya taimake ka, Ya kara maka lafiya da basira wajen gudanar da ayyukanka, Ya kuma sanya wannan masallaci ya zama tushen ibada, ilimi da zaman lafiya ga al’umma.
Muna fatan ganin ka a ranar 9 ga Oktoba, 2026.
Wassalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.
Daga:
Yahaya Musa Kodan Hayi
A madadin al’ummar/kwamitin shirya bude Masallacin Juma’a.