09/07/2026
Na ga wani post na ɗan uwa Ismail Gambo akan cewar ana yayin tsintar jariri a Film. Abin da ya ja hankalina comment na wani bawan Allah da ya ce,
"Ashe ba ni kaɗai Film biyu s**a yi wa kamaceceniya ba"
Duk biyun suna da bambanci,
Zarge: Fatima ba tsintar jariri ta yi ba, amanar jariri mahaifiyar jariri ta ba ta, sannan a gabanta aka haifi yaron, ta kuma ga irin tashin hankalin da mahaifiyarsa ta shiga kafin samuwar shi da yadda ake farautar rayuwarsu.
Ruɗani: Fatima tsintar jariri ta yi, ba ta san shi ba, ba ta san mahaifiyarsa ba, ba ta san shege ne ko ka halak ba, kawai ɗabi'arta ta tausayi ta sakata ɗaukar jariri.
Bambancin su shi ne: Iyayen Fatima ta zarge sun yarda ita ta haifi yaron idan ka ɗauke wasu tsirarun a gidansu.
Iyayen Fatima ta Ruɗani sun nuna yarda akan ɗiyarsu, har ma sun ɗauki matakin da ya dace. Sai dai munafukai da kuma magulmatan da s**a soma haddasa fitinar da za ta gogawa Fatima baƙin jini.
Abu mafi sake tabbatar da bambancin shi ne: Kowa ne labari saƙon da yake ɗauke da shi daban.
Zarge: Labari ne da ya kai shekara tara ko takwas ina tunanin da rubuta shi a matsayin littafi cikake. Daga marubuciya Mamu.
Ruɗani kuma na ji kamar uwar marayu ta ce ture life ne wanda shi ma ya kai shekara bakwai, domin ta tabbatar da yaron da aka tsinta yana raye a wani rubutu da ta wallafa a shafin Yahaya S. Kaya Fauziyya D. Sulaiman
Kamancinsu guda biyu ne: Kowa ce ta zo da jariri gida, amma kuma kowace hanyar da ta samo shi da hanyar da aka karɓe shi a gidansu akwai bambanci.
Ta inda s**a zama a bu ɗaya
Dukkansu Film ne.
Sunayensu ɗaya ne.
Zuwa da jariri gida amma kowa da hanyar da ta samo shi.
Ƙarin daɗawa jaririn Fatima yana da uba da dangi, shi kuwa RUƊANI ba lallai ya zama akwai iyayensa ba duba da cewa na gina labarin akan yaran da ake yasarwa ba tare da an waiwaye su ba.
Kowace kuma sunanta Fatima da ta zo da jariri.
Duk dai yadda ya kasance muna maraba da duka biyun kuma za mu ci gaba da bibiya mu ɗauki darasin ɗauka.
Jinjina ga marubutan duka✍️