02/04/2025
MAGANA TA ADALCI GAME DA ƊAN BELLO
Da farko dai ya kamata mu sani cewa Ɗan Bello da Sheikh Balalau ƴan Adam ne ba ma'asumai bane zasu iya dai-dai zasu iyayin kuskure
Sheikh Balalau kamar yadda aka sani Shahararren malamin Addinin ne Wanda ya samu shaidar nagarta daga manyan MALAMAI na ƙasar nan kuma sannan jimawar da yayi Yana riƙon shugabancin ƙungiyar izala ya tabbatar da haka domin asanina ba'a taɓa samin wata ɓaraka ba tun daga lokacin daya karɓi shugabancin har zuwa yanzu hakan yake tabbatar da nagartar sa da kuma kirkinsa da riƙon amanarsa, lallai Sheikh Balalau mutumin ƙirkiri ne da wahala ace wai an haɗa baki dashi an cuci Al'ummar Musulmai wannan kenan
Shi kuma Ɗan Bello mutum ne matashi ɗan Boko kuma ɗan gwagwarmaya mai kishin ƙasa da son ganin anyi gyara game da yadda alamuran ƙasar nan Ke tafiya Mai son ganin an magance matsalar cin hanci da rashawa a kasar nan, akwai matasa ire-irensa da muke dasu a ƙasar nan kamar irin su Barr. Abba Hikima da Barr. Bulama Bukarti irin su Jafar Jafar da sauransu da wasu da dama da ban ambata ba
Ire-iren mutanen nan lallai a yanayin yadda ƙasar nan take tafiya lallai muna bukatar ƴan gwagwarmaya ire-irensu waƴanda zasu yi amfani da ilimin su da matsayinsu wajen ganin an kawo gyara a kasar nan don haka su ɗin ba ƙashin yadawa bane, domin suma ɗin suna da amfani garemu mu Musulmi, Mu ƴan Arewa, lallai muna buƙatar su Sai dai kuma yakamata Kai Mai karatu kasan cewa:-
(1) Su Ba ma'asumai bane s**anyi dai-dai s**anyi kuskure
(2) Su ƴan boko ne, shi kuma ɗan Boko idan bai koshi da addini ba tinaninshi ba abin dogaro bane 100% , akan samu zamiya da sauka daga shoulder
(3) Su s**an dogara ne da abinda ya bayyana agaresu ko kuma abinda bincikensu ya haifar
(4) Su ba karnukan ya hudawa bane kamar yadda wasu suke musu kallan haka kawai don suna zaune a kasashen waje ko dan ƴan boko ne, a fahimtata mutane ne masu son kawo gyara wannan kenan
Lallai Malamammu na Addini ba ƙaramin gudummawa suke bawa zamantakewar rayuwarmu ba, amfaninsu garemu bazai misaltuna bai kuma baidace ba wani ya ɗauki layin cutar dasu ko cin mutuncinsu ba, domin su kaɗai s**a rage mana a kasar nan da suke sadaukar da rayuwarsu akanmu, Allah ya ƙarfafesu Allah ya tai makesu duniya da lahira Ameen
Kai tsaye zan kutsa cikin magana game da abinda yake trending a yanzu na tuhuma da ɗan Bello yayi ga Sheikh Balalau da kuma Jibwis
Ɗan Bello acikin maganganun dayi game da Balalau akwai rashin ADALCI da baiyi Mai ba domin ya tuhumesa kamar haka:-
(1) Ya tuhumesa da mallakar account sama da Talatin, Wanda wannan ba laifi bane ɗan ƙasa ya mallaki account 100 ma ko sama da haka da BVN number ɗaya.
(2) Ya ɗora masa laifin da shi kansa Ɗan Bello n bai kawo hujja ba ƙarara wacce take nuna Balalau Yana ciki tsamo-tsamo.
(3) Ya zargi ƙungiyar da Balalau yake jagoranta wato JIBWIS da karɓar kuɗi daga wajan gomnati hakan ya nuna kenan ana Kashi muraba dasu tare da Azzaluman ƴan Siyasa.
Kuma dalilin da ya bada ya nuna cewa ƙungiyar Izala Jibwis nada Alaƙa da Kamfanin dake karɓar kuɗin daga gomnati Wanda yake zargin ba'a gudanar da aikin, Sai kuma ga hujjoji suna yawo a social media na ayyukan an kamamala, hakan yake nufin Ɗan Bello yayi kuskure wajan rashin tabbatar da ingancin bincikensa kafin ya yaɗashi kuma zargin daya jefa zuwa ga Jibwis bayyi Mata Adalci ba domin ba ita gomnati ta sawa kuɗi a account ba, don haka tuhumarta Zalinci ne
SHAWARA GAREKA ƊAN BELLO
Ni a shawarce shawarar da zan ba Ɗan Bello itace kamar haka:-
(1) Karinƙa tabbatar da dukkan binciken ka kafin ka yaɗashi don kudun kada ka kwana aikin
(2) Masu baka rahoto suma sai ka tabbatar Baza suyi Maka ƙarya ba kuma sannan su kansu suna tabbatar da ingancin bayanai kafin su baka
(3) Sannan ka rinƙa tuhumar wa'ƴanda bincikenka yabaka hujja, ba'a wa'ƴanda baka da hujja akan su ba walau ƴan Siyasa ne ko malaman Addini ne Kai koma wani irin mutum ne katabbatar kana da hujja akanshi, domin kasan cewa akwai kotu
(4) Sannan kasani Kai ba kotu bane abinda zaka iyayi shine zargi ba hukunci ba, kotu ce kaɗai take iya yin hukunci cewa wane ankama shi da laifin kaza ko kaza, Kai naka zargi binciken kotu shi zai tabbatar
(5) Fatan alkhairi kare ka da duk sauran ƴan gwagwarmaya ire-irenka musamman Barr. Abba Hikima da Barr. Bulama da sauransu
SHAWARA ZUWA GA USTAZAI DA ƊALIBAN ILIMI
A shawarce shawarar da zan Bamu anan shine muji tsoron Allah, kada murinƙa Fasiƙantar da mutum ko Yi masa ƙazafi ko ɓatashi (total condemnation) saboda yayi kuskure ko kuma saboda muna tuhumarsa da Zalinci, ya kamata musani cewa a baya dayake ɓan kaɗo ire-iren wayannan bayanai Yaba masa muke muna jinɗaɗi muna masa kirari da kwarzon shekara kamar yadda wani naga postin na wani matashi dake karatu a waje Mai suna Alhassan Mai lafia saboda abin bai shafemu ba ƴan Siyasa yake tonawa asiri.
To kaga irin hakan ba Adalci bane idan ana tuhumar wasu muna jin daɗi to kuma don tazo akanmu bai kamata kuma mu koma ɓata mutum ba, idan mukai haka me kenan? mun zama ƴan Bid'a kenan!!? Allah ya tsare kuma ya kamata musani cewa shi Mai girma Sheikh Balalau ba ma'asumin bane idan an tuhumeshi akan wani abu Gaskiyarsa itace zata kuɓutar dashi Wanda Bama shakkar Gaskiyar sa da nagartar sa
Abinda ƴan uwa s**ayi na zaƙulo ajujuwan da aka Gina cewa ba cinye kuɗin a kaiba wannan shine abinda ya dace ba zage-zage ba da cin mutuncin mutum manya-manyan MALAMAI na da ma da wasu daga cikin sahabbai an humcesu Gaskiyar su ta kuɓutar dasu ballantana na yanxu
Don haka masu zagi da cema Masa Ai dama maƙaryaci ne ko kuma ai Karen farautar ya hudawa ne su yake wa aikin don yaɓata MALAMAI kongila aka bashi kuji tsoron Allah wannan abu da kuke tafarkin ƴan Bid'a NE ba na ahlus Sunnah, ba zayyuba muna Kiran kanmu Ahlus Sunnah kuma munayi Abinda Allah subhanahu wata'ala ya Hana nayin ƙazafi ga mutum kuma munsan ba haka bane, kawai saboda ya fusata mu
Idan mutum yayi Maka ƙazafi ko yayi Maka sharri to Kai amatsayin Ahlus Sunnah kaima ba ƙazafi ko sharri zakai maiba, sai kuza ma ɗaya Allah ya tsare
A ƙarshe nake cewa USTAZAI da Ɗaliban ilimi da ƴan ƙungiyar Izala Allah ya huci zuciyar ku lallai Ɗan Bello yayi kuskure babba Allah ya gafarta Mana baki ɗaya ameen
✍️Usaimeen Mustapha
wed, 2 April. 2025