Kobo Da Kobo

Kobo Da Kobo Jaridar Kobo Da Kobo - Za ta ringa kawo muku labarai da rahotanni da dumi dumi.

Gwamnan jihar Kano ya bayar da umarnin a gaggauta biyan albashin watan Maris na shekarar 2026 ga dukkan ma’aikatan gwamn...
14/03/2026

Gwamnan jihar Kano ya bayar da umarnin a gaggauta biyan albashin watan Maris na shekarar 2026 ga dukkan ma’aikatan gwamnatin jihar domin ba su damar yin shirye-shiryen bukukuwan Eid-el-Fitr (Sallah) cikin sauki.

Mukaddashiyar shugabar ma’aikatan gwamnatin jihar, Hajiya Bilkisu Shehu Maimota, ta ce matakin na nuna kulawar gwamnati ga walwalar ma’aikata da kuma godiya ga gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar.

Ta kuma bukaci ma’aikata su yi amfani da wannan dama cikin hikima tare da ci gaba da nuna jajircewa da kwazo wajen gudanar da ayyukansu.

UEFA na shirin bude bincike kan wani lamari da ya shafI dan wasan Chelsea, wato Pedro Neto, wanda aka rawaito cewa ya tu...
12/03/2026

UEFA na shirin bude bincike kan wani lamari da ya shafI dan wasan Chelsea, wato Pedro Neto, wanda aka rawaito cewa ya tura wani ball boy a lokacin wasan ranar Laraba a filin wasa na Parc des Princes.

Rahotanni sun ce dan wasan na Portugal na iya fuskantar dakatarwa ta wasa daya saboda abin da dokokin UEFA s**a kira “unsportsmanlike conduct” (halin da bai dace ba a wasa), duk da cewa ya ba da hakuri a karshen wasan.

- RMC Sport.

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gargadi kwamishinoni da manyan jami’an gwamnatinsa da ke tunanin sauya s...
12/03/2026

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gargadi kwamishinoni da manyan jami’an gwamnatinsa da ke tunanin sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya daban da wadda gwamnati ke ciki da su shirya ajiye aikinsu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin jagorantar zaman majalisar zartaswar jihar karo na 38 a fadar Gwamnatin Kano.

Ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci jami’in gwamnati da ke aiki a karkashinta amma a lokaci guda yana goyon bayan wata jam’iyya daban ba, domin hakan na iya kawo cikas ga tafiyar gwamnati da aiwatar da manufofinta.

Saboda haka, ya bukaci duk wani jami’i da ke da niyyar sauya sheka zuwa wata jam’iyya da ya ajiye aikinsa domin bai wa gwamnati damar nada wanda zai yi aiki da cikakkiyar biyayya ga manufofinta.

Haka kuma, gwamnan ya bukaci mambobin majalisar zartarwar jihar da su ci gaba da kada kai domin tabbatar da nasarar manufofin gwamnati da ci gaban al’ummar jihar Kano.

Me ye ra'ayin ku?

WASANNI:🚨: Hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Argentina ba ta amince da a yi wasan Finalissima a filin wasan Santiago Bernabé...
12/03/2026

WASANNI:

🚨: Hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Argentina ba ta amince da a yi wasan Finalissima a filin wasan Santiago Bernabéu ba kuma sun yi watsi da buƙatar nan take.

CONMEBOL za ta sanar da wannan shawara ga UEFA.

- Cewar, Gastón Edul.

Daga Mukhtar S Yahuza

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Nentawe Yilwatda, ya ce shugaba Bola Ahmad Tinubu yana da cikakken kudurin kare dimokrad...
12/03/2026

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Nentawe Yilwatda, ya ce shugaba Bola Ahmad Tinubu yana da cikakken kudurin kare dimokradiyya da bin doka, bayan sanya hannu kan dokar zabe ta 2026.

Ya bayyana haka ne bayan wani taron buda baki na addinai daban-daban da aka yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja, wanda ya hada shugabannin APC da na IPAC.

Yilwatda ya ce taron ya nuna hadin kai tsakanin shugabannin siyasa da na addinai, duk da bambance-bambancen da ke tsakaninsu.

Ya kuma yabawa Tinubu kan jagorancinsa, yana mai cewa manufofin tattalin arzikin gwamnatinsa sun fara nuna alamun daidaituwa.

Kotu ta amince ICPC ta ci gaba da tsare El-Rufai na karin kwanaki 14Kotu ta amince da bukatar hukumar yaki da cin hanci ...
11/03/2026

Kotu ta amince ICPC ta ci gaba da tsare El-Rufai na karin kwanaki 14

Kotu ta amince da bukatar hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ta tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, na karin kwanaki 14.

Mai shari'a Okechukwu Akweke ne ya bayar da wannan umarni domin bai wa hukumar damar kammala bincike kan wasu sabbin zarge-zarge da ake yi wa tsohon gwamnan.

El-Rufai ya taba rike mukamin ministan babban birnin tarayya Abuja a baya.

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, ya karɓi bakuncin Janar T.Y. Danjuma a wata ziyarar girmamawa da ya kai masa a fadar s...
28/02/2026

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, ya karɓi bakuncin Janar T.Y. Danjuma a wata ziyarar girmamawa da ya kai masa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

An kaddamar da wata sabuwar doka mai suna “Dokar Vinicius” domin yaki da wariyar launin fata a harkar kwallon kafa.Hukum...
28/02/2026

An kaddamar da wata sabuwar doka mai suna “Dokar Vinicius” domin yaki da wariyar launin fata a harkar kwallon kafa.

Hukumar tsara dokokin kwallon kafa ta duniya, International Football Association Board (IFAB), tare da FIFA, sun amince da wasu sabbin matakai da nufin dakile wariyar launin fata.

Daya daga cikin matakan shi ne haramta wa ‘yan wasa rufe baki yayin da suke magana da abokin hamayya a filin wasa.

Ana sa ran za a amince da wannan doka gaba daya kafin fara gasar cin kofin duniya ta 2026.

Shugaba Tinubu Ya Sabunta Wa'adin Aikin Abubakar Audi A Matsayin Kwamanda Janar Na NSCDCShugaba Bola Ahmad Tinubu ya sak...
28/02/2026

Shugaba Tinubu Ya Sabunta Wa'adin Aikin Abubakar Audi A Matsayin Kwamanda Janar Na NSCDC

Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya sake nada Dr. Ahmad Abubakar Audi a matsayin Kwamanda-Janar na Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) na wani sabon wa’adi na shekaru biyar, daga 27 ga Fabrairu, 2026.

An fara nada shi ne a 2021 ta hannun tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma wa’adinsa na farko ya kare ne a makon da ya gabata.

Shugaba Tinubu ya umurce shi da ya kara inganta aikin hukumar domin ta taka rawa sosai wajen inganta tsaron kasa.

Dr. Audi, haifaffen jihar Nasarawa, ya shiga aiki da NSCDC a 1996 kuma ya rike mukamai daban-daban kafin ya zama Kwamanda-Janar.

Barau FC ta nemi afuwa kan sabanin fahimta tsakanin kocinta da dan jarida a KanoDaga Nazir Bashir TsamiyaKungiyar kwallo...
28/02/2026

Barau FC ta nemi afuwa kan sabanin fahimta tsakanin kocinta da dan jarida a Kano

Daga Nazir Bashir Tsamiya

Kungiyar kwallon kafa ta Barau FC da ke Kano ta nemi afuwar abin da ya faru tsakanin mai horas da ‘yan wasanta, Eugene Agbabe, da mamban kungiyar marubuta labaran wasanni ta SWAN kuma ma’aikacin Freedom Radio, Aminu Halilu Tudun Wada, inda ta bayyana lamarin a matsayin sabanin fahimta.

Manajan gudanarwar kungiyar, Mista Dominic Lorfa, ne ya bayyana hakan yayin wani zaman sulhu da aka gudanar tsakanin Barau FC da SWAN a safiyar Asabar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.

Lorfa ya ce tun farko sabanin ya samo asali ne daga rashin fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu, yana mai cewa ya kamata tun a wancan lokaci su kwantar da hankalinsu domin kauce wa rikicin.

Ya kuma jaddada kyakkyawar alakar da ke tsakanin kungiyar da ‘yan jarida, musamman SWAN, yana mai cewa kungiyar ta dauki mataki kan lamarin tare da alkawarin cewa hakan ba zai sake faruwa ba.

Har ila yau, ya yabawa shugabannin SWAN karkashin jagorancin Zahraddeen Saleh bisa jajircewarsu wajen sasanta rikicin.

Tun da fari dai, Aminu Halilu Tudun Wada ya zargi kocin Barau FC, Eugene Agbabe, da cin zarafinsa da kuma yunkurin dukansa a bainar jama’a, lamarin da ya kira rashin mutunta dan Adam.

Address

No. 179 Durumin Iya
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kobo Da Kobo posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share