26/10/2023
Mene ne laifi idan ka dangwalawa ɗan’uwanka ‘Like’ da niyyar ƙarfafa shi a Facebook.
Muna da marubuta masu tasowa a wannan kafa ta “Facebook” ta yaya zamu ƙarfafesu,? Suna yin rubututtuka masu amfanin gaske, amma haka za ka ga an barshi ba mai kulawa ballantana ya yi musu ‘Like ko comments,’ Irin wannan rashin ko na kula ɗin yana sare ma da yawa daga cikin su gwiwa, kuma haka na sabbaba mu rasa su, na san akwai wani Mentality na ƴan’uwa a wannan soshiyal midiya ɗin na ganin idan s**a yi maka "Like ko Comments" k**ar sun taimaka maka ne.
Kada kace: “Idan har don Allah suke yi baza su damu da like ko comments ɗin kowa ba.”
Mun san da wannan amma komai yana buƙatar ƙarfafa ai, akwai waɗanda muke tare da su ake musu ganin manyan marubuta ne a wannan kafa da ace za su ƙarfafi irin waɗannan da like ɗin su ko comments, kai idan ya rubuta abu mai kyau sosai ma kayi "Sharing" hakan zai ƙarfafeshi wajen dagewa sosai.
Dalilin irin waɗannan abubuwan dake faruwa a tsakaninmu yasa wasu ba'adin ƴan’uwa s**a koma rubuta shirme saboda an fi mayar da hankali kan shi, misali k**ar haka: “Da ace zaka rubuta abu kan Jawabin Sayyid (H), ba a cika mayar da hankali kan sa ba. Amma idan a kan soyayya ka rubuta sai kaga an yi ɗuuu a kan sa sama da wancan.”
Yanzu abin da yake gudana kenan a tsakanin mu, kuma yana da kyau mu gane ya k**ata mu canza wannan abin, a wannan ɓangaren wallahi amawa sun fi mu haɗin kai, ka shiga Pages ɗin su kaga yadda suke ƙarfafa junan su, sai kana da abokai Amawa za ka gane mai nake faɗa, idan kuma kana tunanin ba haka bane abin da nake faɗa, ka shiga (Timelines) ɗin wasu ƴan’uwa, sannan sai ka koma na amawa mutanen gari, anan zaka fahimci abin da nake faɗa.
Amma sai ka rasa irin waɗannan ƴan’uwan da za ka dinga ganin su a shafukan wasu Jaridun Online da wasu shafukan wasu sanannu a wannan kafar suna yi musu comments da likes mai suke yi a lokacin da ɗan’uwansu shi ma yake baza fikirarsa wajen yin rubutu. Sai na rasa shin neman suna ya k**ata mu kira shi, ko neman wajen zama, ko shishshigi, kai ko nace wulaƙanta kai. Zaka ga da za a samu saɓanin fahimta ya soki abin da suke so, sai su koma faɗar ba muyi tunanin haka daga gare ka ba. Bayan tun farko su s**a yi kuskuren bashi wannan amincin.
Tabbas wannan gaskiya ce mai ɗaci, amma buri na shi ne mu fi ƙarfin zuciyoyinmu mu amshi wannan gaskiyar. Tabbas muna aiki saboda Allah ne a wannan kafar ta Fesbuk, amma akwai abubuwan da zasu ƙarfafemu wajen Inganta ayyukanmu a waɗannan kafafen da muka bayyana.
Idan mutum yana yin rubutu, mu kuma muna daure wa mu fi ƙarfin zuciyoyinmu muna yi mishi ‘like da Comments’, wallahi hakan zai ƙarfafe shi.
Ƙiri-ƙiri mutum yana jin daɗin Posting ɗin ka a duk lokacin da kayi, amma ɗan like ɗin da zai danna maka, shi ne bazai yi ba, sai dai yayi Scrolling down ya wuce. Wasu a tunaninsu ma idan s**a yi maka Like ko Comment taimaka maka s**a yi. Musamman ƴan'uwa da muke tarayya da su a wannan kafar, sai kaga mutum yana kyashin yi maka Like ko Comment. Kuma yana jin daɗin Posting ɗin ka.
Amma tsabar neman suna, sai ka tsince su can shafukan Celebrities ko kuma manya-manyan Jaridu suna yin Comment da Liking, Amma nan sun ƙi tsayawa su mayar da shafin ɗan'uwansu Shahararre. Wallahi idan kaga shafin ɗan'uwa a wannan sahar yana da yawan Likers da Commenters, to wallahi amawa (mutanen gari) ya tara a shafin shi da yawa. Sun fi ƴan'uwa yawa a shafin nashi. Saboda su basa kyashin yi maka liking. Ban ce kada ayi musu like ko Comments ba waɗanda ake cewa Celebrities.
Ni wallahi ina sane wata rana nake rubuta kuskure nayi Posting, don na gane masu bibiya ta. Amma ba zaka gansu suna yi maka Like ko Comment ba a duk Posting ɗin ka.
To idan ma ba zaka yi hakan don Allah ba, to akwai tsarin da Fesbuk s**a yi yanzu akan ‘Like da Comment’ a wannan kafa ta Fesbuk. Kuma tsakani da Allah ni abin yayi matuƙar burge ni, ganin yadda wasu ke rayuwa a wannan kafa ta Fesbuk ɗin. Duk da wannan tsarin ya ɗan jima, amma wasu na ɗan tambaya akan Malam wane mun dena ganin Posting ɗin ka a fesbuk, ko ka dena ne.? Sai nace musu: Idan ka dena ganin Posting ɗin ɗaya daga cikin abokanka na Fesbuk, yana da alaƙa da rashin “Like ko Comment ”ɗin ka a duk Posting ɗin da yayi.
Saboda haka idan kana son ganin Posting ɗin ɗaya daga cikin abokanka na Fesbuk kana buƙatar ka dinga bibiyar abubuwan da ya rubuta ta hanyar yi mishi “Liking ko Comment”. Hakan ne zai baka damar ganin duk Post ɗin da yayi sabo, idan kuma ba za kayi hakan ba, idan ka dena ganin Posting ɗin shi kar ka tambayi mutum ka dena ganin shi.
To ka sani idan baka yi hakan ba, hukumar da ke gudanar da Fesbuk suna ganin k**ar ma baka buƙatar shine. Shi yasa suke ɓoyeshi daga gare ka, daga ƙarshe ma su cire maka shi ta hanyar Unfriending ɗin shi daga Friend list ɗin ka.
Yana dakyau mu gane hakan. Ayi min Afuwa.
-Aba Sajjadi.