15/10/2024
Tsakanin Shugabannin Nijeriya da Talakawansu
Alaka tsakanin Shugabannin Nijeriya da Talakawansu alakar bayi ce da iyayen gidansu. Maimakon shugabanni su yi hidima ga Talakawansu, kamar yadda abin yake a ko wane tsarin mulki a duniya, a Nijeriya talakawa ke bauta, su kuwa shuwagabanni su kwashe arzikin kasa don amfanin kawunansu da iyalansu da yan barandansu.
Ana yin gwamnati ne don ta sarrafa arzikin kasa, ta samar da ababen more rayuwa ga yan kasa, amma banda a Nijeriya. A kasata Nijeriya banda ma gwamnati ta kasa samar da kome ga talaka, kullum sai tatsar sa take yi, tana yi masa alkawuran karya da rainin wayo.
Gwamnatin Nijeriya ta kasa samarwa yan kasa tsaron rayukansu da dukiyoyinsu, ta bar su a hannun yan fashi da yan ta'adda da yan daba da yan fashin daji da sauran dukkan nau'i na masu laifi. Yau yan Nijeriya su ke samawa kansu tsaro. Don haka hatta a cikin birane ko ina sai shingaye kake gani suna tashi don ba wa kai tsaro.
Gwamnatin ta gaza ba wa yan kasa abinci, a yau yunwa tana kashe mutane ana ji, ana gani, babu ruwan shugabanni. Su aikin sace dukiyar mutane da kulle-kullen siyasa ne ya dame su. Abinci ya fi karfin talaka saboda rashin abincin da tsadarsa da rashin kudi a hannun mutane.
Gwamnati ta gaza ba mutane ilmi, yau kowa ya koma ga makarantu masu zaman kansu, sai dai wanda ba shi da hali shi ke kai yayansa makarantun hukuma wadanda suna ne kawai na makarantu suke dauke da shi, amma ba hakika ba.
Gwamnati ta kasa samar da tsarin lafiya ga talakawa, don haka mutane sun koma asibitoci masu zaman kansu, saboda asibitocin gwamnati sun zama suna kawai, kuma a hakan ma kome sai talaka ya biya.
Gwamnati ta kasa ba mutane ruwan sha, saboda haka talakawa sun koma shan ruwan jiyoji da kududdufa, nusamman a yankunan karkara, masu hali kuma su haka rijiyoyin burtsatsae.
Gwamnati ta gaza samawa talakawa wutar lantarki, don haka mutane sun hakura da hasken lantarki kuma sana'o'i da s**a dogara da wutar lantarki duka sun tsaya, abinda ya kara jefa mutane cikin talauci. Masu hali sun koma amfani da "Sola", marasa shi kuma ko oho.
Gwamnatin Nijeriya sam ta daina gina tituna, sai dai t**in kabilanci da ya fi ko wanne t**i a duniya tsada. Tituna duka sun rugurguje, ba bambanci tsakanin birane da dazuka. A sakamakon haka, kullum sai hadurra ake yi wadanda suke lakume rayukan talakawa da haddasa asarar dukiya. Kuma saboda tsabar raina talaka wai harajin t**i za su dawo da shi, kowa ya hau matattun titunansu sai ya biya.
Ya Allah Annabinka Muhammad (SAW) ya yi addu'a, ya ce:
"اللهم من ولي من امر امتي شيءا فشق عليهم فاشقق عليه." (رواه الامام مسلم)
Ma'ana: "Ya Allah wanda ya shugabanci wani abu daga al'amarin al'ummata, kuma ya tsananta musu, ka tsananta masa."
Ya Allah ga Shugabanninmu sun tsananta mana, Allah ka tsananta musu.