12/08/2025
Majalissar Matasa Ta Kasa Reshen Jihar Katsina NYCN Sun Gudanar Da Bikin Ranar Matasa Ta Duniya (International Youth Day).
Majalisar Matasa ta Kasa (NYCN) reshen jihar Katsina ta shirya taron musamman domin bikin Ranar Matasa ta Duniya, wanda ake gudanarwa a duk shekara domin kara wayar da kan matasa kan rawar da suke takawa wajen ci gaban kasa.
Taron ya samu halartar manya manyan mutane na fadin jihar katsina, shugabannin matasa daga sassa daban-daban na jihar, kungiyoyin fararen hula, dalibai da wakilan hukumomin Gwamnati.
An gudanar da jawabai da dama masu karfafa gwiwa, inda aka tattauna kan muhimmancin matasa a harkokin siyasa, ilimi, sana’o’i da kuma ci gaban tattalin arziki.
Da yake jawabi a lokacin taron, shugaban majalisar Hon. Yusuf Abubakar Papa, ya yi kira ga matasa da su rungumi zaman lafiya, hadin kai da kuma yin amfani da damammakin da suke da shi wajen inganta rayuwarsu da ta al’umma baki daya.
Ya kuma gode wa duk masu ruwa da tsaki da s**a tallafa wajen ganin taron ya yi nasara.
Gwamnan jihar Katsina wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa Hon. Faruk Lawal Jobe ya bayyana cewa ranar Matasa ta Duniya tana tuna mana muhimmancin matasa a matsayin ginshiƙin ci gaban kowace al’umma da ƙasa.
Ya kara da cewa, Gwamnatin jihar na da niyyar ci gaba da tallafawa shirye-shiryen da ke rage rashin aikin yi da bunkasa ƙwarewar matasa.
Sauran mutanen da s**a yi jawabai na kwarin gwiwa da cigaban matasa a wajen taron sun hada da; Kwamishinar mata ta jihar Katsina Hajiya Hadiza Yar’adua, shugaban hukumar cigaban jihar Katsina Dr. Mustapha Shehu, shugaban hukumar KATDICT Alhaji Naufal Ahmad, Sadaukin Kasar Hausa Dr. Haruna Maiwada da sauaransu.
Taron wanda ya gudana a ranar Talata 12/8/2025 a dakin taro na Bello Kofar Bai ya gudana cikin yanayi na nishadi, tare da gudanar da wasu wasanni da nuni na al’adu domin kara hadin kai tsakanin matasa.