29/11/2025
ZUWA GA GWAMNAN JIHAR KAN, DA TSOHON GWAMNA GANDUJE, DA SANATA BARAU.
Assalamu Alaikum,
A wannan lokaci da al’amuran tsaro s**a fara ɗaukar wani sabon salo a Jihar Kano, muna roƙon ku, Gwamnan Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, da tsohon Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, tare da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Dist. Sen. Barau Jibrin, ku ajiye maganar sabani, ku ɗora a kan abin da ya fi komai muhimmanci: tsaron rayukanmu da mutuncin jihar da ke hannunku.
Yanzu lamarin ya kai matakin da ’yan bindiga ke shiga kananan hukumomi suna k**a jama’a, suna razana al’umma, suna rage mana kwanciyar hankali. Wannan ba lokacin siyasa ba ne, ba lokacin jayayya ba ne. Lokacin haɗin kai ne.
Abin da muke so yanzu shi ne:
Hadin kai wajen Shirye-shiryen kawo tsaro a jihar Kano a wannan Lokacin.
“Don Allah, ku haɗa kai. Ku mayar da tsaro a matsayin abu na farko a wannan lokacin.
Tarihin Kano zai rubuta sunayenku da zinariya idan kuka tsaya, kuka tashi tsaye wajen magance wannan bala’i tare.
Sarkin Maganin Nigeria