23/03/2025
Hana Hawan Sallah A Kano: Matakin Da Zai Kare Lafiya da Tsaron Jama’a
Ina kira ga gwamnatin Kano da ta yi duba mai kyau game da shirin gudanar da Hawan Sallah da Sarakuna biyu ke shirin yi a birnin Kano.
A matsayina na wanda ke da fahimta a fannin tsaro da walwalar jama'a, ina so in ja hankalin Gwamnatin Kano da hukumomin tsaro cewa, barin wannan hawa ya gudana a lokaci guda yana iya jefa rayuka da dukiyoyin jama’a cikin hatsari.
A halin yanzu, muna sane da cewa rikicin masarautar Kano na ci gaba da haifar da damuwa a zukatan mutane. Idan aka bar Sarakuna biyu su gudanar da Hawan Sallah, akwai yiwuwar hakan ya zama mafari na rashin tsaro da rikici a birnin Kano, wanda zai iya haifar da barnar da ba za a iya iya lissafawa ba.
Dole ne mu tuna cewa a irin wannan yanayi, tarukan jama’a sukan zama mafaka ga masu haddasa fitina. Hakan na iya zama babbar barazana ga lafiya da zaman lafiyar al’umma. Don haka, Ina roƙon Gwamnatin Kano da ta ɗauki matakin gaggawa na hana kowanne bangare daga gudanar da Hawan Sallah a bana, domin gujewa mummunan tashin hankali.
Idan har akwai bukatar gudanar da Hawan Sallah, to yana da kyau a samu tsari na musamman tare da hadin gwiwa da hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa ba a samu barazana ga zaman lafiya ba.
Ina kira ga daukacin al’ummar Kano da su zama masu bin doka da oda, tare da gujewa duk wani yunkuri na tayar da hankalin jama’a.
Allah ya ci gaba da kare Jihar Kano da al’ummarta baki ɗaya.
Sarkin Maganin Nigeria Dr Hafiz