22/09/2025
Yanzu lokaci yayi da Matasa Yakamata munfito mu nunama waɗannan tsoffin jiragen ruwan nan zamu iya.
Assalamu alaikum wa rahmatullah,
Ina sanar da ku ‘yan uwana, abokaina da al’ummar ƙaramar hukumar Tarauni, cewa na yanke shawarar tsayawa takara a matsayin ɗan majalisar jiha mai wakiltar Tarauni a jihar Kano.
Wannan mataki ba don sha’awa ko son zuciya ba ne, illa don burina na ganin al’umma ta amfana da wakilci nagari – wakilci mai cike da gaskiya, adalci, da kula da jin daɗin jama’a. Na ɗauki Khalifa Umar bin Abdul’aziz a matsayin abin koyi, saboda irin shugabancinsa na gaskiya da tsoron Allah wanda ya kasance ginshiƙi ga al’umma.
Ina roƙon goyon bayan ku, addu’o’inku da haɗin kan ku, domin tare zamu iya kawo canji mai amfani da cigaba ga al’ummarmu ta Tarauni.
Allah ya taimake mu, ya tabbatar da mu akan gaskiya.