08/02/2023
Akwai alamun Rashin lafiyar ƙwaƙwalwa ga wanda ya zaba Jam'iya da ba NNPP ba - Yaro
Matashi Comrd. Abdulrazak Ibrahim Yaro, Ya Bayyana Ra'ayinsa A Kakar Zabe Mai Zuwa na 2023, Matashin Yayi Jankunne Ga Yan'uwa Matasa Maza Da Mata Kan Su Guji Zabar Wata Jam'iyyar Siyasar Bayan NNPP Mai Kayan Marmari, saboda itace Jam'iyya É—aya tilo na gaskiya da rikon Amana a Nijeriya wanda Talaka zai amfana.
Bugu da ƙari Matashin ya kara da cewa; Al'ummar Nijeriya sun gwada PDP, da APC, cikin wasu shekaru baya da s**a shuɗe amma har Yanzu ba wani abu da ya canza, don haka ga jam'iyyata nan mai kayan marmari yana kira ga al'umma fa su zabi Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso a matsayin shugaban kasar Nijeriya a zaɓen kakan bana mai zuwa 2023.
Matashin ya kara da cewa; da yiyuwar a duba kwakwalwar duk wani wanda ya zaba wata jam'iya da ba NNPP ba bisani Matashin dan siyasa a kano wanda yake kishin al'umma ya Bayyana yana cewa mu gyara Siyasar mu Domin mu Gudu Tare Mutsira Tare dole ne matashi ya shiga siyasa domin kawo sauyi ga matasa, matasa mune kashin baya a ko ina. saboda haka a kano bai kamata mubar APC takawo koda akwati guda daya ba ko wata mazaba daya Akano ba saboda mu y'an kano wayayyu ne munga irin rawar da wannan jagoran mu tundaga 1999 zuwa yanzu mai girma jagora
A cewar matashin Eng.Dr Rabiu Musa Kwnkwaso bawanda ya kaishi tarihi a yan siyasa da muke da su muna kira da muyi kokari mucere san rai mu zabi ABBA kabir yusif a matsayin Gwamnan Jihar Kano, A kasa kuma ina kira da sauran jahohi mubi a hankali muzabi Eng Dr Rabiu Musa Kwnkwaso saboda nasan yadda yayi tsarin Mulkinsa a kano haka zaiyi a Nageriya, kada mubi layin da bazai kaimu ga nasara ba mubi layi nagari.
Bawanda yakai Kwnkwaso lafiya a yan takarkarinmu na shugabancin kasa da kuma kishin kasar sa talaka yake wa aiki ba kansaba, yayi Addu'ar Allah Ubangiji Yayi Mana Jagora Sannan Yaci Gaba Da Bamu Nasarorin Sa Aduk Kannin Al'amuran Da Muka Sa Agaba.
Daga Comrd. Abdulrazak Ibrahim Yaro.