13/09/2025
KUDI IRIN NA DANGOTE KO ILIMI IRIN NA PANTAMI...
Ina yawan ganin mutane suna hada wanan tambaya suna posting a social media, cewa kudi irin na dangote ko ilimi irin na pantami zabi daya, to bari mu danyi nazari kadan akan wanan tambaya.
Ilimi dai yana tare da arziki, basira, fahimtar addini da duniya, da kuma mallakar hikimar da zata iya canza rayuwar mutum da al’umma baki ɗaya, Ilimi yana bayar da haske, yana sa mutum ya zama abin dogaro, kuma yana raye har bayan mutuwarsa ta hanyar tasirin da ya bari. Misali, Malam Pantami ko bayan ranSa zai bar darussa, littattafai, wa’azi, da ilimi da zasu cigaba da amfani ga mutane. Wannan shi ake kira da “sadaqatul jariya”.
Kudi yana tare da arziki, wadata, mallakar dukiya da kadarori da ake iya gani da amfani da su a rayuwa. Kudi yana kawo iko, suna, da karfin yi wa mutane taimako. Amma idan babu ilimin da zai jagoranci mutum to kudin na iya zama abin barna ko kuma ya zame maka fitina.
Don haka idan muka duba zamu gane cewa, Wanda ya mallaki ilimi zai iya mallakar kudi, amma wanda ya mallaki kudi ba tare da ilimi ba, kudin nasa yana iya bacewa ko ya zama cuta a gare shi.
Kenan zamu iya cewa, Ilimi ya fi kudi daraja, idan mutum ya mallaki duka biyun yana cikin alheri dumy-dumu. Wani malami ya taba cewa: Idan ka ba jahili kudi, ka ba shi makami ne da zai iya kai shi ga halaka da asara, amma idan ka ba mai ilimi kudi, ka ba shi kayan aikin da zai taimaki kansa ya taimaki Al'umma baki daya.