30/04/2024
𝐀𝐋𝐀𝐌𝐎𝐌𝐈 5 𝐃𝐀 𝐙𝐀𝐊𝐀 𝐆𝐔𝐉𝐈 𝐒𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐀 𝐃𝐀 𝐌𝐀𝐂𝐄 𝐌𝐀𝐈 𝐒𝐔..
Wa dan nan Wasu Alamomi Ne Da Ya Kamata Ace Ka Kula Dasu Yayin Da Kake Cikin Soyayya, Domin Tabbas Zasu Taimake Ka Wajen Gina Soyayar ka Cikn Farin Ciki Da Kuma Samun Macen Data Dace Da Rayuwarka...
1. Kada Ka So Macen Da Ke Yawan Tambayarka Kudi, 💰 Ko Wasu Kayan Kyale Kyale Na Rayuwa.Domin Wannan Macen Kasuwanci Take Dakai Tana Kwasan Riba Ba Soyayya da kai.
2.Ka Kiyaye Soyayya Da Mace Mai Girman Kai Ko Nuna Isa, Gami Da Jiji Da Kai Domin Mace Mai Wannan Dabi'ah, Koda Ka Aureta Ba Zata Taba Bin Umurnin ka Ko Sarrafuwa Agareka Ba 🙅♂️🙅♂️
3-Ka Guji Soyayya Da Mace Dake Katange Ka Daga Abokanka, Ko Nesan Taka Da Ahalinka, Domin Duk Macen Dake Maka Haka War Gaje Maka Rayuwa Zatayi.
4-Kayi Nesa Da Mace Mai Karyata Ka Ko Yawan Jayayyah Dakai Domin Wannan Macen Bazata Taba Girmamaka Ba, Kana Kuma Zatayi Kokarin Kauda Duk Wani Farin Ciki Dake Tare Dakai ba🙅♂️🙅♂️
5-Ka Kiyaye Soyaya Da Macen Dake Kewaye Da Maza Wadda Take Kiransu Da Abokan Ta🤔🤔 Domin Wadannan Mazaje Zasu Maye Gurbinka Agareta Sanan Kuma Tsakaninka Da Ita Babu Sirri Duk Wani Abu Inka Gaya Mata Koya Faru A Tsakninku, To Kadauka Kaman Kayi Magana ne A Kunnen Su
NOTE::- Matukar Zaka Kiyaye Wannan Tabbas Zaka Samu Abokiyar Zama Wadda Zaku Zauna Cike Da Farin Ciki Kana Kuma Da Fahimtar Juna Matukar Kasamu Macen Da Bata Da Dabi'ah Daya Daga Cikin Wadanna To Tabbas Dan Uwa Kayi Dace Kayi Kokarin Riketa Hannun Bibbiyu 🙏🙏
SHAWARI NE KYAUTA.