02/10/2023
Haba BBC Hausa😭😭😭😭
Muna Da Mabiya Shafin Ku Sama Da Miliyan Shida Da Ɗigo Biyar (6.5) Wanda Kaso Mafi Tsoka Suna Jin Yaren Hausa Kuma Suna Fahimtar Hausa, Kaso Mai Tsoka Sun Yarda Da Cewa Duk Labarin Da Ya Fito Daga Wajan Ku To Ingantacce Ne,
Kun Yarda Kuyi Posting Akan PI Network!
Kun Yarda Kuyi Posting Akan Gwauro!
Kun Yarda Kuyi Posting Akan Film!
Kun Yarda Kuyi Posting Akan Kidnerppers!
Kun Yarda Kuyi Posting Akan Kwallo!
Da Asuban Fari Kuke Mana Posting Akan Akarasa Muku Wannan Karin Maganar!
Amma Yau Kwana Biyu Yan Arewa Na Zanga-Zangan Lumana A Social Media, Yan Arewa Na Kuka Da Nuna Alhinin Su Akan Sace Mutane Da Akeyi A Arewa, Wanda Kuna Daga Cikin Masu Posting In Hakan Ya Faru, Kuna Bata Lokaci Kuyi Posting Wajan Isar Da Sakon Yan Bindiga, Amma Baku Da Lokacin Da Zaku Gayawa Duniya Kukan Yan Arewa Akan Sacewa Da Kashewa Da Lalata Dukiyoyin Mutane Da Ake A Arewa😭.
BBC Ina Da Yakinin Kun Zamu Madubi Ga Manya-manyan Jaridun Mu Na Wannan Zamanin Wanda Da Kun Sanya Wanga Labari Tabbas Da Duniya Ta Dauka, Da Kun Sanya Wanga Labari Da Tuni Kila Munji Response Daga Gwamnati!
Haba BBC Hausa Ya Kamata Ku Gyara Yadda Kuke Gudanar Da Aikin Ku, Ya Dace Ku Duba Maslahar Al-ummar Arewa Da Nigeria, Jarida Wajan Isar Da Sako Ne Ko Da Kuwa Yaci Karo Da Ra'ayina Da Naku.
Babu shakka wannan shike lokacin da yakamata ace kuma kun bamu gudun mawa matukar kunayine dominmu,sannan inna mai sanar muku da cewa matukar baku sanarwa da duniya cewa ga halin da muke cikiba a wannanokaci to zakusha mamaki agurin alumar arewacin Nigeria. yanzu aka fara wasan muje zuwa
daga BilyaBilya A Saji