DC Hausa Media Services Limited

DC Hausa Media Services Limited Media Services Limited

"Hatta a cikin gidan Tinubu Muslim-Christian ake yi, saboda haka ba a Nijeriya Sheikh Jingir zai fito ya ce a yi takara ...
11/08/2026

"Hatta a cikin gidan Tinubu Muslim-Christian ake yi, saboda haka ba a Nijeriya Sheikh Jingir zai fito ya ce a yi takara Musulmi -da-Musulmi ba"

- Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ɗan takarar mataimakin shugaban Najeriya a jam'iyyar NDC

Daya daga cikin fitattun Malaman Addinin Musulunci a nan Kano Sheik Alaramma Hadi Inuwa Maihula Sanka ya ce Auren zawara...
11/08/2026

Daya daga cikin fitattun Malaman Addinin Musulunci a nan Kano Sheik Alaramma Hadi Inuwa Maihula Sanka ya ce Auren zawarawa da gwamnatin Jihar Kano ta yi Haramun ne domin Allah madaukakin Sarki bai dorawa bawansa dole yayi Aure ba, sai wanda yake da iko.
‎
‎Sheik Hadi MaiHula ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da 'yan Jaridu a nan Kano da yammacin talatar nan.
‎
‎Ya ce al'qur'ani mai girma yayi bayanin cewa fitar da Zakka da zuwa aikin Hajji da kuma yin Aure sai wanda yake da ikon yi, yana mai cewa Aure Addini ne, Amma diban kudin talakawa da gwamnatocin jihohi ke yi domin yin Auren zawarawa ko Auren gata "Haramun ne." Ana kashe kudaden al'umma a hanyoyin da basu da ce ba, yayin da mutanen Kano s**a rasa ingantaccen Ruwan Sha da wadatattun asibitoci.
‎
‎"Da Aure, Zakka da zuwa aikin Hajji ba'a taba dorawa wani ya zama Dole ba matukar bashi da ikon," inji Malamin.
‎
‎"Allah yayi bayani a cikin Suratul Nur da Hadisan da Imam Muslim da Bukhari s**a rawaito," inji MaiHula.
‎
‎Malamin ya ce wasu daga cikin shugabannin da s**a yi a baya ma sunyi nadamar aikata hakan, yana mai Jan hankalin gwamnatin Jihar Kano ta da dakatar da aikata hakan a nan gaba.
‎
‎"Garin Kano da babu wadatattun asibitoci, babu wadatattun kwararrun likitoci, babu Ruwan Sha, Mutanen da s**a yiwa al'umma aiki wato 'Yan Fasho ba'a gama biyansu ba, amma za'a kwashi makudan kudaden ayi abun da bai da ce ba," inji MaiHula.
‎
‎"Tun daga Gwarzo ko Takai ko Tsanyawa al'umma suke tahowa asibitin kwararrun na Murtala, kuma asibitin nan tun 1928 aka yi shi, me yasa baza a gina irin asibitin a Takai ko Tsanyawa ko Gwarzo ba ?" Inji Alaramma.
‎
‎Daga nan yayi fatan gwamnatin Jihar Kano da sauran jihohi da suke da tunanin Ire-iren wannan Aure zasu dena, yana mai cewa Idan akayi Auren, gwamnatin zata ciyar musu da Matar ne ko kuma zata dauki Nauyin biyar kudin Hakika idan Matan sun Haihu, inda ya kara da cewa maimakon haka kamata yayi gwamnatin Jihar Kano ta koya musu sana'o'in dogaro da kai maimakon Barnatar da dukiyara Al'umma a hanyar da bata da ce ba da sunan Auren Gata.

Sheikh Sani Yahaya Jingir ya musanta cewa ya yi kira ga Musulmi da kada su zaɓi Kirista a kowane mataki na zaɓen 2027.Sh...
11/08/2026

Sheikh Sani Yahaya Jingir ya musanta cewa ya yi kira ga Musulmi da kada su zaɓi Kirista a kowane mataki na zaɓen 2027.

Shehin malamin ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a Jihar Kano, inda ya ce ba haka yake nufi ba.

Hotunan yadda Abdulmajid Danbilki Kwamanda jigo a jam’iyyar APC ya ziyarci Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban kasa na ...
11/08/2026

Hotunan yadda Abdulmajid Danbilki Kwamanda jigo a jam’iyyar APC ya ziyarci Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC

Ɗan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Tudun Wada Sule Lawan Shuwaki ya sanar da ficewarsa daga j...
11/08/2026

Ɗan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Tudun Wada Sule Lawan Shuwaki ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC, inda ya koma PDP.

Kakakin majalisar dokokin Kano Ismail Falgore ne ya karanta wasiƙar ficewar ɗan majalisar a zaman majalisar da aka gudanar ranar Litinin.

A cikin wasiƙar Shuwaki ya ce ya yanke shawarar barin APC ne bayan “nazari mai zurfi da shawarwari” da ya yi da abokan siyasarsa, magoya bayansa da iyalansa.

"Ni bana neman mataimakin shugaban ƙasa ko shugaban ƙasa a mutu ko ayi rai, domin ni a yanzu alhamdulillah ba nida wata ...
11/08/2026

"Ni bana neman mataimakin shugaban ƙasa ko shugaban ƙasa a mutu ko ayi rai, domin ni a yanzu alhamdulillah ba nida wata matsala, buri na shine a inganta Najeriya."

~ Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

DCL/ Facebook

’Yan Najeriya sun kashe kimanin Naira tiriliyan 6.6 wajen amfani da intanet cikin watanni 12, daga Yunin 2025 zuwa Mayun...
11/08/2026

’Yan Najeriya sun kashe kimanin Naira tiriliyan 6.6 wajen amfani da intanet cikin watanni 12, daga Yunin 2025 zuwa Mayun 2026.

Bayanan hukumar sadarwa ta Nijeriya sun nuna cewa an yi amfani da terabytes miliyan 15.32 na data a wannan lokacin.

Idan aka yi amfani da matsakaicin farashin Naira 431 kan kowane GB, jimillar kuɗin ta kai kusan Naira tiriliyan 6.6.

Amfani da data ya ƙaru daga TB miliyan 1.04 a Yunin 2025 zuwa sabon tarihi na TB miliyan 1.50 a Mayun 2026, wato ƙarin kusan kashi 44 cikin 100.

Haka kuma, MTN kaɗai ta samu kusan Naira tiriliyan 1.7 daga ayyukan data a cikin watanni shida na farkon 2026, wanda ya ƙaru da kashi 38.3 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Wannan na nuna yadda amfani da intanet da tattalin arzikin dijital ke ci gaba da bunƙasa a Nijeriya, duk da hauhawar farashin data.

Rahotanni daga kafafen yaɗa labaran Amurka sun ce an yi wani shiri na musamman domin kare Shugaban Amurka, Donald Trump,...
11/08/2026

Rahotanni daga kafafen yaɗa labaran Amurka sun ce an yi wani shiri na musamman domin kare Shugaban Amurka, Donald Trump, daga wata barazana da ake zargin Iran na iya yi masa.

Jaridar Washington Post ta ruwaito cewa Trump ya hau jirgin Air Force One a bainar jama'a bayan taron NATO a Turkiyya, amma daga bisani aka ɓoye shi cikin wata babbar motar ɗaukar abinci a filin jirgin, wadda ta kai shi wani jirgin soja ba tare da manema labarai da wasu jami'an Fadar White House sun sani ba.

Rahotanni daga jami'an Amurka sun ce an gano wata barazana ta gaske da Iran ke yi na iya harba makami mai linzami kan jirgin da Trump ke ciki.
Sai dai Fadar White House ba ta tabbatar da wannan rahoto ba.

A baya, Trump ya ce shi ne “babban abin da Iran ke nema” yayin taron kolin da aka gudanar a Turkiyya.

11/08/2026

An ce Sarki Sanusi bai ma rubuta jarabawar da ake cewa ya samu carry-over ba.

To, amma me ya sa aka ga tawagar Sarkin a jami’ar?

Ga dai abin da binciken BBC ya gano...

“Kafin Rarara, ya zagi Pantami ni ya fara zagi, ya zagi Ganduje, ya zagi shekarau, ya zagi mutane da yawa a Kano” cewar ...
11/08/2026

“Kafin Rarara, ya zagi Pantami ni ya fara zagi, ya zagi Ganduje, ya zagi shekarau, ya zagi mutane da yawa a Kano” cewar Kwankwaso

Address

Kano
700001

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DC Hausa Media Services Limited posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share