Comrd Mustapha Salisu Garo

  • Home
  • Comrd Mustapha Salisu Garo

Comrd Mustapha Salisu Garo Kayi kokarin fuskantar gwagwarmaya da qalubale batare da tsoro ko rauni ko gazawaba. Musty Yaran Oga

KAWANAKIN RAMADAN RAGUWA SUKEYI.Abun zai baka mamaki, kamar yau ne muka fara wannan azumin, amma yau gashi cikin iko da ...
23/03/2025

KAWANAKIN RAMADAN RAGUWA SUKEYI.

Abun zai baka mamaki, kamar yau ne muka fara wannan azumin, amma yau gashi cikin iko da amincewar Allah ta'ala har munyi nisa a cikinsa"

Da yawa an fara azumin nan dasu amma baza a kai ƙarshensa dasu ba, wato kai da kake raye har zuwa yau ɗinnan wane kalar ƙoƙari kayi wajen ganin ka kyautata imaninka a cikin wannan watan, ka bawa kanka amsa da kanka"

Ibnu Rajab R.A yace: Haƙiƙa kusan rabin watan nan mai albarka ya shuɗe, yanzu fa watan nan naku raguwa yake yi, ku ƙara yawan aiyukanku, zai zamo babu ku babu shi, domin kowane wata akan sami wani ya biye bayansa, amma shi ramadana taya za ku sami wanda zai biye muku bayansa"?. Ladaa'iful... 262.

SAHUURManzon Allah (SAW) Yace: "Allah maɗaukakin sarki tare da mala'ikun sa suna yin salati da adduar alkairi ga masu ta...
23/03/2025

SAHUUR

Manzon Allah (SAW) Yace: "Allah maɗaukakin sarki tare da mala'ikun sa suna yin salati da adduar alkairi ga masu tashi don su yi SAHUUR a lokacin azumi".

[Silsilah Sahih 1654].

23/03/2025

WANDA ALLAH YASA YA DACE DA WANNAN DARE TO YA YAWAITA ADDU'AR:

اللهم إنك عفو تحب العفو فاعف عني

اللهم إنك عفو تحب العفو فاعف عني

اللهم إنك عفو تحب العفو فاعف عني

اللهم إنك عفو تحب العفو فاعف عني

اللهم إنك عفو تحب العفو فاعف عني

GOMAN ƘARSHEGoman Ƙarshen Ramadana Tanada Falalar Da Gomomin Bayanta Basu Da Ita, Domin Acikin Goman Ƙarshen Ne Ake Samu...
23/03/2025

GOMAN ƘARSHE

Goman Ƙarshen Ramadana Tanada Falalar Da Gomomin Bayanta Basu Da Ita, Domin Acikin Goman Ƙarshen Ne Ake Samun Wani Dare Guda Ɗaya Tilo, Wanda Yake Falalar Da Yake Ɗauke Da Ita Tafi Na Watanni Dubu Alkhairi, An Ɓoyeshi Ga Sanin Mutane, Amma Haƙiƙa Duk Wanda Ya Raya Dukkanin Darare Goman Ƙarshen To Haƙiƙa Lallai Inshaa Allahu Ana Sa Rai Ya Rayashi"
-
"Duk Wanda Ya Raya Waɗannan Dararen Yana Mai Imani Kuma Da Kwaɗayin Lada, To Haƙiƙa Ya Dace Da Wannan Daren Na Lailatul-Qadri, Kuma Lallai Ya Sami Babban Rabo Daga Cikin Abinda Allah Yayi Tanadi Ga Wanda Ya Raya Wannan Daren Mai Falala Da Alkhairi"
مجموع الفتاوى : (١٥/٤٢٧)
-
"Kuma Abinda Ba'aso Shine Mutum Yace Zai Raya Wannan Daren Da Yake Tsammanin Samun Daren Lailatul-Qadri Yabar Wannan Wanda Baya Tsammanin Samunsa, Yin Hakan Kuskure Ne, Domin Idan Mutum Yace Haka Zai Dinga Yi To Haƙiƙa Zai Iya Yin Asarar Riskar Wannan Daren Mai Tarin Albarka"

Sai fushi suke an ba da tallafin iyayen su... Yan kusun uwa...😂 😹 😂 😹
23/01/2025

Sai fushi suke an ba da tallafin iyayen su... Yan kusun uwa...😂 😹 😂 😹

Kai tsayr daga kaduna police collage, yayin da muka wakilci chairman domin tabbatar da ganin passing out parade na yan k...
23/01/2025

Kai tsayr daga kaduna police collage, yayin da muka wakilci chairman domin tabbatar da ganin passing out parade na yan karamar hukamar kabo da s**a zama cikakkun police officers a yau tareda basu gudunmawar kudi domin suci abinci kuma su isa gida cikin aminci, a wurin kuma mai girma sakataren mulki na kabo LG Hon Abba Maiwake Garo yayi kira garesu dasu zama jakadu nagari kuma su nuna kishin al'umma, sannan su zama silar da al'umma zasu kara gasgata aikin dan sanda abokin kowa

Kai tsaye daga mazabar gude wajan kaddamar da yasar dam din gude,Mai Girma Secretary Mulki na qaramar hukumar Kabo Hon A...
22/01/2025

Kai tsaye daga mazabar gude wajan kaddamar da yasar dam din gude,

Mai Girma Secretary Mulki na qaramar hukumar Kabo Hon Abba Maiwake Garo

Tare dashi akwai MD reka Dr Nura shanono.

Musty Yaran Oga 📸👌🏽

Kai tsaye daga gude gurin tattaunawa da wakilan Gomna Abba Kabir Yusuf MD reka Dr Nura Shanono domin aikin gyaran dam di...
21/01/2025

Kai tsaye daga gude gurin tattaunawa da wakilan Gomna Abba Kabir Yusuf MD reka Dr Nura Shanono domin aikin gyaran dam din gude.

Mai Girma Secretary Mulki Na qaramar hukumar Kabo Hon Abba Maiwake Garo

Tare dashi akwai Hon Zakari Usman Balan
Allah ubangiji yasa afara aiki lafiya Ameen ya hayyu ya qaiyum

Musty Yaran Oga 👌🏽

Alhamdulillah A Yau 7/11/2024 daga office din hakimin secretariat domin wakiltar mai girma Chairman Hon Lawan Najume Kab...
07/11/2024

Alhamdulillah

A Yau 7/11/2024 daga office din hakimin secretariat domin wakiltar mai girma Chairman Hon Lawan Najume Kabo.

Hon Abba Maiwake Garo Secretary local government yakarbi bakuncin Ammasco Radio, inda s**a samemu a fadar hakimi kuma s**a tarar mun kawo kayan aiki, sannan s**azo secretariat s**aga yadda aka bareta anakan aiki, sun jinjina kuma sun saka bayanai a radio din su, sannan zasu ci gaba da kawo program na matasa.

Allah ubangiji yabamu sa'a darabo mai amfani Ameen ya hayyu ya qaiyum 🤲🏼

Ubangiji Allah Ya Qara Maka Sutura.Ubangiji Allah Ya Qara Maka Daukaka.Ubangiji Allah Ya Qara Yi Maka jagora.Ubangiji Al...
07/11/2024

Ubangiji Allah Ya Qara Maka Sutura.
Ubangiji Allah Ya Qara Maka Daukaka.
Ubangiji Allah Ya Qara Yi Maka jagora.
Ubangiji Allah Ya Taimaki Hon Abba Maiwake Garo Secretary local government

Ubangiji Allah Ya Qara Hadamu Da Masoyan Gaskiya Da Amana.

Ubangiji Allah Ya Qara Inganta Rayuwar Ka Ameen ya hayyu ya qaiyum 🤲🏼

Tabbas Naga karamci da kauna agurinka kayi abin nayabamaka domin irinka akanema a siyasa aka rasa.Ubangiji Allah ya ciga...
06/11/2024

Tabbas Naga karamci da kauna agurinka kayi abin nayabamaka domin irinka akanema a siyasa aka rasa.

Ubangiji Allah ya cigabada inganta rayuwarka
Ubangiji Allah ya albarkaci zuri'arka
Ubangiji Allah ya kawo maka matsayinda yafi wanda kake akai yanzu
Ubangiji Allah ya baka ikon sauke nauyinda yake kanka
Ubangiji Allah yayi riko da hannayenka
Ubangiji Allah ya shigemaka gaba a dukkanin harkokinka ameen ya Allah

Address


Telephone

+2348063624745

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Comrd Mustapha Salisu Garo posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Comrd Mustapha Salisu Garo:

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share