26/07/2025
YANZU YANZU:
Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar ADC, David Mark, ya ce Arewa na fama da zubda jini kuma kawai jam’iyyar ADC ce za ta iya magance matsalolin da ke damun yankin
David Mark, shugaban rikon kwarya na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya bayyana cewa Arewacin Najeriya na cikin mawuyacin hali, yana cewa yankin yana zubar da jini saboda yawan matsalolin da ke addabarsa.
Ya ce ADC ce kadai jam’iyyar da ke da ingantaccen shiri da mafita da za ta iya magance wadannan matsaloli idan aka ba ta dama ta shugabanci ƙasar.
A cewarsa, yankin Arewa na fama da kalubale da dama, kuma jam’iyyar ADC ce kadai za ta iya fitar da shi daga cikin wadannan matsaloli.
Daga Kabiru Adamu Muhammad