20/03/2022
Shekaru 7 cikin jiran tsammani...
Yau fiye da shekaru 7 Kenan muna uziri cikin jiran tsammanin warabbuka,na Samun kyautatuwar lamura a Nigeria.
Kafin zuwan me Gaskiya, zaton mu shine komai zai daidaita,tun daga farashin Mai da cin hanci da rashawa da matsalar wutar lantarki da sauran matsalolin dake addabar talaka musamman ma uwa uba matsalar tsaro,a zaton mu idan ya karbi sitiyari komai yazo karshe amma abin mamaki har ya fara tattara kayansa babu abin da ya sauya,sai ma tabarbarewar lamura.
Wallahi kafin ya hau idan nayi mafarki cewar zai shekara 7 talaka bai GA sauyi ba,zance mafarkin shaidan ne,amma sai gashi muna gani a zahiri.Allah mun tuba da muka dora wilaya GA waninka,Allah Ka karbi tuban mu.
Ni dai a ra'ayi na,matsayi na na Dan Nigeria Mai hakki,idan Zan bayar da maki a cikin wadannan shekaru 7 da akayi,sai nace na bayar da maki 6 cikin dari,shima Dan kar ace ina da kwauron maki ne.
Ina la'akari da irin dadin bakin da aka yi mana lokacin yakin neman Zabe,cewar wuta zata samu kaKaraka,man fetur ma za'a rage kudin sa,matsalar tsaro zata zama tarihi,talaka zai sha jar miya blablabla,amma wallahi babu fus duk alkawarin da akayi an mance dashi an kara tura mutane cikin masifar da tafi ta Baya.
Mai daukar albashin dubu 100 idan har ba cuwa cuwa zai yi ba,ko kuma Yana da wata sana'ar Mai kawo masa income ,Bai isa ya mallaki gida ba,idan ma yayi sa'a su ishe shi cefane, domin shinkafar da yake saya buhu naira dubu 8 a zamanin marasa gaskiya yanzu a zamanin me gaskiya ta Zama naira dubu 25, taliyar dubu 1500 yanzu dubu 4500,jarkar mai naira dubu 6 yanzu naira dubu 30. Ina gaskiyar?
Mun gaji da gafara sa alhalin bamu ga kaho ba,.an sha mu basulla an mana dadin baki an kaimu an baro mu.Allah ya kiyaye gaba.nadama dai mun yi ta,kuma ni a ganina mun tafka asara munyo zaben tumun dare.Allah mun tuba Allah Ka kawo mana chanji na gaskiya ba irin chanjin cigaban me hakar rijiya ba.
Na mance Ashe fa dala ma an yi alkawarin Zata daidaita da naira.ko nawace dalar yanzu?