24/12/2025
HANYOYIN SHIGA ALJANNAH CIKIN SAUKI.
FITOWA TA 001,
(9) SUNNONIN DA AKE SO A AIKATA A LOKACIN KIRAN SALLAH,
1-Sunnah Ne Mai Sauraren Kiran Sallah Ya Kwaikwayi Mai Kiran Sallah,
Ribar Yin Haka Shine , MANZON ALLAH YACE:
ALJANNAH Ta Wajaba Ga Wanda Ya Kwaikwayi Mai Kiran Sallah,
2-Sunnah Ne Mai Kwaikwayon Kiran Sallah Ya Karanta Wannan Addu'ar,
(اشهد ان لاإله إلاالله وأن محمد رسول الله،رضيت بل لله ربا وبل لإسلام دينا وبمحمد صلى الله عليه وسلم رسول)،
Idan Kayi Wannan Addu'ar Za'a Gafartama Dukkanin Zunuban Ka,
3-Sunnah Ne Idan Aka Gama Kiran Sallah Kayi Salati Ga MANZON ALLAH,
RIBAR YIN HAKA SHINE:-Idan Kayi Salati (1) MANZON ALLAH,
ALLAH Zai Yi Maka Salati (10),
4-Sunnah Ne Idan Aka Gama Kiran Sallah Kayi Wannan Addu'ar,
(الهم رب هذه الدعوة التامة والصلاة القاءمة، آت محمدا السيلة والفضيلة،وابعثه مقاما محموداالى وعدته)،
Idan Kayi Wannan Addu'ar Ceton MANZON ALLAH Ya Wajaba A Gare Ka,
5-Sunnah Ne Kayi Ma Kanka Addu'ah Idan Ka Kammala Dukkanin Wadancan Addu'o'in Da Muka Fada A Baya,
(10) SUNNONIN DA AKE AIKATAWA LOKACIN IQAMA (IKAMA),
Ita Ikama Ta Kunshi Dukkanin Sunnonin Da Ake Aiwatarwa A Cikin Kiran Sallah,
1-Sunnah Ne Ka Kalli Gabas Idan Zakayi Ikama,
2-Sunnah Ne Natsuwa Yayin Ikama,
3-Dole Ne Ka Fitarda Da Dukkanin Haruffa A Gabobin Da Suke Gita,
4-Sunnah Ne Idan Zakayi Ikama Kayi Cikin Sauri,
5-Sunnah Ne Sassauta Murya Yayin Iqama,
6-Sunnah Ne Bada Dan Lokaci Kadan Tsakanin Kiran Sallah Da Ikama,Wanda Zai Bada Damar Yin Sallar Nafila A Kalla Raka'a 2,
7-Sunnah Ne Mutun Ya Kwaikwayi Ladan Yayinda Ya Ke Ikama,
SAI MUN SAKE HADUWA A FITOWA TA GABA INSHA ALLAHU.,,,
Malam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum Hafizahullah