23/08/2026
Buratai ya bukaci 'yan Nijeriya su yi watsi da tsoma bakin kasashen waje kan zarge-zargen shekaru 33 da s**a gabata kan Tinubu
Tsohon babban hafsan rundunar sojin kasa ta Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya), ya bukaci ’yan Nijeriya da su yi watsi da abin da ya bayyana a matsayin tsoma bakin kasashen waje a cikin harkokin cikin gida na kasar, sakamakon yunkurin fitar da wasu takardu da ake zargin suna da alaka da binciken safarar miyagun kwayoyi da ya shafi shugaba Bola Tinubu sama da shekaru 30 da s**a gabata.
Buratai ya yi wannan kira ne a cikin wata takardar matsaya da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi.
Tsohon shugaban sojin ya ce bai kamata a bar cece-kucen da ya dabaibaye shugaban kasa ya janyo illa ga martabar Nijeriya a idon duniya ko kuma ya raunana ikon mulkin kasar ba, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.