Nuradeen Aisar

Nuradeen Aisar Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Nuradeen Aisar, Digital creator, Kano.

LABARI MAI FARANTA RAI DAGA KASAR NIJARKasar Faransa ta bada sanarwan kawo karshen yarjejeniyar tsaro da Jamhuriyar Nija...
26/09/2023

LABARI MAI FARANTA RAI DAGA KASAR NIJAR

Kasar Faransa ta bada sanarwan kawo karshen yarjejeniyar tsaro da Jamhuriyar Nijar kuma zata kwashe duk sojojinta dake Kasar, sannan ta janye jakadanta dake Kasar Nijar

Bayan haka Faransa tace tana duba yiwuwar kulle ofishin jakadancinta dake babban birnin Kasar Nijar Nyamey, tace ta dauki wadannan matakai ne saboda yanzu babu Demokaradiyya a Nijar (oho dai, aje a hakan 😂)

Kuma a taron Majalisar dinkin duniya da ya gabata Ministan harkokin waje na Kasar Nijar ya halarci taron, hakan na nufin har Majalisar dinkin duniya ta amince da Gwamnatin Soji na Kasar Nijar

Don haka yanzu borin kunya ya rage wa kungiyar ECOWAS ta cire dukkan takunkumin zalunci da rashin imani na karya tattalin arziki da ta kakaba wa Kasar Nijar, tunda uwargijiyarta Faransa ta hakura don dole, kuma masu yunkurin shan jinin Musulmai a Nijar da Arewa sun ji kunya

Yanzu Nijar ta samu 'yancin kai cikin ruwan sanyi ba tare da zubar da jinin mutun daya ba, Nijar zata karbe dukkan ragama na juya tattalin arzikinta daga Faransa

Masana suna cewa nan gaba Nijar sai ta zama wata kasa da 'yan Afirka zasu dinga rububin shiga cikinta domin cin moriyar arziki, saboda suna da tsarin Shûgabanci mai cike da adalci, hatta tsaro a yankin Sahel sai ya inganta

AlhamdulilLah 'Yanci mai dorewa yazo Kasar Nijar, 'Yan uwa na Kasar Nijar muna tayaku murnan samun 'yanci

Ba zamu manta da gudunmawar da Shugaban Izala na duniya Sheikh Abdullahi Bala Lau da tawagarsa s**a bayar ba wajen kawar da fitinar yaki a Nijar, Allah Ya biyasu da Aljannah

AlhamdulilLah 🙏

ME YASA RAYUKAN 'YAN AREWA BAI DA DARAJA?Yau kwana biyu kenan da 'yan bindiga masu garkuwa da mutane s**a shiga jami'ar ...
25/09/2023

ME YASA RAYUKAN 'YAN AREWA BAI DA DARAJA?

Yau kwana biyu kenan da 'yan bindiga masu garkuwa da mutane s**a shiga jami'ar tarayya dake Gusau jihar Zamfara s**a saci dalibai mata

Babban Ministan tsaron Nigeria Badaru Abubakar yana can Kasar Amurka taron Majalisar UN yana tattaunawa akan yadda Sojojin ECOWAS (karyan farautar Kasar Faransa) zasu afka wa Nijar da yaki domin a dawo da abin bautar turawa Demokaradiyya amma ya gagara yin magana akan abinda ya faru a Gusau

Karamin Ministan tsaro Matawalle ya fito daga jihar Zamfara, shima har yanzu bai yi magana akan lamarin ba b***e ayi batun yunkurin kubuto da daliban

Wani abinda zai baku mamaki da takaici, akwai wani mawaki a jihar Lagos wai shi Mohbad, abokan Kungiyarsu na cúltism s**aci amanarsa s**a kashe shi, har fadan Shugaban Kasa sai da s**a magantu, kuma s**a dauki kwararan matakai domin a gano wadanda s**ayi kisan

Kuma duk inda ka leka a kafofin watsa labarai batun mawaki Mohbad ake yi, manyan Yarbawa sun bawa rundinar 'yan sanda umarni akan su gudanar da bincike don gano wadanda s**a kashe mawakin

Ga jarin sunayen jami'an 'yan sanda guda 19 wanda zasu gudanar da bincike akan kisan mutum daya tal mawaki
SPECIAL INVESTIGATION TEAM ON MOHBAD CASE
👇
1. DET. ACP SAHEED KASSIM - Head
2. DET. CSP CRIS ONYEISI
3. DET. SP MASTA ALH. BUNU
4. DET. SP IBRAHIM A. YUSUF
5. DET. DSP AHMED ABDULLAHI
6. DET. ASP ODERINDE GALFAR
7. DET. ASP ALABI BOLANLE
8. DET. ASP MOHAMMED YUSU
9. DET. INSPR. ADESIDA ADEFISAYO
10.DET. INSPR. AMEH MICHAEL
10.DET. INSPR. OISA ROSELINE
12.DET. INSPR. MAYOWA OWOEYE
13.DET. INSPR. BABATUNDE VICTOR

LEGAL TEAM
👇
1. SP CARDOSO YETUNDE ESQ - OC Legal
2. DSP UMAR BELLO ESQ - Legal Officer
3. ASP AUGUSTINE NWABUISI ESQ - Legal Officer

FORENSIC TEAM
👇
1 DET. CSP AYITU AKPAMA - Team Leader
2 DET. INSPR ELIZABETH OLOKODE - Member
3 DET. INSPR QUEEN AGOFURE - Member

Kun taba gani an kashe wani mutum daga Arewa an kawo kwararrun 'yan sanda irin wannan sun gudanar da bincike?, haka b

BATUN DAWO DA TALLAFIN MAN FETURYanzu na kammala karanta wani rahoto a shafin BBC dake cewa Gwamnatin Tinubu ta dawo da ...
22/09/2023

BATUN DAWO DA TALLAFIN MAN FETUR

Yanzu na kammala karanta wani rahoto a shafin BBC dake cewa Gwamnatin Tinubu ta dawo da tallafin man fetur amma a boye

Ba zaka gane an dawo da tallafin ba sai ka karanta rahoton, da ba don an dawo da tallafin ba da yanzu litar man fetur a Nigeria zai iya kaiwa Naira N1,500 ko sama da haka
Da yanzu wahalar da muke sha ta ninka sosai

Anan zan iya cewa Shugaban Kasa Tinubu ya danyi abin alheri, kuma ya nuna tausayawa ga talakawan Nigeria, zaku iya zuwa shafin BBC Hausa ku shiga website dinsu ku karanta cikakken labarin

Sai dai muddin ana son talaka yayi walwala a Kasarnan dole a gyara matatun man fetur na Kasar da s**a durkushe, ya zama ana tace danyan mai a cikin Kasar

Muna rokon Allah Ya kawo mana saukin rayuwa a Kasarmu Nigeria

NAMIJI: yakan shiga fitina a duk lokacin da baiyi dace da macen aure na kirki ba,daga nan matsalar zata fara samuwa sabo...
21/09/2023

NAMIJI: yakan shiga fitina a duk lokacin da baiyi dace da macen aure na kirki ba,daga nan matsalar zata fara samuwa saboda rashin wannan dacen da baiyi da matar kirki ba,wani tun lokacin daya ke neman auran ta wasu daga cikin halayyanta kan iya bayyana masa, musamman tana nuna masa ita bazata iya masa biyayya yadda yake bukata ba,ko kuma dai wasu dabi'un ta daban hakan,zai iya nacewa akan yana son ta hakan.
Wani koda aibun ta aka nuna masa bazai dame sa ba shi dai soyayyah ta rufe masa ido.
Sai anyi auren Kuma a lokacin zai fara gane abinda ake nuna masa.

_bazata masa biyayya ba.
_ba zata kula masa da gidan sa ba.
_ba zata kula masa da yaran sa ba.
_ba zata kula masa da iyayen sa ba.
_ba zata kula masa da danginsa ba,babu mai zuwa wajan sa.
_bai isa ya nuna mata gaskiya ba.
_bata kulawa dashi wata ko abinci ba zata masa ba.

Kuma da yawa sai dai hakuri yake yi da ita,a lokacin zai fara nadamar rashin tsayawa binciken matar kirki mai tarbiyya.
Musamman idan taga tana kasuwanci mai karfi ko aiki wanda samun ta yafi nasa,a lokacin tana gadara da kudin ta bai isa da ita ba.

Yana daga cikin illar rashin binciken tarbiyyar mace kafin ka aure ta,da yawa mazan mu na Yanzu sun fi kallon kyalkyalin mace fiye da tarbiyyar ta,sai sun dawo daga baya kuma suna nadamar rashin tsayawa binciken matar kirki na aure.

Shawara a gare ka,duk kyalkyalin mace idan bata da tarbiyya,idan ka aure ta,bata aiki da yadda addini ya umurci mace tayi, bata da ilimin addini sannan bata nema ba ko aiki dashi,idan ka aure ta saboda son zuciya,zaka dawo kana nadama,zaka yi nadamar rashin bincike,zaka rasa abinda ya kaika neman auran ta a wannan lokacin.

Lallai ya zama wajibi a gare ku maza ku nema wa yaran ku,uwa ta gari domin samun kwanciyar hankali ku Dana iyalan ku.

21/09/2023

TSAKANINA DA 'YAN KWANKWASIYYA

Ban taba daukar dan Kwankwasiyya ko wani da muke da sabanin ra'ayi na siyasa a matsayin abokin gaba ba

Kun ga wannan tsarin Mulki na Demokaradiyya ba shine tsarin Mulkin da Allah da ManzonSa suke so ba, saboda babu hukunci da Qur'ani da Hadisi a cikinsa, asalima yana fada ne da tsarin Musulunci

To a matsayina na Musulmi me zai sa na dauki wanda muke da banbancin ra'ayin siyasar Demokaradiyya a matsayin abokin gaba? Idan nayi haka ban yiwa kaina adalci ba, Musulunci da ya hadamu yana gaba sosai da Demokaradiyya abin bautar Turawa

Sheikh Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo yace a irin wannan yanayi na siyasar Demokaradiyya a Nigeria babu wani da zaka zaba da zai kare maka Qur'ani da Sunnah, don haka ana yinta ne duk don duniya

Inda ya kamata Musulmi ya nuna kishinsa da fushinsa yayi fada shine idan makiya Musulunci s**a taba Musulunci da Musulmai, Allah bai haliccemu ya kawomu duniya don muyi Demokaradiyya ba, Allah Yayi mu ne don mu bauta masa, muna yin Demokaradiyya saboda ta zama laluri ne a garemu

Ku duba ku gani, shin 'ya'yan wadannan manyan 'yan siyasa da suke cin moriyarta suna zagin junansu? suna gaba da junansu? asalima har auratayya suna hadawa a tsakaninsu, ku kuma an barku da zagi da hauragiya cikin yunwa da bakin talauci da jahilci

Duk wanda ya zage ni akan siyasa ko ya min sharri na yafe masa, tun kafin yayi zagin na yafe Wallahi, kuma bana rike kowa da gaba akan siyasar Demokaradiyya

Daga karshe ina jaddada batun zama lafiya, ko kai mai ra'ayi da tarbiyyan dura buhun ashar ne ka sani sai ana zaune lafiya ne zaka iya zagin wani, mai iskanci baya iya sakewa yayi iskancinsa sosai yadda yaga dama sai ana zaune lafiya, haka mai addini da kasuwanci da komai na walwalar rayuwa bai yiyuwa sai da zaman lafiya

Muna rokon Allah Ya zaunar da jihar Kano lafiya da Nigeria gabaki daya Amin 🙏

26/08/2023

KU SAURARA DA KYAU

Duk namijin da zai fito ya aibata mace to idan ka bincika watakila ba dan Sunnah bane, ko kuma akwai bakin uwa a kansa

Haka nan duk macen da zata fito ta aibata na miji, ta ce wai namiji ba dan goyo da zani bane, to fa har da Ubanta wanda ya kwanta da Uwarta aka samu cikinta take nufi, duk dan halal kuwa ba zai aibanta Ubansa ba

Sai dai ana iya samun yaran da aka haifesu ta hanyar aure sai su lalace su zama 'yan iska karuwai, su rasa mutunci da kunya a tare da su, shiyasa basa ganin darajar kowa, kuma harka na aure baya gabansu

Mata masu hankali da tarbiyya islama sun san namiji Uba ne, idan kin aibata namiji watarana zaki kwanta ki mutu, namiji ne zai tsaya kanki ya miki sallah, sannan maza ne zasu kaiki makabarta su bunne

Karuwanci da fitsara yasa kuna manta wannan ko? idan kin mutu ki bada wasiyya cewa kar namiji ya kula gawarki

24/08/2023

GA WANI LABARIN SOYAYYA:

Wata yarinya ce tana yawan zuwa wani studio ta saye CD cassete a wajen wani saurayi, ashe son shi ne take yi, duk lokacin da taje sayen cassete sai ta tsaya suyi hira, har ta fada masa gidan su, ta bashi labarin iyayen ta.

Watarana sai tayi kwana bakwai bataxo ba! Sai saurayin nan yaje gidansu da tayi masa kwatanci, domin ya tambaya lafiya kwana 2 bai gane ta ba, bayan yaje, ya aika yaro sai mahaifiyar ta ta fito, ta fada masa ai yau sati daya da rasuwar yarinyar, nan take ya fadi ya suma, bayan an watsa masa ruwa ya farfado... Yayi zugum Yana kallon su, sai mahaifiyar tace ya shigo cikin gidan, ya shiga, ta jashi ta kai shi har dakin yarinyar, suna shiga yaga hoton sa manne a bango, mahaifiyar ta bashi labarin irin yanda yarinyar ke son shi, ta dauko tulin kasusuwan da yarinyar ke saye daga gareshi, tace ka gansu bata taba bude ko daya ba, na sha gaya mata idan taje wurin ka, ta fada ma tana son ka. Ta aje kasusuwan kusa gareshi, ya diba su daya bayan daya, ba wanda aka bude.

Ashe tana zuwa ne ta saye cassete, don kawai ta gan shi suyi hira, sai kawai ya fashe da kuka! Mahaifiyar tace lafiya? Sai ya bude mata cassete guda taga wasika a ciki, ashe shima duk cd da ta saye sai ya rubuta mata wasikar soyayyarshi aciki.

Yan uwa maxa da mata in kanason mutum ka fada masa, kar kayi zurfin ciki.

Address

Kano

Telephone

+2348060629279

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nuradeen Aisar posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share