
08/07/2023
1.0 Menene Bulk SMS
1.1 Yaya Tsarin Bulk SMS yake
1.2 amfanin Bulk SMS
1.3 Banbancin SMS na waya da Bulk SMS
1.4 kasuwancin Bulk SMS
1.5 kammalawa.
1.0 ♦Manhajar Bulk SMS ko ace Mass Short Message Services fasaha ce ta aika saƙonnin bai ɗaya na sanarwa, gayyata ko tunatar wa kokuma tallata manufofi ko kasuwanci da sana'a ko kamfanoni.
Da manhajar Bulk SMS ne mutum zai iya zama Digital Messenger wato me aikawa da saƙonni dijital ta hanyar amfani da wannan fasaha ko wata mai k**a da ita.
Bulk SMS Cikin sauƙi zai bada damar tura saƙo zuwa ga sama da mutum dubu a farashi mai sauƙi a ƙasa da mintuna Biyar.
1.1 Tsarin Bulk SMS tsari ne na amfani da lambobin mutane komai yawan su domin aika musu saƙon bai ɗaya nan take ta hanyar danna maɓalli ɗaya.
Dazaran kunyi amfani da ɗaya daga cikin manhajar dake samar da fasahar Bulk SMS zakuga Box Guda biyu tafarko zaku jera adadin lambobin da zaku turawa saƙo ko sun kai dubu ɗaya a box na ƙasa kuma za'a rubuta saƙon da'ake son turawa ɗin kai tsaye sai a danna send.(ku kalli ɗaya daga cikin Photon dake haɗe da wannan rubutun)
Sannan saƙon zaije ne da irin title Ɗin da aka saka masa misali taro, ko gayyata ma'ana de saƙon zaije ne da irin sunan da aka tura shi bada sunan wanda yatura ko lambar sa ba za'a iya amfani da sunan kamfani ko duk Abunda akeso.
1.2 amfanin Bulk SMS
k**ar yadda nayi bayani bulk SMS wani tsarine natura saƙonnin baiɗaya
Za'a iya amfani da bulk sms ta hanyoyin sada zumunta, kasuwanci da sauransu.
Idan katurama kwastomominka saƙo ta hanyar email ba tabbas su dubaba, haka baza’a iya tura ma numbobin mutane dubu biyu ko uku saƙoba 1 by 1 za'a gaji.
Za'a iya sana’ar bulk sms mutum yazama k**ar ɗan jarida ko ɗan aike (digital messager)
Idan ana wani event ko wani abu za'a buƙaci tura saƙonni ga mutane, hakan yakan zama aiki, amma idan ka iya bulk sms zaka iya turama kowa cikin ƙasa da minti daya zuwa biyar wannan saƙon.
Bulk SMS lamari ne ma sauƙi da ban mamaki kuma babbar dama ce ta aika saƙonni dubbai cikin lokaci musamman domin gayyata ko tallata kasuwanci ko sanarwa.
1.3 Bambancin SMS na waya da Bulk SMS
(1) a bulk sms babu numbar wanda yaturo mutum zai zaɓi sunan dayakeso wanda yataurawa saƙon yagani wanda hakan yana bawa mutum damar nuna shi na musamman ne
(2) tura saƙo maiyawa lokaci ɗaya kuma yashiga lokaci daya (kenan zaka iya amfani dashi ta fuska dadama)
(3) bashida tsada kuma yanada sauƙi.
1.4 Kasuwancin Bulk SMS
Komai kake saidawa kana Buƙatar Bulk SMS acikin kasuwancinka
Wani lokacin customer yamanta da kamfaninka ko sana'ar ka
Amma da bulk sms zaka dawo dashi ko ka tunatar dashi sana'ar ka.
Yadda za'ayi kasuwancin Bulk SMS abune me sauƙi Nafarko de shine Mutum ya wayarwa da mutane akan amfani da ma'anar Bulk SMS wato abunda ake ƙira da "Marketing Orientation" bayan wannan shine Mutum ya bibiyi ɗaya daga cikin Platform dake samar da Bulk SMS yafara gwadawa ko so ɗaya ne domin ya fahimci yadda akeyi da irin chajin da sukeyi sai kuma mutum ya tallata kansa a matsayin mai sana'ar Bulk SMS wato Bulk SMS Services.
Sana'a ce da dayawa ana dogaro da ita domin ana samun kuɗi kuma zai iya fara tallata kansa a sana'ar Bulk SMS ds Bulk SMS Ɗin misali a karon farko mutum yatura saƙo ga Mutum dubu ɗaya yana musu tallan zasu iya bashi kwangilar aikawa da saƙonnin su kai tsaye a kamfanin sa ’yan’uwa masu son Samun kuɗin online wannan Babbar harka ce me Kyau kuma me sauƙi sosai ga samun kuɗi kuma ga babbar damar tallata sana'ar ta amfani da tsarin wani Abu da mutane basu sani ba a yanzu akwai a tsarin Digital Ad a ko ina a duniya ana saka Bulk SMS a farko farko.
1.5 Ataƙaice fasahar Bulk SMS za'a iya amfani da ita domin amfanin ƙashin kai kokuna domin yin sana'a kuma salo ne me ban sha'awa da ƙayatar da kasuwanci ana amfani dashi Wajen gayyatar old boys taro ko ɗaurin aure ko tallata ɗan takarar siyasa ko kamfanoni ko sana'o'i.
Isma'il Aliyu Ubale
Albadar Global Agency Ltd
https://t.me/fasaharalbadar
8th January 2023