03/08/2026
🚨| Ku Hayayyafa – Amma Bisa Tsari!
Annabi Muhammad ﷺ ya ce:
“Ku auri mace mai ƙaunar ku, kuma mai yawan haihuwa, domin ni zan yi alfahari da ku a gaban al’umma ranar Alƙiyama.”
— Hadisi sahihi (Abu Dawud, Ahmad da Ibn Hibban)
Amma mene ne Annabi ke nufi da wannan hadisin?
Shin kawai yana nufin a haifi yara da yawa ne ko akwai tsarin da ya dace da hakan?
Ga abin da ya k**ata mu fahimta daga wannan hadisin:
1️⃣ Addinin Musulunci yana so a haifi yara da yawa, amma ba kawai saboda yawan su ba, amma saboda a haifi 'ya'ya masu kyau, masu tarbiyya, masu taimakawa addini da al’umma.
2️⃣ Yawan yara babu tsarin rayuwa ba shi ne Annabi ﷺ ke alfahari da su ba. Yara masu cutar da kansu da al’umma ba su cikin wadanda zai alfahari da su.
❌ Abinda ke faruwa yanzu:
Wasu suna haihuwar yara 10 ko fiye da haka, amma sun kasa basu, tarbiyya da ilimin addini dana zamani, sun kasa ɗaurasu tafarki madai daiciya dan gyaran goben su,
Sai kaga:
Wasu yara sun zama 'yan daba, Wasu sun fada shaye-shaye, Wasu sun bar addini ko bijirewa iyaye, Suna addabar unguwa da jama'a...
Shin da irin waɗannan yara Annabi zai yi alfahari da su? Wallahi ba haka bane .
Amma kuma duk da hakan zakaga wani yahaifi ƴaƴa biyu zuwa uku ko hudu kai wani ma ɗa 1 gareshi Amma yakasa basu tarbiyya da ilimi yanda Yak**ata, sai kaga sun zama annoba acikin Al-umma.
Wani kuma zakaga Allah ya bashi ikon haifuwar ƴaƴa dayawa 5 zuwa 10 koma fiye da haka kai wani ma har 20 akwai, Amma sai kaga ya basu tarbiyya yanda Yak**ata ya ɗaura su a hanya madaidaiciya.
To ashe anan zamu gane cewa shikan sa, tarbiyyar yara da saka su ahanya madaidai ciya yana da Alaka da su kansu iyayen yara,
Kuma ga wasu da keyin irin tunanin Turawa,
kada mu haifi yara da yawa saboda gudun talauci ne,
To ku saurara! Sun manta cewa kowane ɗan da aka haifa yana zuwa duniya da nasu arziki da kaddara.
Allah ne Mai azurtawa, kuma duk da haka dole ne mu tsara rayuwa da tunani mai kyau.
✅ Abin da Musulmi ya k**ata ya yi:
1. Auri mace mai ƙyau da nagarta.
2. Tsara rayuwa – da hankali da addu'a.
3. Haifi yara tare da niyyar bautar Allah da alfanu ga al’umma.
4. Kula da su da tarbiyya da ilimi.
5. Kasance uba ko uwa mai koyi da tsarin Musulunci.
Amma duk da haka addinin musulunci bai kayyade cewa ga adadin ƴaƴan da zaka haifa ba, dayawa ko kadan, idan kaso ka haifi ɗa 1 shi kenan idan kaso ka haifi 100 ma idan zaka iya, Amma yana da kyau kayi shi cikin sari, da kuma kyakkyawan niyya, dan anawa fahimtar babu wani Annabi da yahaifi ƴaƴa sama da 12, dan duk cikin annabawa Annabi yaqub shine kaɗai mai ƴaƴa 12, Amma Banda Annabi Adam saboda shi ba'a baiyana yawan ƴaƴan shi ba,
Sannan idan kayi duka ga manyan malamai na duniya, k**a daga musulmai da wanda ba Musulmi ba, k**ada daga malaman addini dana wanda ba na addini ba babu wanda yatara ƴaƴa fiye da kima,
Sabida haka ɗan uwa yanzu zamani ya zanca kaɗan mai Albarka yafi dayawa mara Albarka,
🔚 Kammalawa:
Annabi ﷺ yana alfahari ne da yawan mutane nagari — ba kawai yawan mutane ba.
Idan muna so ya yi alfahari da mu, mu tabbatar da cewa muna gina iyalai na gari da yara masu tarbiyya da amfani.
Allah yasa mudace 🙏
1/7/2025
🖋️ kauji