06/06/2026
MANEMA LABARAI
6 ga Yuni, 2026
HUKUMAR NOA RESHEN JIHAR KANO TA ZIYARCI FAFAR YAƊA LABARAI TA AREWA VIEW POINT DON WAYAR DA KAI KAN CUTAR EBOLA
A wani bangare na ƙoƙarin da take yi na wayar da kan jama'a game da cutar Ebola (EVD), Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA), Reshen Jihar Kano, ta yi amfani da shirin kafar yaɗa labarai ta yanar gizo mai suna Arewa View Points domin isar da saƙonnin kariya da faɗakarwa ga al'umma.
Shirin, wanda Babangida Musa Baba ya gabatar, ya samu halartar Hajiya Hauwa Adamu Garba, Shugabar Sashen Sadarwa da Yaɗa Labarai ta NOA Kano, tare da Hajiya Hafsat Kabiru Yaradu'a. Mahalartan sun yi cikakken bayani kan muhimmancin wayar da kai da ɗaukar matakan kariya domin kare lafiyar al'umma daga barazanar cutar Ebola.
Sun bayyana cewa duk da cewa a halin yanzu babu wani rahoto da ya tabbatar da bullar cutar Ebola a Najeriya, akwai buƙatar jama'a su kasance cikin shiri tare da bin shawarwari da matakan kariya da hukumomin lafiya s**a gindaya.
Jami'an sun jaddada muhimmancin wanke hannu akai-akai da ruwa da sabulu, kiyaye tsafta, gujewa hulɗa da ruwan jikin wanda ake zargin ya kamu da cutar, da kuma gaggauta kai rahoton duk wani mutum da ke nuna alamomin cutar ga hukumomin lafiya da abin ya shafa.
Har ila yau, shirin ya zama wata dama ta kawar da jita-jita da bayanan ƙarya da ke yawo game da cutar Ebola, tare da ƙarfafa jama'a su dogara da sahihan bayanai daga hukumomin gwamnati da cibiyoyin lafiya masu inganci.
Hukumar NOA Reshen Jihar Kano ta sake tabbatar da aniyarta na ci gaba da haɗin gwiwa da kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa jama'a sun samu ingantattun bayanai da za su taimaka wajen kare lafiyarsu da kuma dakile yaɗuwar cututtuka masu saurin yaɗuwa.
Kabiru Bala
Jami'in Hulɗa da Jama'a (PRO)Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA)Reshen Jihar Kano