26/04/2024
Kada ka zama mutumin kirki. Nazari cikin Falsafa.
Wannan mutumin bisa haÉin kan duniya babu shi ba a kuma taÉa yin sa ba, ba wani mutum da yake da wannan kalmar, face ga wasu babu wanda bai cancance ta ba sama da shi. Babu wani addini guda Éaya, al'ada, fahimta, ra'ayi, falsafa, hikima... da ta iya samar da wannan mutum bisa ra'ayin duk duniya kowa ya yarda, ba tare da samun mai s**a ba.
A ilimin halitta, akwai abunda mun yi tarayya akan sa, misali: komai kafin ya wanzu dole sai da kuzari (energy), ka san me ya sa mutane s**a yarda da haka? Saboda ba wanda ya san energy a haĆiĆanin sa, ka riĆe wannan; mutane ba suna saÉa ni a kan abunda ba su sani ba ne, ai daman ba su san shi ba, suna saÉani ne akan abunda s**a sani, saboda sun san shi.
A mafi yawan lokaci, mutane na siffanta wani da kirki ne bisa raunin da suke da shi, wanda ya iya magance mu su, misali: a wajen mai kwaÉayi, wanda bai san abun sa, kuma yake ba shi, mutumin kirki ne.
A wajen masifaffe, Wanda ya amincewa wulaĆacin sa, mutumin kirki ne, a wajen mai cin hanci, wanda zai bayar mutumin kirki ne.
Wasu kuma kirki a wajen su, na nufin mai irin fahimtar su koda mene ne halin sa, misali masu aĆida Éaya, addini Éaya, Ćabila Éaya, sana'a Éaya, sun fi jin kirki ga waÉanda suke da abu Éaya irin na su, sama da mai kishiyantar su, ka da manta sabanin tsakanin Fulani, da Mahauta.
Wasu kuma kirki a wajen su shi ne hali ya zo Éaya, kamar zafi, ko sanyi, kyauta ko mugunta.
Wasu kuma kirki a wajen su shi ne: masu abunda ba su da shi, kuma suke son sa a matsayin Ćarin daraja, misali; Ćalibi na ganin wanda ya fi shi ilmi ya fi shi kirki, haka talaka ga mai kuÉi, haka mace ga mijin ta, har sai wani dalili ya kore hakan.
Wasu kuma shekaru kamar ya'ya da iyayen su. A takaice siffanta mutum da kirki wani abu ne na daban ga mutane daban daban, kuma a kalma Éaya ga kowa da kowa babu shi a zahiri, duk wani hali da wani zai ga kirkin ka akan sa, shi ne dai halin da wani zai ga rashin kirkin ka akan sa.
Saboda Hi**er ya kashe Yahudawa ya zama mutumin banza ga Yahudu, amma ga yan N**i wannan shi ne dalilin zaman sa mutumin kirki, don haka ka da ka yi ĆoĆarin zama mutumin kirki, domin babu shi, idan kuma ka ce sai ka yi, za ka rasa zatin ka, to ya za ka yi ? Amsa: ka yi ĆoĆarin zama mutumin gaskiya, ita ce: siffa da ta tsaya da zatin ta ba tare da jingina ba, don haka ma Allah da bai jingina da kowa ba, ya siffantu da ita.
Tambaya Éaya ta rage, wane ne mai gaskiya ?
1- Shi ne mutumin da Yake Kallon lamari a yadda yake bisa azancin hankali, ba da nazarin Ćawazuci ba.
2- wanda yake a shirye ya bar abu a duk lokacin da ya fahimci ba dai-dai ba ne ba.
3- wanda ya fahimci rayuwar sa na da manufa sama wanzuwar sa.
4- wanda ya san amfani mutum amfanar da bayi ne ba amfanar da ubangiji ba.
5- Wanda ya fahimci Allah ake bauta mahalicci ba son zuciya ba.
Idan ba ka gane hakan ba, a sauĆaĆe shi ne: Ka yi riĆon da sunnar manzon Allah (saw) gam, ko da kuwa kowa bai ga kirkin ba, daman ba su ne za su yi ma ka hisabi ba, ita sunna gaskiya ce mai zaman kan ta bisa zatin ta, sawa'an an bi ta ko ba a bi ta, ga Allah ake komawa, kuma Allah shi kaÉai ke ba da sakamako, ba wai kawai don an ce da kai mautumin kirki ba a duniya, sai ya ba ka aljanna a lahira, da wannan siffar ta kirki da wasu s**a ba ka, mai yiwuwa ne ita ce silar zuwan ka wuta. Kirki na haĆiĆa na cikin bin halin Manzon Allah (saw) sau da Ćafa.
Allah ya yi mana tsari.
âď¸. Bukhari Alhawari