Gaskiyar Magana Radio & TV Hausa

Gaskiyar Magana Radio & TV Hausa GMT HAUSA-Gaskiyar Magana Radio Da TV Hausa. Tabbatattun labarai da sharhi kan harkokin siyasa, rayuwa da al’umma.

18/09/2026

BIDIYO: BOLA TINUBU NA SHIRIN DAKATAR DA CIRE TALLAFIN MAN FETIR NA DAN LOKACI SABODA A ZABE SHI - ATIKU

Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin saukar da farashin man fetir da nufin samun kuri’un jama’a. Ya yi zargin cewa da zarar an sake zabar sa, Tinubu zai sake maida farashin yadda ya ke.

Ya ce: “A cikin ’yan kwanaki, za a fara zanga-zanga daga Lagos kan farashin man fetur. Hakan zai ba Bola Tinubu dalilin dawo da tallafin man fetur na dan lokaci, kuma idan aka zabe ahi sai ya sake maida shi yadda yake a da. Saboda haka, ‘yan Najeriya su san da wannan shirin.”

18/09/2026

BIDIYO: “SUN FESA WANI ABU A DAKIN DA MUKE TSARE BAYAN SUN SHIGAR DA MU, SAI MUTANE S**A FARA FADUWA” – WANDA YA TSIRA DAGA CIKIN MASU HAKAR MA’ADINAI

“Sun fesa wani abu a cikin dakin da aka tsare mu bayan sun shigar da mu, sai mutane s**a fara faduwa,” in ji wani mai hakar ma’adinai da ya tsira, yayin ziyarar da Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya kai Jihar Neja.

📹 TVC News

18/09/2026

BIDIYO: ZANGA-ZANGA TA BARKA A WASU SASSAN MINNA BAYAN MUTUWAR WASU MASU HAKAR MA’ADINAI DA KE TSARE

Mazauna garin Minna a jihar Neja na tura hotuna a kafafen sasa zumunta na abin da suke kira zanga-zangar da ta barke a wasu sassan birnin Minna, babban birnin Jihar ta Neja, bayan mutuwar masu hakar ma’adinai da aka tsare.

Rahotanni sun ce yankunan Tungan Roundabout da NSTA Park na daga cikin wuraren da lamarin ya fi k**ari.

Tuni sai hukumomi s**a ce an dakatar da kwamandan Hukumar Tsaron Fararen Hula (NSCDC) na jihar daga mukaminsa, wadda a wajensu ne matasan s**a mutu.

LABARI CIKIN HOTUNA: KO A JIKINSA - TINUBU YA CI ABINCI DA MACRON A FADAR ELYSÉEDa Alama Shugaban Najeriya yana can yana...
18/09/2026

LABARI CIKIN HOTUNA: KO A JIKINSA - TINUBU YA CI ABINCI DA MACRON A FADAR ELYSÉE

Da Alama Shugaban Najeriya yana can yana ci gaba da hutunsa cikin jin dadi, inda Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya karbi Bola Ahmed Tinubu din, a wani cin abincin dare na musamman a daren Alhamis a Fadar Élysée.

Ganawar ta nuna irin dorewar kyakkyawar alakar da ke tsakanin Najeriya da Faransa, da kuma kudurin kasashen biyu na kara karfafa hadin gwiwar da ke tsakaninsu.

Tinubu dai na neman wa’adi na biyu a zaben da za a gudanar a Najeriya a watan Janairun 2027.

MACE DAYA TILO: HAJJA BINTU KONTOHajja Bintu Konto masaniya ce a fannin kiwon lafiyar jama’a, shugabar ayyukan jin kai d...
18/09/2026

MACE DAYA TILO: HAJJA BINTU KONTO

Hajja Bintu Konto masaniya ce a fannin kiwon lafiyar jama’a, shugabar ayyukan jin kai da kuma a harkokin ci gaba, wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aiki a fannonin samar da kiwon lafiya, bunkasa al’umma, ayyukan jin kai da hada kai da masu ruwa da tsaki.

Tarihin ayyukanta, musamman a al’ummomin da ke fama da rikice-rikice a Arewacin Najeriya, ya sa ta samu karbuwa sosai a matsayin mai hada kan jama’a, gina fahimtar juna da kuma shugaba mai tausayi.

Bayan shafe shekaru tana aiki a Catholic Relief Services, inda daga bisani ta yi ritaya, Hajja Konto ta rike muk**ai daban-daban na jagoranci, ciki har da matsayin Jami’ar Shirye-shiryen Hada Kai Tsakanin Al’umma da Gwamnati.

Hajja Konto ma’aikaciyar jinya ce, ungozoma, mai ilimantar da jama’a kan kiwon lafiya kuma kwararriya a fannin kiwon lafiyar jama’a. Tana da digirin Master a fannin Kiwon Lafiyar Jama’a, sannan ta taba koyarwa a matsayin malama a fannin Kiwon Lafiyar Al’umma, inda ta taka muhimmiyar rawa wajen horas da sabbin kwararrun kiwon lafiya.

KOTU A BIRTANIYA TA DAURE WANI DAN NAJERIYA SABODA WASA DA AL'AURAR SA A BAINAR JAMA'AWata kotu a Manchester, Birtaniya,...
18/09/2026

KOTU A BIRTANIYA TA DAURE WANI DAN NAJERIYA SABODA WASA DA AL'AURAR SA A BAINAR JAMA'A

Wata kotu a Manchester, Birtaniya, ta yanke wa wani dan Najeriya mai shekaru 36, Babatunde Odutola, hukuncin daurin makonni 44 a gidan yari bayan ya amsa laifin nuna tsiraici a bainar jama’a da kuma karya umarnin kotu.

Hukumar ‘yan sandan sufuri ta Birtaniya (BTP) ta ce Odutola, wanda ba shi da tabbataccen adireshin zama, ya aikata laifin ne a cikin jirgin kasa da ke tafiya daga Cheshire zuwa Manchester Piccadilly da misalin karfe 7 na yammacin ranar 11 ga Satumba, 2026.

A cewar hukumar, Odutola ya tunkari wata mata da ke cikin jirgin, inda ya rika kallonta cikin yanayi mai tayar da hankali. Bayan ta ki amsa masa, sai ya fito da al’aurarsa tare da aikata istimana'i yayin da yake zaune a kan keken guragu, yana kuma kiran matar ta zo kusa da shi.

Wani fasinja ne ya taimaka wa matar ta fita daga cikin keken jirgin bayan ta shiga cikin damuwa sak**akon abin da ya faru.

BTP ta ce hotunan kyamarorin CCTV sun nuna cewa Odutola ya ci gaba da aikata abin da yake yi yayin da sauran fasinjoji ke wucewa. Daga bisani jami’an tsaro s**a k**a shi bayan jirgin ya isa tashar Manchester Piccadilly.

A ranar 14 ga Satumba, kwana uku bayan faruwar lamarin, Odutola ya gurfana a gaban Kotun Majistare ta Manchester, inda ya amsa laifin guda na keta mutuncin jama’a da kuma karya umarnin hukuncin da aka dakatar.

Hukumar ta ce Odutola ya kasance cikin rajistar masu aikata laifukan jima’i, kuma lamarin ba shi ne karo na farko da aka samu irin wannan zargi a kansa ba.

Jami’in BTP, Leonidas Christoforou, ya ce matar ta kasance ita kadai a lokacin da aka yi mata wannan abu, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin tsoro.

Ya ce ko da yake Odutola ya musanta zargin a yayin tambayoyin ‘yan sanda, hotunan CCTV da bayanan shaidu sun samar da hujjojin da s**a tabbatar da zargin.

Kotun ta yanke masa hukuncin daurin makonni 44 a gidan yari.

GWAMNATIN JIHAR KANO TA GARGADI JAMA’A KAN MASU SAYAR DA TAKARDUN DAUKAR AIKIOfishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar...
18/09/2026

GWAMNATIN JIHAR KANO TA GARGADI JAMA’A KAN MASU SAYAR DA TAKARDUN DAUKAR AIKI

Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano ya gargadi jama’a kan wasu mutane ko kungiyoyi da ke karbar kudi domin sayar da takardun daukar aiki na gwamnatin jihar.

A cikin wata sanarwa da daraktar wayar da kan Jama’a ta ofishin, Rukayya Uba Sulaiman, ta sanya wa hannu a ranar 17 ga Satumba, 2026, gwamnatin ta bayyana cewa takardun ɗaukar aiki na Gwamnatin Jihar Kano ba na sayarwa ba ne.

Ofishin ya ce duk wanda ke neman kudi domin ba da takardar daukar aiki ko kuma ya yi alkawarin samar wa mutum aikin yi a Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano, ya k**ata a yi taka-tsantsan da shi, domin irin wannan aiki ba shi da izinin ofishin.

Sanarwar ta kuma bukaci jama’a da kada su bai wa kowa kudi, takardun sirri ko wasu kayayyaki masu daraja da sunan neman aikin gwamnati.

Gwamnatin ta shawarci masu neman aiki da su rika dogaro da tashoshin sadarwa na hukuma da sahihan sanarwar gwamnati wajen samun bayanai kan daukar ma’aikata da ba da guraben aiki.

Ta kuma bukaci jama’a da su kai rahoton duk wani mutum ko
kungiya da ake zargi da aikata irin wannan damfara ga hukumomin da s**a dace.

MUTANE 49 SUN MUTU SAKAMAKON SHAN GURBATACCIYAR BARASA A JIHAR ONDOGwamnatin Jihar Ondo ta ce adadin mutanen da s**a mut...
18/09/2026

MUTANE 49 SUN MUTU SAKAMAKON SHAN GURBATACCIYAR BARASA A JIHAR ONDO

Gwamnatin Jihar Ondo ta ce adadin mutanen da s**a mutu sak**akon shan wata barasa mai guba ya kai 49, yayin da wasu 170 s**a samu matsala a sassa daban-daban na jihar.

Kwamishinan Lafiya, Dr Banji Ajaka, ya ce mutane takwas ne s**a mutu a karamar hukumar Irele, inda jami’an lafiya ke ci gaba da gudanar da bincike da daukar matakan gaggawa.

Gwamnatin jihar ta hada kai da NAFDAC, NDLEA, DSS da NSCDC domin gano tushen abin da ake zargin wani hadin barasa na gargajiya ne da ake kira “Monkey Tail”, wanda ake zargin yana dauke da sinadarin methanol.

A baya, ‘yan sanda sun k**a mutane 15 bisa zargin hannu wajen hadawa da rarraba abin, yayin da gwamnati ta haramta sayar da barasa da magungunan gargajiya da ba a tantance ba.

KADA KU SIYAR DA GIDAJENKU DOMIN SIYAN HANNUN JARIN DANGOTE - SUNUSISarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya gargadi masu so...
18/09/2026

KADA KU SIYAR DA GIDAJENKU DOMIN SIYAN HANNUN JARIN DANGOTE - SUNUSI

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya gargadi masu son zuba jari da kada su sayar da gidajensu ko su yi amfani da kudin makarantar ’ya’yansu wajen sayen hannun jarin matatar Dangote.

Sanusi ya yi wannan gargaɗin ne a ranar Alhamis yayin taron wayar da kan masu zuba jari kan sayar da hannun jarin Dangote Refinery a Kano.

Rahotanni sun rawaito cewa Sarkin ya shawarci mutane da su zuba kudin da za su iya warewa na dogon lokaci, yana misalta da Naira 10,000, 20,000 ko 30,000.

Ya kuma bukaci masu zuba jari da kada su nemi riba cikin gaggawa, sai dai su bar jarin na tsawon lokaci domin ganin yadda zai bunkasa.

Ya ce yana son mutanen Kano su samu damar mallakar wani kaso na kamfanin Dangote ta hannun jarin.

“Idan aka zabe ni gwamna a zabe mai zuwa, cikin shekaru biyu zan kawo karshen rashin tsaro a jihar, da yardar Allah, ko ...
18/09/2026

“Idan aka zabe ni gwamna a zabe mai zuwa, cikin shekaru biyu zan kawo karshen rashin tsaro a jihar, da yardar Allah, ko kuma in bar mukamin.”

Dan takarar gwamnan Jihar Zamfara na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress, Kabiru Marafa, ya yi wannan alkawarin na magance matsalar rashin tsaro tare da kawo karshen ayyukan ’yan bindiga a wa’adinsa na farko idan aka zabe shi a 2027.

Da yake magana ranar Alhamis, tsohon dan majalisar ya ce ba a bai wa yaki da rashin tsaro da ’yan bindiga isasshen kulawa daga hukumomin da abin ya shafa ba.

Ya ce za a iya magance ayyukan ’yan bindiga cikin kankanin lokaci idan aka ba matsalar kulawar da ta dace tare da daukarta da muhimmanci.

Marafa ya ce: “Idan aka zabe ni gwamna a zabe mai zuwa, cikin shekaru biyu zan kawo karshen rashin tsaro a jihar, da yardar Allah, ko kuma in bar mukamina.”

Ya kara da cewa: “Ko dai na kawo karshen ’yan bindiga a wa’adina na farko a ofis, ko kuma in yi murabus. Na taba zama kwamishina a jihar, sannan na yi shekaru da dama a matsayin sanata a Majalisar Dokoki ta Kasa. Saboda haka, na san matsalolin da ke addabar jihata da kuma kasar baki daya.”

Address

Kano Municipal Council
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gaskiyar Magana Radio & TV Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share