29/12/2024
Saɓani tsakanin Najeriya da Nijar
Saɓani ne da ya samo asali tun shekarar bara, bayan da sojojin ƙasar s**a hanɓare zaɓaɓɓen shugaban farar hula Muhamad Bazoum, bisa zarginsa da laifin cin amanar ƙasa, zargin da har kawo rana irin ta yau gwamnatin sojin Nijar ba ta gabatarwa duniya bayyanannun hujjojin da suke tabbatar da hakan ba, wanda zamu iya gane cewa zargi ne marar tushe b***e mak**a.
Wannan juyin mulki a ƙasar dake cikin gamayyar ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) guda goma sha biyar, ya jawo rabuwar kai a tsakanin ƙasashe membobin ƙungiyar, inda guda goma sha ɗaya a ƙarkashen mulkin farar hula s**a ja tungar goyon bayan dawo da mulkin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar da aka hamɓare, guda hudu kuma a ƙarƙashin mulkin soji s**a goyi bayan masu juyin mulkin, sai dai abin sani anan shi ne, goma sha huɗun nan suna da tarihin kin mulkin mallaka da kuma mulkin gwamnatin soji.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu shi ne shugaban wannan gamayyar ƙasashe, wanda sananne ne akansa cewar ya shafe wani kaso mai yawa na rayuwarsa yana gwagwarmayar adawa da tsarin mulkin soja a Najeriya. Wannan abu ne wanda yake sananne ga dukkan wanda ya san tarihin siyasa da gwagwarmayar da Mista Bola Tinubu yayi a baya.
A tsawon tarihi, Najeriya da Nijar zaman ‘yan uwantaka suke yi, in ban da wannan karon da gamayyar ƙasashen ECOWAS s**a ɗauki matakin hukunta gwamnatin sojan Nijar ɗin da s**a yi juyin mulkin, hukuncin da ya ƙunshi dakatarwa da sanya takunkumin tattalin arziƙi, shige da fice, diplomasiyya da sauran danginsu akan waɗancan ƙasashe huɗu, wannan kuma yarjejeniya ce aka cimma ba ra'ayin shugaba Tinubu ba.
Matakan da shugabancin ECOWAS ya ɗauka matakai ne masu kyau da tsayawa a tsaka tsaki, wanda duk mai hankali zai fahimta kuma ya gamsu da su, domin rashin ɗaukar mataki akan wancan juyin mulki, tamkar amincewa ne da mulkin bakin bindiga, mulkin k**a karya, da kuma gayyato sojoji a sauran ƙasashe akan su sake fitowa daga bariki su ƙwaci mulki a kasashensu. A duniyar yau, soji ba shi da gurbi a jagorantar gwamnati. Ra'ayin al'umma mafiya rinjaye shi ne yake jagoranci.
Yasir Ramadan Gwale
29.12.2024