02/10/2025
Wallahi kai din ka kasance wanda muka tashi muka gan ka kana koyarda yadda ake Soyayyar Annabi
Mun tashi mun ganka kana koyar da yadda ake bin Manzon Allah S.A.W
Mun tashi mun ganka kana raba hanya da dukkanin wadanda suke kaucewa hanya ta koyarwar Manzon Allah. Idan aka ga kana rigima to ana sabawa Manzon Allah ne, idan aka ganka a waje to an shirya za’a bi Manzon Allah ne kadai, Wallahi wannan shine shaidar mu gare ka, Allah shine shaida mun fadi wannan gaskiyar mun sauke kada a tashi Alqiyama Allah ya tsayar da mu akan mun boye abinda muka sani akan ka, kuma kamar yadda ka tsaya akan gaskiya duk tsananinta tsawon shekaru tabbas Allah ba zai taba tozarta ka ba domin Alkawarin sa ne.