26/09/2025
YANZU YANZU:
Gwamnatin Jihar Kano ta karbi wasu koke-koke da kuma kokwanti daga kungiyoyin addinin Islama da s**a shafi kalaman da Sheikh Lawan Triumph ya yi a jihar Kano.
Mai girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ba da izni da a tura dukkan koke-koken zuwa ga Majalisar Shura ta Jihar Kano domin yin karin tattaunawa a kan su.
A cewar wata sanarwa da Musa Tanko, Sakataren Yada Labarai na Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), kungiyoyin da s**a mika koken sun hada da:
1. Safiyatul Islam na Nigeria
2. Tijjaniya Youth Enlightenment Forum
3. Interfaith Parties for Peace and Development
4. Sairul Qalbi Foundation
5. Habbullah Mateen Foundation
6. Limamai na Masallatan Juma'a karkashin kungiyar Qadiriyya
7. Kwamitin Wa'azin Sunnah, Kano
8. Multaqa Ahbab Alsufiyya
SSG, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, a madadin gwamnati, ya ba da umarnin a tura dukkan koke-koken zuwa ga Majalisar Shura ta Jihar domin yin nazari sosai da kuma ba da shawara.
Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada aniyarta ta kiyaye zaman lafiya, hadin kai, da mutunta juna a tsakanin dukkan kungiyoyin addini a jihar.
"Mun bukaci dukkan al'ummar Kano da su natsu da kuma ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullun tare da rike ka'idojin doka," in ji SSG.
Takardar Ta Samu Sanya Hannun
Sakataren Yada Labarai
Ofishin Majalisar Zartarwa, Jihar Kano
ƘARIN BAYANI...👇
Wannan Ke Nuna Gwamnati Zata Bar Malamai Ne Suyi Wannan Nazari Da Duba Akan Wannan Matsalar, Hakan Kan iya Kawowa Ayi Muqalaba Da Wadanda Ke Nuna Cewar Sheik Lawan Yayi Batanci Ga Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, kokuma a umurce su Sukawo Dalili ko Shima Yakawo Nasa dalilin, Muna Shawartar Al Ummar Jihar Kano Da Su Zama Masu Bin Doka Don Ɗorewar Zaman Lafiya A Fadin Jihar Dama Ƙasa Baki Daya, Allah Ya Zaunar Damu Lafiya Amen.