ANNUR MEDIA TV

  • Home
  • ANNUR MEDIA TV

ANNUR MEDIA TV ANNUR MEDIA TV tashar yada labarai ce wacce ke kawo sahihan labarai, ilimi, fadakarwa, da abubuwan da suka shafi al’umma cikin harshen Hausa.

Manufarmu ita ce yada gaskiya, ilimantarwa, da kawo abubuwan da zasu anfanar da al’umma. Ku danna following.

🎉 CONGRATULATIONS 🎉ANNUR MEDIA TV na miƙa saƙon taya murna ga Comrd. Mujahid Jilani Ishaq bisa samun ƙarin matsayi da ak...
12/07/2026

🎉 CONGRATULATIONS 🎉

ANNUR MEDIA TV na miƙa saƙon taya murna ga Comrd. Mujahid Jilani Ishaq bisa samun ƙarin matsayi da aka ba shi a ƙungiyar JIBWIS a matsayin Divisional Publicity Secretary, Tudun Wada "B" Division.

Wannan naɗi wata shaida ce ta amana, ƙwazo, jajircewa da kuma kyakkyawan aiki da ka nuna wajen hidimtawa addini da al'umma.

Muna addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba ka hikima, lafiya, ƙarfin guiwa da dacewa wajen sauke wannan nauyi, Ya sanya wannan matsayi ya zama alheri ga addini, al'umma da ƙungiyar JIBWIS baki ɗaya.

Allah Ya ƙara ɗaukaka, Ya ba da ikon sauke nauyin da aka ɗora maka cikin nasara. Amin.

— ANNUR MEDIA TV

30/06/2026

🎉 TAYA MURNA! CONGRATULATIONS 🎉

Ina miƙa saƙon taya murna ga ɗan'uwanmu kuma abokin aiki, Yusuf Muhammad Ladan (Rijiyar Zaki), bisa samun ƙarin girma daga matsayinsa na baya zuwa Superintendent of Unity (SU) a ƙarƙashin Nigerian Peace Unity and Progress Association (NPUPA), Kano State Command.

Wannan ƙarin girma shaida ce ta ƙwazo, jajircewa, riƙon amana da sadaukarwar da ka nuna wajen hidimtawa al'umma da bunƙasa zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara maka hikima, lafiya, ƙarfi da basirar gudanar da wannan sabon matsayi. Allah Ya sanya wannan muƙami ya zama alheri gare ka, iyalanka, ƙungiya da ƙasa baki ɗaya.

Muna yi maka fatan samun ƙarin nasarori da manyan muƙamai a gaba.

🎊 Congratulations once again! 👏 Superintendent of Unity (SU) Yusuf Muhammad Ladan (Rijiyar Zaki).

ANNUR MEDIA TV
Truth • Information • Awareness

PRESS RELEASE 🎉 TAYA MURNA! CONGRATULATIONS 🎉Ina miƙa saƙon taya murna ga ɗan'uwanmu kuma abokin aiki, Yusuf Muhammad La...
30/06/2026

PRESS RELEASE

🎉 TAYA MURNA! CONGRATULATIONS 🎉

Ina miƙa saƙon taya murna ga ɗan'uwanmu kuma abokin aiki, Yusuf Muhammad Ladan (Rijiyar Zaki), bisa samun ƙarin girma daga matsayinsa na baya zuwa Superintendent of Unity (SU) a ƙarƙashin Nigerian Peace Unity and Progress (NPUP), Kano State Command.

Wannan ƙarin girma shaida ce ta ƙwazo, jajircewa, riƙon amana da sadaukarwar da ka nuna wajen hidimtawa al'umma, kare rayuka da dukiyoyin al’umma, bunƙasa zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara maka hikima, lafiya, ƙarfi da basirar gudanar da wannan sabon matsayi. Allah Ya sanya wannan muƙami ya zama alheri gare ka, iyalanka, ƙungiya da ƙasa baki ɗaya.

Muna yi maka fatan samun ƙarin nasarori da manyan muƙamai a gaba.

🎊 Congratulations once again! 👏 Superintendent of Unity (SU) Yusuf Muhammad Ladan (Rijiyar Zaki).

ANNUR MEDIA TV
Truth • Information • Awareness

CongratulationsMuna taya Usama Yahaya bisa samun karin matsayi a rundunar Nigerian peace unity and progress, Allah ya ta...
29/06/2026

Congratulations
Muna taya Usama Yahaya bisa samun karin matsayi a rundunar Nigerian peace unity and progress, Allah ya tayaka riko

CongratulationsMuna taya Asu Surajo Ayuba bisa samun karin matsayi a rundunar Nigerian peace unity and progress, Allah y...
29/06/2026

Congratulations
Muna taya Asu Surajo Ayuba bisa samun karin matsayi a rundunar Nigerian peace unity and progress, Allah ya tayaka riko, Amin.

29/06/2026

⛔PRESS RELEASE.....

NIGERIAN PEACE UNITY AND PROGRESS TA DAGA LIKAFAR JAMI'INTA, ASU NURA LAWAN SULAIMAN, ZUWA MATAKIN DEPUTY SUPERINTENDENT OF UNITY (DSU).

Hukumar Nigerian Peace Unity and Progress (NPUP) Kano State Command, ta amince da ɗaga likafar ɗaya daga cikin jami'anta, Assistant Superintendent of Unity (ASU) Nura Lawan Sulaiman, zuwa sabon matsayi na Deputy Superintendent of Unity (DSU).

Wannan ƙarin girma ya zo ne a matsayin girmamawa da yabawa ga jajircewa, riƙon amana, ƙwarewa, da gudummawar da ya bayar wajen inganta zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban al'umma.

A yayin bikin miƙa sabbin muƙamai, shugabannin ƙungiyar sun bayyana cewa irin wannan ƙarin girma na nuni da ƙoƙari, nagarta da sadaukarwa wajen gudanar da aiki, tare da ƙarfafa sauran jami'ai su ci gaba da yin aiki cikin gaskiya da ƙwazo.

Da yake bayyana farin cikinsa, DSU Nura Lawan Sulaiman ya gode wa Allah Maɗaukakin Sarki bisa wannan ni'ima, sannan ya nuna godiyarsa ga shugabannin ƙungiyar bisa amincewa da s**a yi da shi. Ya kuma yi alƙawarin ci gaba da gudanar da aikinsa cikin gaskiya, biyayya da kishin ƙasa.

Haka kuma, ya taya dukkan jami'an da s**a samu irin wannan ƙarin girma murna, tare da addu'ar Allah Ya ba su ikon sauke nauyin da aka ɗora musu, Ya sanya albarka da nasara a cikin ayyukansu.

ANNUR MEDIA TV tana taya Deputy Superintendent of Unity (DSU) Nura Lawan Sulaiman murna tare da yi masa fatan samun nasara da ƙarin ci gaba a aikinsa na hidimtawa al'umma da ƙasa.

Media Contact:
ANNUR MEDIA TV
08160209034
Promoting Truth, Peace & Development

📚✨ THE IMPORTANCE OF KNOWLEDGE AND PUTTING IT INTO PRACTICE ✨📚"Knowledge is light, but acting upon that knowledge is wha...
07/06/2026

📚✨ THE IMPORTANCE OF KNOWLEDGE AND PUTTING IT INTO PRACTICE ✨📚

"Knowledge is light, but acting upon that knowledge is what makes that light benefit society."

Today, we live in a world where knowledge has become the foundation of progress, success, and societal development. However, unfortunately, many people seek knowledge without using it to bring about positive change.

Anyone who possesses knowledge has a responsibility to use it for:
✅ Helping the community
✅ Solving problems
✅ Building peace and unity
✅ Creating employment and economic development
✅ Teaching others what they know

Remember:

👉 Knowledge is not just a certificate.
👉 Knowledge is not just a title.
👉 Knowledge is not just a position.

True knowledge is that which changes lives, refines character, and benefits society.

Lack of knowledge, or the failure to use the knowledge one has acquired appropriately, can plunge a person into ignorance, poverty, lack of vision, and backwardness.

A youth who has knowledge and acts upon it is like a lamp that illuminates the way for others.

Let us remain steadfast in seeking beneficial knowledge. Thank you for reading; may Allah fulfill your righteous desires.

Signed: ANNUR MOBILIZATION & AWARENESS FOUNDATION (AMAF).

Address

Tudun Wada

710104

Telephone

+2348160209034

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ANNUR MEDIA TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to ANNUR MEDIA TV:

Shortcuts

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share