MW Hausa

MW Hausa Domin Samun ingantattun, sahihan labarai.

LABARI DA DUMI-DUMI: Dan Takarar NDC Ya Kai Jam'iyyarsa Kara Wajen Hukumar EFCC Kan Zargin Damfarar Naira Miliyan 20.Wan...
10/06/2026

LABARI DA DUMI-DUMI: Dan Takarar NDC Ya Kai Jam'iyyarsa Kara Wajen Hukumar EFCC Kan Zargin Damfarar Naira Miliyan 20.
Wani dan takarar majalisar dattawa (Sanata) da ke fushi a jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ya shigar da korafi gaban Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Ta’annuti (EFCC), inda yake zargin mambobin kwamitin tantance 'yan takarar sanata na jam'iyyar da laifukan zamba, damfara, da hadakar baki don tafka laifi da ya shafi Naira miliyan 20.

Ofishin Shugaban Hukumar EFCC ne ya karbi takardar korafin a babban sakatariyar hukumar da ke Abuja a ranar Talata.

Wannan lamari ya faru ne biyo bayan wasu zarge-zarge da jarumin fina-finai kuma dan siyasa, Kenneth Okonkwo ya yi kwanan nan. Shi dai Okonkwo yana tsaka da takaddama da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, bayan ya yi zargin cewa shugabannin jam'iyyar sun kafa wani tsari na karbar kudaden dole a hannun masu neman takara.

Bisa ga hujjojin da wani shafi na tona asiri mai suna Pidomnigeria ya fallasa a dandalin X (wanda aka sani da Twitter da), dan takarar da farko ya sayi fom din nuna sha'awar tsayawa takara na hukumar jam'iyyar akan kudi Naira miliyan 3, inda ya bi dukkan ka'idojin da shugabannin jam'iyyar s**a gindaya.

Sai dai, bayan isarsa Abuja don gudanar da tantancewar dole, an zargi kwamitin da tilasta wa dan takarar sanya hannu kan wata takardar rantsuwa ta doka, inda ya yi alkawarin amincewa da duk wani hukunci da kwamitin zai yanke, sannan kuma ya janye hakinnsa na kai jam'iyyar NDC gaban kotu don neman hakki.

Ya ce: “Da isarsa Abuja, s**a ba shi wani fom ya sanya hannu cewa zai amince da duk abin da kwamitin tantancewar ya yi, kuma ba zai kai NDC kotu ba. Ya yi mamaki, amma duk da haka ya sanya hannun. Ya zata za su tantance shi ne bisa la'akari da aikinsa na kwarewa, gogewarsa ta siyasa, tasirinsa ga mutanen karkara, ayyukansa na baya, da takardun shaidar karatu da ya mallaka, da sauran su.

“Amma abin mamaki, sai s**a fara tambayarsa game da bayanan asusun bankinsa (bank statement), adadin gidaje da kadarorin da ya mallaka, motoci da zuba jari, da kuma karfinsa na kudi.

“S**a shaida masa cewa lallai sai ya nuna bajinta da karfin kudi idan har da gaske yake yana son zama sanata. S**a rubuta masa bayanan asusun banki na FCMB, s**a ce ya biya tsabar kudi Naira miliyan 20,000,000 a ciki. Ya biya kudin, kuma tun daga ranar NDC ta rufe masa kofofinta har zuwa yau.

“Yanzu haka yana neman jam'iyyar da ta mayar masa da kudinsa Naira miliyan 20,000,000, kuma ya shigar da korafi a kansu wajen hukumar EFCC.”

Rahoranni sun bayyana cewa kwamitin ya tsananta wa dan takarar da tambayoyi game da asusun bankinsa, gidajen da ya mallaka, motocinsa, da sauran guraren da ya zuba jari, duk a karkashin sunan tantance karfinsa na kudi na tsayawa takara.

Bayan tantance karfinsa na kudi, an zargi kwamitin da ba wa dan takarar lambar asusun banki na First City Monument Bank (FCMB) ba tare da ba shi rasit ba, inda s**a umarce shi da ya tura Naira miliyan 20 cikin gaggawa domin ya tabbatar da samun gurbin takarar. Dan takarar ya cika wannan umarni, amma bayan nan sai shugabannin NDC s**a yanke dukkan wata alaka ta gudanarwa da shi.

Okonkwo ya bayyana irin wadannan zarge-zarge a kwanan nan. Kafin nan, Okonkwo ya taba raba wasu bayanan sirri na cikin gida daga wajen wani dan takarar Majalisar Wakilai, Obunike Ohaegbu, wanda shi ma ya yi zargin cewa jam'iyyar ta yi amfani da wasu kungiyoyin daidaita alamura na jiha (parallel state caucus structures) wajen neman Naira miliyan 10 daga hannun masu neman takarar Majalisar Wakilai da kuma Naira miliyan 20 daga hannun masu neman takarar Sanata, kafin a tattara jerin sunayen 'yan takarar a asirce a Otal din Johnwood da ke Abuja.

Me ake nifi da Minab 168'Yan wasan ƙwallon ƙafar Ir@n da za su halarci gasar Kofin Duniya sun isa ƙasar Mexico suna sany...
10/06/2026

Me ake nifi da Minab 168
'Yan wasan ƙwallon ƙafar Ir@n da za su halarci gasar Kofin Duniya sun isa ƙasar Mexico suna sanye da tambarin ƙirji (lapel pins) domin tunawa da waɗanda s**a mut¥ a wani hari mai muni da aka kai wa makarantar firamare a Minab a farkon yaƙin Gabas ta Tsakiya.

'Yan wasan sun sanya tambarin zinariya mai ɗauke da lambar “168” a jikin jaket ɗinsu lokacin da suke sauka daga jirginsu a birnin Tijuana na Mexico ranar Lahadi. Wannan lambar tana nufin mutane 168 da s**a mut¥, mafi yawansu yara ne, a harin da ya afkawa makarantar a Minab da ke kudancin Ir@n a ranar 28 ga Fabrairu.

Ofishin jakadancin Ir@n da ke Hungary ya yi nuni da waɗannan tambura a wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta ranar Litinin, tare da ambaton Minab.

Tun a baya, tawagar Ir@n ta riga ta yi wani taron tunawa da waɗanda s**a mut¥ a harin makarantar kafin wasan sada zumunci da s**a buga a watan Maris a Antalya, Turkiyya. A lokacin, 'yan wasan sun ɗaga jakunkunan makaranta masu ruwan hoda da shunayya yayin da ake kunna taken ƙasarsu.

Amurk@ da Isra'il@ ba su amince da alhakin kai harin makarantar ba. Harin ya fuskanci s**a mai tsanani daga Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama.

Kungiyar Kwadago Ta Najeriya (NLC) Ta Sanya Ranar Fara Sabuwar Tattaunawa Kan Mafi Karancin Albashi Na Kasa.Kungiyoyin k...
09/06/2026

Kungiyar Kwadago Ta Najeriya (NLC) Ta Sanya Ranar Fara Sabuwar Tattaunawa Kan Mafi Karancin Albashi Na Kasa.

Kungiyoyin kwadago na kasar nan sun sanya watan Yuli na shekarar 2026 a matsayin lokacin da za su fara sabuwar tattaunawa da gwamnatin tarayyar Najeriya kan mafi karancin albashi na kasa.

A cewar kungiyar kwadagon, mafi karancin albashi na yanzu da ake biya da ya kai ₦70,000 ya daina aiki kuma bai dace da yanayin tattalin arzikin da ake ciki a kasar ba a halin yanzu.

Wannan matsaya ta hadakar kungiyoyin kwadagon, wadda ta kunshi Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) da kuma Kungiyar Shugabannin Ma’aikata (TUC), ta fito ne a yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da s**a gudanar a gefen taron kasa da kasa na kwadago karo na 114 (114th International Labour Conference) da ake gudanarwa a birnin Geneva na kasar Switzerland.

Haka zalika, kungiyoyin kwadagon sun nuna gamsuwarsu da yadda gwamnonin jihohi s**a gane cewa mafi karancin albashin na yanzu bai isa ya biya bukatun yau da kullum na ma'aikata ba, sai dai sun yi kira gare su da kada su gaggauta sanya wani kayyadadden farashi, a maimakon haka su jira har sai an bi hanyoyin da s**a dace.

Taruka guda Uku da basu da amfani a yanzu.Daga shafinHassan Nasir Musa GwammajaTaron Old BoysTaron FamilyTaron Cigaban U...
01/06/2026

Taruka guda Uku da basu da amfani a yanzu.

Daga shafin
Hassan Nasir Musa Gwammaja

Taron Old Boys
Taron Family
Taron Cigaban Unguwa.

Taron Old Boys tarone da akeyi aga yanda rayuwa tayi da wasu bayan rayuwar makaranta, a dora masu shadda me kyalli a hightable haka za'a tashi ba agenda sai wata shekarar a turo maka account kasa kudin taro.

Taron Family shima kusan tafiya daye suke dana makaranta banbancin kawai shi sai annuna an Isa dakai amma Yayan masu kudin family sune taurari a wajen karshe kafin a tashi babansu za'aita godewa a mic.

Taron unguwa kuwa idan kaga an Kira taro wani ne ya zama dan iska tuburan sunga zai bata musu Y'ay'a amma bazaka tabajin an taru domin a biyawa yara kudin Jamb, Waec ko Neco ba, duk taron masu kudin wnanan unguwa baza kaji sunce zasu dauki masu hankalin layinsu kasuwa ko makaranta ko masu degree su dauke su aiki ba, haka za'ai taron ai ta tsinewa yaron da s**a lalace karshe idan megidan ya mutu kaji ana ai dama Alhaji wane ne ya siyi gidan.

Jama'a yanzu fa muna karni na 21 Wanda zai taimake ka bazai wahalar dakai ba shiyasa akayi Opay da Moniepoint dan haka a daina doraku a igiyar zato da taron iska da wofi.

~Hassan Nasir Musa Gwammaja

Gwamnoni sun bukaci Gwamnatin Tarayya da ta duba yanayin kara albashi ya kai 100,000 a matsayin mafi karancin Albashi ga...
31/05/2026

Gwamnoni sun bukaci Gwamnatin Tarayya da ta duba yanayin kara albashi ya kai 100,000 a matsayin mafi karancin Albashi ga ma'aikata. Saboda rage radadin matsin tattalin arziki.

Ana ta cecekuce:Waye zai iya rike Amana
28/05/2026

Ana ta cecekuce:
Waye zai iya rike Amana

Ba wani a duniya da ya isa ya tsare ko ya natsuwa a zuciyar Dan Adam sai Allah.Wannan shugaban kasa ne a nan Africa ya j...
28/05/2026

Ba wani a duniya da ya isa ya tsare ko ya natsuwa a zuciyar Dan Adam sai Allah.
Wannan shugaban kasa ne a nan Africa ya je aikin Hajjin bana.
Shugaba Alasan Quatara.

26/05/2026

Yau ce ranar Arfa:
Yan'uwa Musulmai mu yawaita Anbaton Allah da Addu'oi, da fatan Allah ya karba mana amin.

ZANANAN BUNGUDU: Dan majalisar Tarayya zai kaddamar da kuma bude Asibitin da ya gyara.Rahoton - Shafiu Ibrahim maikatifa...
23/05/2026

ZANANAN BUNGUDU: Dan majalisar Tarayya zai kaddamar da kuma bude Asibitin da ya gyara.

Rahoton - Shafiu Ibrahim maikatifa

Kwamitin Mai Girma Dan Majalisar tarayya Mai Wakiltar Kananan Hukumomin Maru da Bungudu Hon. Abdulmalik.Zannan Bungudu Zai Kaddamar da Asibitin Kula da Lafiya Matakin Farko Dake Garin Jabaka na Karamar Hukumar mulkin Maru Wacce Dan Majalisar Ya Gyara tare da Hannuntata Ga Hukumar wannan Asibiti.

karshen rahoton kenan
Shafiu Ibrahim maikatifa

Ziyara ta Diflomasiyya:Shugaban Amurka ya kai Ziyara ChinaShugabar Rasha ya kai Ziyara ChinaYanzu kuma Shugaban China za...
22/05/2026

Ziyara ta Diflomasiyya:

Shugaban Amurka ya kai Ziyara China

Shugabar Rasha ya kai Ziyara China

Yanzu kuma Shugaban China zai kai Ziyara Korea

To wai me hakan ta ke nufi

Ku bayyana mana ra'ayinku a comment section ko menene ma'anar hakan

Address

Titin Aisha Block, Kofar Dawanau

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when MW Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share