
28/04/2025
Hausa
Daga Ofishin Sanata Natasha Akpoti Uduaghan
Mai Girma Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio,
Da girmamawa mai cike da kwaikwayo da ɗan murmushi nake rubuta wannan wasikar na “ba da hakuri” saboda babban laifin da nayi a gaban majalisarka mai tsarki.
Na yi dogon tunani game da wannan babban kuskure na rashin fahimtar cewa nasara a majalisa a wasu lokuta, ba ta hanyar kwarewa ake samun ta ba, sai dai ta hanyar ƙwarewar bin umarni kai tsaye.
Yayi muni yadda ban gane cewa ƙin amsa “buƙatunku” ba kawai ra'ayi na bane, amma tamkar karya wata doka ce ta al’adar wasu mazaje masu jin suna da iko da komai.
Ina ba da hakuri saboda fifita cancanta akan yarda da zalunci, hangen nesa akan son zuciya, da kuma biyayya ga amanar jama’a akan cin amana a bayan fage.
Yanzu na gane illar da na haifar: tsaikon dokoki, ɓacin rai, da raunana girman kai da ya fi girman birane har yana buƙatar sabon lambar adireshi kansa.
Don wannan rikitarwa da na kawo a tsarin "kai min, in ba ka," ina sunkuyar da kaina cikin rashin gaskiya da kuka na.
Don Allah, ka samu cikin zuciyarka mai cike da takama — inda take ɓoye ƙasan zurfin jin kai — ka yafe wa wannan Mace mai taurin kai wadda ta yi imani cewa kujerarta a majalisa ta samu ne ta hanyar zaɓe, ba ta hanyar wasu “zaɓuka” na daban ba.
Ina nan,
A matsayin mara tsoro, mai ƙin sayar da kai.
Sanata Natasha H Akpoti