28/06/2026
Gidauniyar Gumel Emirate Foundation ta buƙaci gwamnatin Jihar Jigawa da ta faɗaɗa tare da inganta titin Maigatari zuwa Gumel zuwa hanya mai layuka biyu (dual carriageway), domin karɓar ƙarin zirga-zirgar kasuwanci da ake sa ran za ta ƙaru sak**akon farfaɗo da Kasuwar Export Processing Zone (EPZ) da ke Maigatari.
Shugaban Kwamitin Amintattu na gidauniyar, Alhaji Mohammed Sani Ahmed, Dan Amar na Gumel, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar manema labarai.
Ya ce farfaɗo da aikin EPZ da Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yi, babban ci gaba ne ga tattalin arzikin jihar.
A cewarsa, aikin wanda ya kwashe sama da shekaru ashirin yana cikin halin dakushewa, yanzu ya zama wani muhimmin mataki na bunƙasa masana’antu, jawo hannun jari da samar da ci gaban tattalin arziki ga al’ummar jihar da yankin baki ɗaya.
Alhaji Mohammed Sani Ahmed ya yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa hangen nesansa da jajircewarsa wajen sauya fasalin tattalin arzikin jihar ta hanyar samar da ingantattun ababen more rayuwa da kuma kyautata yanayin kasuwanci.
Ya kuma bayyana jin daɗin gidauniyar kan yadda masu zuba jari daga ƙasashen waje, ciki har da wasu kamfanoni masu goyon bayan kasar Sin, s**a fara shiga cikin aikin bunƙasa yankin. Ya ce hakan zai taimaka wajen ƙara saka hannun jari, faɗaɗa masana’antu, haɓaka fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje da kuma samar da dubban guraben ayyukan yi ga matasa.
Dan Amar na Gumel ya jaddada cewa al’ummar Masarautar Gumel za su ci gaba da ba gwamnati da masu zuba jari cikakken goyon baya domin tabbatar da tsaro da dorewar aikin, tare da samar da yanayi mai kyau da zai bai wa harkokin kasuwanci damar bunƙasa.
Ya sake bayyana godiyar gidauniyar ga Gwamna Umar Namadi kan wannan gagarumin aiki, yana mai cewa al’ummar Gumel da Jihar Jigawa za su ci gajiyar dimbin alfanun da aikin zai samar nan gaba.
A wani ci gaban kuma, Gidauniyar ta Masarautar ta Gumel ta yabawa gwamnatin Jihar Jigawa kan kafa Cibiyar Kyauta ta Wankin Koda (Dialysis Centre) a Babban Asibitin Gumel.
Alhaji Mohammed Sani Ahmed ya ce wannan mataki shaida ce ta gwamnatin da ke sanya jin daɗin jama’a a gaba, musamman wajen samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga marasa galihu.
Ya bayyana cewa cututtukan koda na daga cikin matsalolin lafiya mafi tsada wajen magani, inda kudin wankin koda ke zama babban ƙalubale ga marasa lafiya da iyalansu. Saboda haka, samar da wannan hidima kyauta ya rage musu nauyin kuɗi tare da dawo musu da fata.
A cewarsa, cibiyar ba wai kawai aikin kiwon lafiya ba ce, har ila yau jari ne na ceton rayuka da bunƙasa albarkatun ɗan Adam. Ya ƙara da cewa tun bayan fara aiki a watan Janairun 2026, mutane 53 sun amfana da cibiyar, yayin da aka gudanar da jimillar zaman wankin koda 383, lamarin da ya nuna muhimmancin cibiyar ga al’umma.
Sai dai ya buƙaci gwamnatin jihar da ta samar da tsarin hasken rana (Solar Power System) a cibiyar domin tabbatar da wadataccen wutar lantarki ba tare da katsewa ba, tare da rage kuɗaɗen gudanarwa domin cibiyar ta ci gaba da sauke nauyin da aka ɗora mata yadda ya k**ata.