Dare Dubu Media & Co

Dare Dubu Media & Co DRC Hausa Shafi Ne Dake Kawo Muku Labarai Da Dumi Dumin Su, Bincike Tareda Tattauna Batutuwa Das**a Shafi Rayuwar Al'umma

DALILAI 10 DA YASA MATA S**A FI SON NAMIJIN DA BAYA SON SU:Idan na fada muku gaskiyar yadda kwakwalwar mace take aiki, w...
23/09/2026

DALILAI 10 DA YASA MATA S**A FI SON NAMIJIN DA BAYA SON SU:

Idan na fada muku gaskiyar yadda kwakwalwar mace take aiki, wasu zasu dauka tsana ce. Amma zahirin magana shi ne: Mata da yawa suna kyamatar namijin da yake durkusa musu da tsantsar kauna, su koma suna haukatar da kansu a kan wanda bai ma san da zamansu ba.

Ga dalilan da yasa hakan take faruwa:

1.
Kalubale: Mace ba ta son abin da yake zuwa mata da sauki. Namijin da baya nuna damuwa, yakan zama k**ar wani babban kofi na trophy da take son lashewa don ta tabbatar da cewa kyanta yana aiki.

2.
Rashin Zakuwa: Namijin da yake nuna zakewa yana nuna rauni a idonsu. Amma wanda yake tafiyarsa yana nuna cewa rayuwarsa tana tafiya daidai koda babu ita, wannan rashin damuwar ita take tayar musu da hankali.

3.
Gasa a Tsakanin Mata: Idan mace ta ga baka damu da ita ba, lissafinta yana bata cewa akwai wasu matan da kake bawa kulawa. Wannan tunanin na gasa shi yake rura wutar son ta mallake ka.

4.
Kwarjini Da Jan Aji: Namijin da ya cika yi wa mace bayanin komai yana rasa kwarjininsa. Wanda yake yin shiru bai cika magana ba, shi ne yake sa ta raba dare tana tunanin waye shi a zahiri.

5.
Raunin Motsin Zuciya: Rayuwa da namijin da yake nuna kauna dari-bisa-dari tana basu gajiya saboda babu wani sabon abu. Suna son wanda zai sa su fargaba yau, gobe ya sa su dariya; wannan shi yake sa su ji suna raye.

5.
Karyar "Zan Iya Canza Shi": Wata irin dabi'a ce ta son nuna karfi. Mace takan so ta auri taurin kan namiji da nufin cewa ita kadai ce zata iya yin amfani da dabarunta wajen sassauta shi.

6.
Yawan Kulawa Yana Kawo Raini: Idan ka mayar da mace ita ce duniyarka ta hanyar yi mata bauta, zata fara kallonka a matsayin mara aikin yi. Amma wanda yake watsar da ita yana fuskantar abin gabansa, shi ne take kallo a matsayin namiji mai tsari.

7.
Kuskuren Fahimtar Karfi: Mata da yawa suna fassara nuna ko-in-kula a matsayin tsantsar karfin 'Da Namiji. Suna ganin wanda bai damu da zafin soyayya ba, shi zai fi basu kariya a rayuwa.

8.
Yaudarar Hankali wato Reverse Psychology: A dabi'ance, zuciya tana gudu ne zuwa ga abin da yake guje mata, sannan tana tattaka abin da yake rarrafe a gabanta yana rokon ta.

9.
Tabbacin Daraja: Namijin da baya nuna tsoron rasa mace, ya riga ya tabbatar da cewa darajarsa tana da girma. Ita kuma mace kullum burinta ta hada inuwa da wanda darajarsa ta fi tata.

A matsayinka na 'Da Namiji, ka daina gina rayuwarka a kan lallashin mace ko bauta mata don neman yardarta. Ka Gina kanka, ka fuskanci neman na kai, ka ajiye tsarin kanka. Idan ka zama wani abu, su da kansu za su neme ka.
UMAR ALIYU DAHIRU ✍️

22/09/2026
Wani magidanci ya tambayi matarsa rancen dubu biyu (2000) zaiyo musu cefane, sai tace bata da kudi ya fita yabar gidan. ...
16/09/2026

Wani magidanci ya tambayi matarsa rancen dubu biyu (2000) zaiyo musu cefane, sai tace bata da kudi ya fita yabar gidan.

Ba'a dade ba sai ga wani yaro ya shigo gidan ya kawo tallar maganin mallakar miji, da kuma hana shi kara aure ko wanne dubu biyu (2000).

Sai matar ta dauki duka guda biyun, ya k**a dubu hudu ke nan (4000) ta biya kudin.

Ashe layune guda biyu, yaron yace bayan awa daya ta kwance ta jika a ruwa ta bawa megidanta ya sha.

Ai kuwa tana kwance kullin farko sai taga an rubuta "Allah ya baki ikon yiwa mijinki biyayya".

Sai ta kwance ta biyun, sai taga an rubuta "Daga mijinki baban Khadija yau cefananki harda tantakwashi zan kawo miki".

✍️ Sa'idu Aliyu

Senator Shehu Buba Umar,  Kuma Dan Takara Gwamna Jahar Bauchi a Jam'iyar PRP Wanda ake zargi da Daukar nauyin Yan'ta'add...
16/09/2026

Senator Shehu Buba Umar, Kuma Dan Takara Gwamna Jahar Bauchi a Jam'iyar PRP Wanda ake zargi da Daukar nauyin Yan'ta'adda da Ta'addanci ya fito ya wallafa wani Rubutu a Shafin sa Kamar haka.

Senator Shehu Buba Umar yace.

" Na kalubalanci duk mai hujja akan zargin da akemin ya rufamin Asiri Allah ya Isa"

Wannan Shine saqon daya wallafa Cewa ya Kalubalanci duk Wanda duk yake da wata Hujja akansa Bisa Zargin da akemasa inya Rufa Masa Asiri bai yafe ba inji shi senator Shehu Buba Umar.

Me kuka Fahimta da wanna sakon?

Atiku ya yi alkawarin binciken kwakwaf kan N33.75bn da aka raba wa ƴan NajeriyaTsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Ab...
06/09/2026

Atiku ya yi alkawarin binciken kwakwaf kan N33.75bn da aka raba wa ƴan Najeriya

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin kafa tawaga ta ƙwararru masu zaman kansu domin sake duba sak**akon binciken da ya shafi rabon Naira biliyan 33.75 ga gidaje miliyan 3.29 masu fama da ƙalubalen tattalin arziki.

Atiku ya ce tawagar za ta ƙunshi ƙwararru a fannonin kuɗi, binciken lissafi, fasahar zamani da lissafin kuɗaɗen gwamnati.

Binciken zai mayar da hankali ne kan yadda aka kashe da kuma yadda aka raba kudaden da aka ware ƙarƙashin shirin tallafin kuɗi kai tsaye na Gwamnatin Tarayya.

Wanda a ka ce an baiwa gidaje miliyan 3.29. 25,000 kowanne .

06/09/2026

Yadda Twagar Dan Takarar Gwamnan Borno Sukayi Jungum Jungum, Masu Tada Kayar Baya Sun Tareda Hanya Anata Tarwatsa B0ma B0mai

"Kada Kuyi Ganganci Na Kin Sake Zaben Tinubu, Hakan Babban Kuskure Ne" Acewar Dan Majalisar ZariaKakakin Majalisar Wakil...
05/09/2026

"Kada Kuyi Ganganci Na Kin Sake Zaben Tinubu, Hakan Babban Kuskure Ne" Acewar Dan Majalisar Zaria

Kakakin Majalisar Wakilai Tajiddeen Abbas ya ce rashin sake zaɓar Tinubu zai zama babban kuskure

Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce ’yan Najeriya za su yi babban kuskure idan ba su sake zaɓar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 ba.

Abbas ya ce gwamnatin Tinubu na aiwatar da ayyukan raya ƙasa da dama, yana mai cewa ya k**ata ’yan Najeriya su duba irin ci gaban da ake samu kafin yanke shawarar wanda za su zaɓa.

Ya ƙara da cewa sake zaɓar Tinubu zai bai wa gwamnati damar ci gaba da ayyukan da ta fara.

ME YASA JAMI'AN ƳAN SANDA KE TURURUWA AJIYE AIKI?🔥🔥🔥TAKARDAR AJIYE AIKI DA CORPORAL YUSUF ALIYU YA AIKA WA RUNDUNAR YAN ...
05/09/2026

ME YASA JAMI'AN ƳAN SANDA KE TURURUWA AJIYE AIKI?🔥🔥🔥

TAKARDAR AJIYE AIKI DA CORPORAL YUSUF ALIYU YA AIKA WA RUNDUNAR YAN SANDA BAYAN SHEKARU BIYU BA TARE DA ALBASHI BA.

Jami’in, wanda ke aiki a matsayin Corporal mai lambar aiki F/No. 524180 a sashen ƴan sanda na Dambam, ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin aikin ne sak**akon matsalar albashinsa da ya ce ta dauki tsawon shekaru biyu ba tare da an warware ta ba.

A cikin takardar da ya aika wa Rundunar Ƴan Sandan Jihar Bauchi da hedikwatar rundunar da ke Abuja, jami’in ya ce duk da cewa albashinsa yana nunawa cewa an sarrafa kuma an biya shi, bai iya shiga ko cire kudin ba, duk da kokarin da ya ce ya yi ta hanyoyin da s**a dace.

Ya ce lamarin ya jefa shi cikin matsanancin hali na rashin kudi tare da sanya masa wahalar gudanar da bukatun kansa da na iyalinsa, lamarin da ya sa ya rasa kwarin gwiwa kan tsarin.

A takardar mai kwanan wata 30 ga Agusta, 2026, jami’in ya sanar da cewa murabus dinsa zai fara aiki ne daga ranar 30 ga Satumba, 2026.

Ya kuma nuna godiya ga Rundunar Ƴan Sandan Najeriya bisa damar da ta ba shi na yi wa kasa hidima, tare da alkawarin mayar da duk wani kayan gwamnati da ke hannunsa kafin ranar barinsa aiki.

INDA RANKA: Yadda wasu mabiya Shi'a a Jihar Katsina s**a kwaikwayi salon yadda hukumar EFCC ke tsare da tsohon Gwamnan J...
05/09/2026

INDA RANKA: Yadda wasu mabiya Shi'a a Jihar Katsina s**a kwaikwayi salon yadda hukumar EFCC ke tsare da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Kuma Jigo A Jam'iyyar ADC Malam Nasiru El-rufai.

📷- Yantandu

Address

Kano
Kano

Telephone

+2347032362833

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dare Dubu Media & Co posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Dare Dubu Media & Co:

Shortcuts

Share