30/03/2026
📌 MENENE TELEGRAM PONZI?
Telegram Ponzi wata irin damfara ce da ake yi ta amfani da manhajar Telegram, inda masu damfara ke kirkirar group ko channel suna yaudarar mutane da cewa za su samu riba cikin sauri.
⚠️ YADDA SUKE AIKI
Za su ƙirƙiri group mai suna k**ar:
“Crypto Investment”
“Double Your Money”
“VIP Earnings”
Za su saka hotunan karya na:
kuɗi
bank alerts
shaidu na ƙarya
Za su ce: 👉 Ka saka ₦5,000 → zaka samu ₦15,000 cikin awa 24
Wasu lokuta suna biyan mutum ɗaya ko biyu don su yaudari sauran mutane
Da zarar mutane da yawa sun saka kuɗi… ❌ Sai su ɓace (su rufe group ko su block kowa)
🚨 ALAMOMIN TELEGRAM PONZI
Alkawarin riba mai yawa cikin gajeren lokaci
Babu cikakken bayani na kamfani
Ana matsa maka da sauri ka saka kuɗi
Babu wani tabbacin doka (no license)
Ana amfani da “admin” kawai, babu office ko adireshi
🛑 YADDA ZAKA KAUCEWA
✔️ Kada ka yarda da “get rich quick”
✔️ Kada ka tura kuɗi ga wanda baka sani ba
✔️ Ka bincika kafin ka saka kuɗi
✔️ Ka guji groups da ke tilasta maka ka biya cikin gaggawa
✔️ Ka tambayi kwararru ko masu ilimi kafin ka shiga
💡 MUHIMMIN SAKO
👉 Duk inda aka ce: “Ka saka kuɗi ka samu ninki biyu cikin sauri” 👉 Kashi 90% damfara ce!
📣 KARSHEN SAKO
Ka taimaka ka wayar da kai: 👉 Ka raba wannan sako domin kare ‘yan uwa daga fadawa damfara