Comr. ADAM M ADAM

Comr. ADAM M ADAM Writer and digital creator

A ƙasar FINLAND1. Duk malamin da zai koyar a firamare wajibi ne ya kasance yana da digiri na biyu.2. Iyayen yara ne suke...
13/08/2024

A ƙasar FINLAND

1. Duk malamin da zai koyar a firamare wajibi ne ya kasance yana da digiri na biyu.

2. Iyayen yara ne suke da haƙƙin zaban Hedimasta.

3. Wajibi ne kowane yaro a saya masa Computer, don ba a amfani da littafi.

4. Ɗalibai 20 kaɗai a kowana Aji.

5. Muhadara 5 kaɗai kullum.

6. Albashin Malamin Firamare yafi na shugaban ƙasa yawa.

7. Ba a jarrabawar ƙarshen zango. Malami yana fitar da sakamakon ɗalibai ne gwargwadon aikin da s**a gabatar a zangon karatu.

8. Malamin Firamare yana da KATI na musamman wanda yake amfani da shi wajen siyayya kuma duk abin da ya siya rabin kuɗin zai biya.

✍️ Sukairaj Hafiz Imam

Ana rade-radin cewa Buhari da wasu tsofaffin shugabannin Najeriya sun bawa Tinubu shawara akan ya dawo da tallafin Man F...
13/08/2024

Ana rade-radin cewa Buhari da wasu tsofaffin shugabannin Najeriya sun bawa Tinubu shawara akan ya dawo da tallafin Man Fetur don samun saukin rayuwar halin kuncin da 'yan Najeriya suke ciki, a yayin ziyarar da s**a kaiwa Tinubu yau a fadar shugaban kasa, saidai ana zargin kafafen yada labarai na fadar shugaban kasar sunki yada labarin.

28/03/2024

Ajiya ne Tinubu ya karbo bashin ¥15bn daga kasar Japan, Najeriya za ta shafe shekaru 30 tana biyan bashin, inji Ministan kudi Wale Edun.

Jerin ƙasashen da a dakatar da hada-hadar kasuwancin Binance 1. United Kingdom2. Japan3. Italy4. Canada5. Belgium6. Nige...
25/03/2024

Jerin ƙasashen da a dakatar da hada-hadar kasuwancin Binance

1. United Kingdom
2. Japan
3. Italy
4. Canada
5. Belgium
6. Nigeria
7. Australia
8. India
9. Netherlands
10. Thailand
11. Philippines
12. Germany
13. France
14. Bangladesh
15. Iran
16. Vietnam
17. Kazakhstan
18. Malaysia
19. China

# Arewa

25/03/2024

Jikina saida yayi sanyi da naga an kara kudin aikin Hajji da yawa haka. Ya Allah muna rokonka da ka h**e mana ka bamu ikon biya ko nawa s**a maidashi.

25/03/2024

Dala ta dawo 1,370 a kasuwar bayan fage.

25/03/2024

An kara kudin aikin Hajji daga Naira miliyan 4.5M zuwa Naira miliyan 6.4M.

25/03/2024

Duk wanda zai biya kudin aikin Hajji a yanzu Naira miliyan 8.2M zai biya. Duk wanda ya riga da ya biya miliyan 4.9M an bashi wa'adin kwanaki hudu da ya gaggauta cika miliyan 1.9M kudinshi ya zama miliyan 6.4M, idan ba haka ba a dawo mishi da kudin shi, inji hukumar.

25/03/2024

Allah ya kyauta

ALLAH YA KYAUTAWani attajirin mai kudi ya fitar da kayan abinci zai rabawa mabukata a cikin garin BauchiMutane maza da m...
24/03/2024

ALLAH YA KYAUTA

Wani attajirin mai kudi ya fitar da kayan abinci zai rabawa mabukata a cikin garin Bauchi

Mutane maza da mata sun fi dubu 10 s**a je gurin rabon kayan abincin, a gurin turmutsitsi aka turmutse wannan yarinya ta rasa rayuwarta

Mahaifin yarinyar yana aiki a Asibiti, an tambayeshi yace ba da izninsa yarinyar ta fita ba, ya bar wa Allah Ya masa sakayya tsakaninsa da wanda yayi sanadin rasa rayuwar 'yar sa

Ya kamata masu rabon kayan abinci wa mabukata su ji tsoron Allah su gyara tsarin rabon kayan abinci da suke yiwa talakawa

Muna adawa da yadda ake fito da dubbanin matan mutane zuwa gurin rabon abinci, ayi ta daukarsu a hoto ana yadawa a duniya saboda riya

Da wanda Allah Ya bashi rufin asiri da wanda Allah Ya hanashi rufin asiri duka jarrabawa ne, ba wanda yafi karfin Allah Ya jarrabeshi, ku dena amfani da damar da Allah Ya baku kuna wulakanta matan mutane

Muna fatan Allah Ya jikan wannan yarinya

ABIN TAUSAYI: Hotunan wasu daga cikin Daliban makarantar Kuriga ta jihar Kaduna da sojojin Najeriya s**a kubutar.
24/03/2024

ABIN TAUSAYI: Hotunan wasu daga cikin Daliban makarantar Kuriga ta jihar Kaduna da sojojin Najeriya s**a kubutar.

Cikin daren jiya barayi sun fasa Masallaci sun shiga sun sace Inverter ta Solar da ake amfani da ita a masallacin. Abun ...
24/03/2024

Cikin daren jiya barayi sun fasa Masallaci sun shiga sun sace Inverter ta Solar da ake amfani da ita a masallacin. Abun ya faru ne a masallacin Layin Akogo Street dake Kwanar Dan-Goma.

21/03/2024

Sojojin Nijar sun umurci a bude boda kamar yadda Nijeriya ta bude tata

Amma sun ce a karfafa matakan tsaro wajen shige da fice

13/03/2024

'Yan ta'adda sun sake sace mutane 62 a Kajuru jihar Kaduna bayan sun kashe wasu.
Ya Allah Ka Bamu mafita Albarkacin mazan Allah S.A.W

13/03/2024

Shin Don Allah yaya iyayen yara 320 da aka sace za suji? Shin kuna ganin zasu iya bacci cikin kwanciyar hankali?

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Comr. ADAM M ADAM posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share