Daginawa Media News

Daginawa Media News Labarai Da tallace-tallace

27/01/2025

Wacce suna'a zakayi da jarin million 1 ka dinga samun Dubu 10 kullum?

Napoli ta yanke shawarar kin mayar da Victor Osimhen cikin tawagar taHukumomin kulab din na Seria A sun tabbatar da huku...
01/09/2024

Napoli ta yanke shawarar kin mayar da Victor Osimhen cikin tawagar ta

Hukumomin kulab din na Seria A sun tabbatar da hukuncin a daren ranar Asabar, kamar yadda masanin harkokin kwallon kafa Fabrizio Romano ya bayyana.

Napoli ta tabbatar da cewa ba ta da wani shiri na sake cigaba da amfani da Victor Osimhen a cikin tawagar.

Fabrizio Romano ne ya tabbatar da hakan a shafin sa na X,kamar yadda kungiyar ta bayyana a daren lahadi.

Manajan kungiyar Antonio Conte ya bayyana takaicin sa kan gazawar kungiyar ta siyar da Osimhen a kakar wasan da ta gabata.

Kungiyar ta Napoli ta maye gurbin Osimhen da Romelu Lukaku da ke benci a kungiyar wanda ya basu nassara a wasan da s**a yi a makonnan.

Kwankwaso da Ganduje sun ga juna ido-na-ganin-ido yayin da s**a halarci daurin auren ‘yar Atiku Abubakar a Juma'ar nan
23/08/2024

Kwankwaso da Ganduje sun ga juna ido-na-ganin-ido yayin da s**a halarci daurin auren ‘yar Atiku Abubakar a Juma'ar nan

Daga jiya zuwa yau nagani a gidajen jaridun kasar nan sun buga almajiran Sheikh Zakzaky sunyi tattakin da s**a Saba guda...
22/08/2024

Daga jiya zuwa yau nagani a gidajen jaridun kasar nan sun buga almajiran Sheikh Zakzaky sunyi tattakin da s**a Saba gudanarwa duk Shekara. Ance Bana har jagoran nasu yafito dukda shi ba anan kasar ya gudanar da Nashi ba.

Abunda ya burgeni dasu shine tsarinsu, duk yawansu banji ance an samu matsalar fasa shagon Wani ba ko wawashe dukiyar bayin Allah talakawa Yan uwanmu ba.

Mizai Hana duk abunda zamuyi mu Dunga koyi da bayin Allahn nan wallahi tsarinsu Yana burgeni tabbas idan mukabi tsarinsu wajen kawoma kasarmu ci gaba gami da tabbatar da adalci tohm zamuyi Nasara sosai domin kuwa inada tabbaci tsarinsu bazai ta6a bari waninsu ya mana son rai ba.

_Cewar Ƴar Jaridar Hafsat Abdullahi

Gwamnatin jihar kano ta ƙaddamar da kwamitin kar-ta kwana domin aiwatar da riga-kafin cutuka masu yaɗuwa a lungu da sako...
22/08/2024

Gwamnatin jihar kano ta ƙaddamar da kwamitin kar-ta kwana domin aiwatar da riga-kafin cutuka masu yaɗuwa a lungu da sako na jihar Kano.

Da yake kaddamar da kwamitin a gidan gwamnati, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce an kafa kwamitin ne domin dakile cutukan dake baraza ga lafiyar yara da mata da sauran al'uma.

Yace wakilan kwamitin wanda zasu kasance karkashin jagorancin mataimakin gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, zasu dinga kewayawa birni da karka domin aiwatar da riga-kafin tarin fuka da mashako da sauran cutuka masu saurin yaduwa a tsakanin al'uma.

Daga nan ya yi kira ga wakilan Kwamitin da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu da yadda za a samu al'uma Mai cike da koshin lafiya.

Da yake nasa jawabin, shugaban kwamitin Kwamret Aminu Abdussalam Gwarzo ya bada tabbacin kwamitin zai gudanar da aikin sa bisa gaskiya da rikon amana.

Wakilinmu na gidan gwamnati Ibrahim Muazzam Sani Dankaka ya rawaito cewa daga bisani gwamna Abba Kabir Yusuf ya rabawa wasu daga cikin wakilan kwamitin motoci da bubura masu kafa biyu domin su samu damar shiga lunguda da sako a jihar nan.

A wani cigaban kuma gwamna Abba Kabir Yusuf ya bada takardun shaidar kwarewa ga wasu masu maganin garjiya a jihar Kano.

Masu magnin da aka bawa shaidar sun hada Dr. Ibrahim Arab Dansokoto da Dr. Salihannur da Mal. Nasiru Sarki da sauran masu maganin da ga ciki da wajen birni Kano.

COV/IMS

Gwamnatin tarayya ta hannun ministar fasaha, al'adu da tattalin arziki, Hannatu Musa Musawa za ta samar da jarin $100bn ...
22/08/2024

Gwamnatin tarayya ta hannun ministar fasaha, al'adu da tattalin arziki, Hannatu Musa Musawa za ta samar da jarin $100bn ga 'yan ƙasa domin farfado da tattalin arzikin Najeriya

Yan bindiga sun sako ɗan sarkin Gobir wanda akayi garkuwa dashi da mahaifinsa, Alh. Isah Bawa Muhammad tun a kwanakin ba...
21/08/2024

Yan bindiga sun sako ɗan sarkin Gobir wanda akayi garkuwa dashi da mahaifinsa, Alh. Isah Bawa Muhammad tun a kwanakin baya.

Babban yayansa, Surajo Isa wanda ya tabbatarwa manema labarai a daren yau, yace dan uwan nasa ya dawo gida ne da misalin karfe takwas da rabi na daren yau.

Yace sai da aka biya makudan kudade da babura biyar ga yan bindinga kafin su sako shi.

Ya kuma bayyanawa manema labarai cewa yan bindigan ne s**a binne mahaifin nasu Alh. Isah Bawa Muhammad wanda ya mutu a hannun yan bindinga tun jiya talata.

YANZU-YANZU: A Ƙarshe Dai 'Yan Bindiga Sun Kashe Sarkin GobirYanzu muke samun labarin rasuwar Sarkin Gobir, da ƴan bindi...
21/08/2024

YANZU-YANZU: A Ƙarshe Dai 'Yan Bindiga Sun Kashe Sarkin Gobir

Yanzu muke samun labarin rasuwar Sarkin Gobir, da ƴan bindiga s**a sakin bidiyo, inda s**a ci zarafinsa, yanzu haka sun kashe shi bayan sun nemi kuɗin fansa.

Jam'iyyar NNPP me Mulki Jihar Kano tayi kira ga dukkanin masu sha'awar tsayawa takarar Shugabancin Ƙaramar Hukuma ko Kan...
20/08/2024

Jam'iyyar NNPP me Mulki Jihar Kano tayi kira ga dukkanin masu sha'awar tsayawa takarar Shugabancin Ƙaramar Hukuma ko Kansila, ƙarƙashin tutar jam'iyyarsu da suyi gaggawar ajiye mukaman gwamnati da suke riƙe dashi nan take ko kuma kafun ƙarshen watan nan na Augustan 2024.

Shugaban Jam'iyyar NNPP na Jihar Kano Hon Dr. Hashim Suleiman Dungurawa ne ya bayyana hakan ayayin wani taron manema labarai daya gudana a birnin Kano ayau Talata domin bayyana matsayar Jam'iyyarsu dangane da dokar Hukumar Zabe me zaman kanta ta Jiha KANSIEC.

Gwamnatin jihar kano tace zata samar da sabbin birane guda biyu, a kananan hukumomi Dawakin Kudu da Tofa domin rage cink...
19/08/2024

Gwamnatin jihar kano tace zata samar da sabbin birane guda biyu, a kananan hukumomi Dawakin Kudu da Tofa domin rage cinkoso a cikin birnin Kano.

Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da takardun biyan diyya ga masu gonakin a gwamnatin ta karba a garin, Lambu, Yar gaya, Rigiyar Gwangwan da kuma Unguwar Rimi.

Gwamnan yace za a bada filoti dubu, 2,483 a Yar gaya da kuma filoti 1,671 ga masu filotai a kananan hukumomin, Dawakin Kudu da Tofa.

Menene ra' ayinku dangane da samar da birane?

A binciken da na yi kan harƙallar Novomed, tabbas gwamna bai san “Ministry of Local Government” ta ba da kwangilar ba ha...
18/08/2024

A binciken da na yi kan harƙallar Novomed, tabbas gwamna bai san “Ministry of Local Government” ta ba da kwangilar ba har sai da Dan Bello ya fitar da bayani.

Kwamishinan ma’aikatar, wanda shi ne mataimakin gwamna, shi ne wuƙa shi ne nama a harkar. Watakil saboda hukuncin “Supreme Court” da ta ba wa ƙananan hukumomi cin gashin kan su, sai ciyamomi da “deputy governor” su ka yi amfani da damar su ka yi gaban kansu.

Duk wanda ya san yadda gwamnati ke wakana, zai gane cewa akwai zummar yin babakere da kuɗin al’umma duk lokacin da ka ga ƙananan hukumomi sun fitar da kuɗi bai-ɗaya kuma a lokaci ɗaya.

Duk da cewa tabbas gwamna bai sani ba, maganar a nan ita ce duk abin da ya faru a gwamnati dole jama’a du ɗora wa gwamna laifi, domin shi su ka zaba a matsayin shugaba. Kuma Allah zai tuhume shi akan yadda ya bari wasu ma’aikatu na gudanar da ayyukan su ba tare da sa ido ba.

Irin wannan wasarere Shugaba Buhari ya yi ministoci su ka riƙa ninke dukiyar al’umma.

Jafar Jafar ✍️

DA DUMI DUMINSA: farashin Man Fetir Lita Ɗaya  Zai koma 600 Zuwa 650 NNPC, Farashin Man Fetur Zai Iya Faduwa Zuwa Naira ...
13/08/2024

DA DUMI DUMINSA: farashin Man Fetir Lita Ɗaya Zai koma 600 Zuwa 650 NNPC, Farashin Man Fetur Zai Iya Faduwa Zuwa Naira 600 Kan Kowacce Lita

‘Yan kasuwar man Najeriya sun yi nuni da cewa matatar man Dangote za ta iya rage farashin man fetur tsakanin Naira 600 zuwa 650 kan kowace lita, ya danganta da farashin da take hakowa.

Hammed Fashola, mataimakin shugaban kungiyar dillalan man fetur ta kasa mai zaman kanta ne ya bayyana hakan a ranar Litinin.

Kalaman na Fashola na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa matatar ta dala biliyan 20 ba za ta fara hako mai ba kamar yadda shugaban rukunin Dangote Aliko Dangote ya yi hasashen tun a tsakiyar watan Agustan 2024.

Fashola ya lura cewa matatar mai da ke Legas na fuskantar babban kalubale wajen samar da danyen mai. Ya yi nuni da cewa farashin man fetur a hukumance da kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya kayyade a halin yanzu yana kan Naira 570 ga kowace lita, Yayin da gidajen man da masu zaman kansu ke sayar da su a kusan Naira 700 kan kowace lita.

Ya kuma jaddada cewa da zarar man Dangote ya samu, Farashin man famfo zai iya raguwa zuwa tsakanin N600 zuwa N650 kowace lita.

Idan dai ba a manta ba, a makon da ya gabata ne matatar mai ta Dangote da hukumar kula da Harkokin man fetur ta Najeriya ta tafka rikici a kan batun rabon gangar Danyen mai Miliyan 26.

Address

Kano

Telephone

+2348037539570

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Daginawa Media News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Daginawa Media News:

Share