Aminchi Tv

Aminchi Tv Daga Malaman Mu
Is An Online Page aim to brings educative clips of Islamic clerics, latest news updates, and more..
(1)

07/08/2026

Wakar kungiyar ƙare hakkin bil'adama ta global community for human rights network Nigeria

05/08/2026

DA DUMI DUMI:Yadda wasu fusatattun matasa s**a bankawa motar jami'an Hukumar KAROTA, wuta a Kwanar Dawaki, bisa zargin jami'an da haddasa haɗari.

Mai Zaku Ce?

31/07/2026

Wanna waka a zatan ku wa Rarara yake nufi da ita

Rundunar Anti-Phone Snatching Force ta k**a mutane 8 kan zargin su da sha da dillancin kayan maye a Kano.Rundunar tsaro ...
31/07/2026

Rundunar Anti-Phone Snatching Force ta k**a mutane 8 kan zargin su da sha da dillancin kayan maye a Kano.

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan daba da ƙwacen waya da kuma daƙile ta'ammali da kayan maye, ta Anti-Phone Snatching Force a Kano, ta k**a mutane Takwas a filin wasa na Mahaha, bisa zargin su da sha da dillancin kayan maye.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, Ibrahim Garba Ahmad, ne ya sanar da hakan yayin zantawar sa da manema labarai a ranar Laraba 29 ga Yuli, 2026.

Ya ce bayan samun rahoton sirri ne kan yadda ake hada-hadar ƙwayoyi da dillancin sauran kayan maye a wasu ɓangarori na cikin filin wasa na Mahaha, kwamandan rundunar Nura Salisu Sharaɗa, ya umarce jami'an sa ƙarkashin jagorancin DC Abduljalal Sa'id Muhammad, s**a halarci wajen.

"Lokacin da jami'an mu s**a je wajen sun tarar da yadda ake hada-hadar ƙwayoyi da Madarar Sukudayin da Sholisho, inda s**a farmake su, masu tarin kayan mayen s**a tsere, sai dai sun k**a mutane Takwas da s**a je sayen kayan maye," in ji shi.

Ibrahim Garba Ahmad ya ƙara da cewa, wannan na zuwa ne a ci gaba da faɗaɗa sintirin su na shiga lungu da saƙo na jihar Kano, wajen zaƙulo masu sha da dillancin kayan maye, a salon aikin nan nasu na "Damisa Ƙi Sabo" domin ɗaukar mataki a kan duk wanda aka k**a da wannan laifi.

Da suke jawaban su daban-daban, mutanen da ake zargin sun bayyana nadamar su bisa yadda aka k**a su lokacin da s**a je sayen kayan mayen a filin wasa na Mahaha da ke Ƙofar Na'isa a Kano.

Ya ce bayan da s**a k**a mutanen bakwai ne Kwamandan rundunar ta Anti-Phone Snatching Force a Kano, Nura Salisu Sharaɗa ya yi umarni aka kai mutanen ga hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA, reshen jihar Kano.

Nura Salisu Sharaɗa ya kuma gargaɗi ɓata garin da suke addabar jama'a da harkokin faɗan daba, da ƙwacen waya da shaye-shayen kayan maye, da su daina kasancewar duk wanda ya zo hannun su na zai ji da daɗi ba.

31/07/2026

An k**a barawan babur na makocin sa

31/07/2026

Wata budurwa ta na neman mijin aure

31/07/2026

Jawabin Ɗan Tik-tok CP ontop, kan yadda ya zargi ƴan sandan Ja'oji da cin zarafin sa cikin dare a Kano.

24/07/2026

DA DUMI-DUMI: Jirgin Enugu Air Ya Kauce Daga Titin Sauka Bayan Zai Sauka A Filin Jirgin Sama Na Benin

Fargaba ta mamaye fasinjoji da ma'aikatan filin jirgin sama a ranar Alhamis bayan wani jirgin kamfanin Enugu Air ya kauce daga titin sauka (runway) bayan ya sauka lafiya a Filin Jirgin Sama na Benin, Jihar Edo.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da ake ruwan sama mai ƙarfi, wanda ake zargin ya sa jirgin ya yi zamewa ya fita daga titin saukar jirage. Duk da firgicin da lamarin ya haifar, babu wani fasinja ko ma'aikacin jirgin da ya ji rauni.

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta bayyana cewa wannan ba haɗarin faɗuwar jirgi ba ne, illa dai jirgin ya kauce daga titin sauka sak**akon yanayin mummunan ruwan sama. Haka kuma, kamfanin Enugu Air ya tabbatar da cewa an fitar da dukkan fasinjoji da ma'aikatan jirgin cikin aminci, yayin da hukumomin da abin ya shafa s**a fara bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin.

24/07/2026

Yadda Wani Jami'in Ɗansanda me suna Amos Friday, yake Cin kasuwar tsaye inda yake Hana Direbobi wucewa mutukar basu bashi naira dubu biyu a matsayin na goro ba.Ya k**ata hukumar Yansanda ta dauki mataki a kansa

Yanzu idan aka bai wa Amos Friday, 5k ko kayan laifi aka dauko se a wuce kenan ? Ku bamu amsa a comment

24/07/2026

A'isha humaira matar Dauda kahutu Rara ta fito taɓawa sanata Barau jibirin maliya Da magoya bayan sa hakuri kan abinda magoya bayan su suke yi

Mai Zaku Ce?

Address

13th Street. 47 W 13th St, New York, NY
Kano
10011

Telephone

+2348064850438

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Aminchi Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Aminchi Tv:

Shortcuts

Share