10/09/2026
A wani mataki na ƙara hanzarta aiwatar da manufofin ci gaban gwamnatinsa da zurfafa sauye-sauyen hukumomi, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani (CON), ya naɗa ƙwararrun mutane zuwa wasu muƙamai masu muhimmanci a gwamnatin jihar.
Waɗanda aka naɗa sun haɗa da Ben Kure, Kwamishinan Ci gaban Wasanni; Amina Akilu Dalhat, Kwamishiniyar Ayyuka na Musamman I; Abdullahi Garba Abbas, Kwamishinan Ayyuka na Musamman II; da Dr. Halliru Soba, Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Gwamna mai kula da harkokin gudanarwa.
Gwamna Uba Sani ya kuma naɗa sababbin mambobin wasu muhimman kwamitocin hukumomin jihar.
Waɗanda aka naɗa sun haɗa da Alhaji Munir Jafaru, Shugaban Hukumar Kula da Lafiya ta Jihar Kaduna; AVM Bashir Gamagira Saidu, Shugaban Hukumar Kaduna Vigilance Service; Mai Shari’a Gideon Isa Kurada (mai ritaya), Shugaban Kwalejin Ilimi ta Gidan Waya; Esther Bago, Shugabar Cibiyar Horar da Sana’o’i da Bunƙasa Ƙwarewa; Dr. Yusuf Aliyu Bature, Shugaban Hukumar Kula da Samar da Kayayyakin Asibitocin Kaduna; da Engr. Namadi Musa, Shugaban Hukumar Kula da Hanyoyin Karkara ta Kaduna.
Gwamnatin ta ce waɗannan naɗe-naɗe an yi su ne domin hanzarta aiwatar da manufofin sauyi na gwamnatin Uba Sani, inganta ayyukan hidimar jama’a, da kuma samar da ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.
Yayin da yake taya sabbin waɗanda aka naɗa murna, Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa an zaɓe su ne bisa la’akari da ƙwarewarsu, amincinsu da kuma jajircewarsu wajen gudanar da ayyuka.
Gwamnan ya buƙace su da su kawo sabbin dabaru da ra’ayoyi wajen gudanar da ayyukansu, su guji sakaci ko nuna gamsuwa da abin da aka riga aka cimma, tare da tabbatar da cewa sun yi cikakken aiki bisa hangen nesan gwamnatinsa na gina Jihar Kaduna mai sauyi da juriya wajen fuskantar ƙalubale.
Ya kuma yi musu fatan samun shiriya da jagorancin Allah a sabbin muƙaman da aka ɗora musu.
Ibraheem Musa
Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Kaduna
10 ga Satumba, 2026