Kibiya Online Radio

  • Home
  • Kibiya Online Radio

Kibiya Online Radio Online Radio Broadcasting Kibiya Kano State.

MAYK EXPRESS ONLINE RADIO KIBIYA KANO STATE.       RAHOTO NA CEWAHukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) a jihar...
11/11/2023

MAYK EXPRESS ONLINE RADIO KIBIYA KANO STATE.

RAHOTO NA CEWA
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) a jihar Bayelsa ta tabbatar da cewa wani jirgin ruwa ɗauke da malaman zaɓe da kayan aiki ya kife a ƙaramar hukumar Ijaw ta kudu da ke jihar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun shugaban sashen hulɗa da jama’a da wayar da kan al’umma na hukumar a jihar ta Bayelsa, Inec ta ce malaman zaɓen na kan hanyarsu ce ta zuwa rumfar zaɓe ta Koluama.

Sai dai sanarwar ta ce an yi sa’a babu ko ɗaya daga cikin malaman zaɓe 12 da ke cikin jirgin ruwan da ya rasa ransa.

Amma ta ce kayan zaɓe, kamar takardar rubuta sakamako da sauran kayan malaman zaɓen sun salwanta a cikin ruwa.

Inec ta ce duk da haka za ta yi ƙoƙarin ganin an gudanar da zaɓe a yankin.

An sace malamin zaɓe

Haka nan sanarwar ta ci gaba da cewa an sace wani malamin zaɓe da aka tura mazaɓar Ossioma da ke ƙaramar hukumar Sagbama a jihar ta Bayelsa.

Ta ce an sace mutumin ne sa'ilin da yake jiran jirgin ruwan da zai shiga zuwa inda aka tura shi, a tashar jiragen ruwa ta Amassoma.

Inec ta ce an sanar da jami'an tsaro game da ɓacewar jami'in nata.

𝗠𝗔𝗬𝗞 𝗘𝗫𝗣𝗥𝗘𝗦𝗦 𝗢𝗡𝗟𝗜𝗡𝗘 𝗥𝗔𝗗𝗜𝗢 𝗞𝗜𝗕𝗜𝗬𝗔 𝗞𝗔𝗡𝗢 𝗦𝗧𝗔𝗧𝗘.    🕛𝗧𝗔𝗥𝗘 𝗗𝗔 𝗠𝗨𝗞𝗛𝗧𝗔𝗥 𝗔𝗨𝗪𝗔𝗟 𝗬𝗔𝗥𝗢 𝗞𝗜𝗕𝗜𝗬𝗔.𝗬𝗔𝗨 𝗠𝗨𝗡𝗔 𝗟𝗔𝗛𝗔𝗗𝗜 01-10-2023 .🕛👁️An gur...
01/10/2023

𝗠𝗔𝗬𝗞 𝗘𝗫𝗣𝗥𝗘𝗦𝗦 𝗢𝗡𝗟𝗜𝗡𝗘 𝗥𝗔𝗗𝗜𝗢 𝗞𝗜𝗕𝗜𝗬𝗔 𝗞𝗔𝗡𝗢 𝗦𝗧𝗔𝗧𝗘.
🕛
𝗧𝗔𝗥𝗘 𝗗𝗔 𝗠𝗨𝗞𝗛𝗧𝗔𝗥 𝗔𝗨𝗪𝗔𝗟 𝗬𝗔𝗥𝗢 𝗞𝗜𝗕𝗜𝗬𝗔.
𝗬𝗔𝗨 𝗠𝗨𝗡𝗔 𝗟𝗔𝗛𝗔𝗗𝗜 01-10-2023
.🕛
👁️An gurfanar da ɗaukacin gwamnonin Najeriya 36 ƙara a gaban kotu.
SERAP ta maka gwamnonin ƙara ne kan kuɗaɗen tallafin man fetur da s**a karɓa daga hannun FG.
SERAP na neman a tilasta gwamnonin bayyan yadda s**a yi da kuɗaɗen da s**a karɓa.

👁️Kotun Amurka ta umarci a ba Atiku damar ganin takardun shaidar digirin Tinubu. Atiku ya tafi kotu, inda yace bai gamsu Tinubu yayi digiri a Amurka ba.
An kai ruwa rana yayin da Tinubu ya nemi a hana Atiku ganin takardun.

👁️Shugaba Tinubu zai taimaki talakawa da kudaden rage radadi.
Ya fadi lokacin da zai fara rabawa mutum miliyan 15 kudade. Ya kuma yi alkawarin jin ta talakawa duk sadda lamurra s**a taso.

👁️Wani ɗalibin jami'ar FUDMA da ke jihar Katsina ya rasa ransa.
ya rasu ne bayan taƙaddama ta ɓarke tsakaninsa da abokansa kan wata budurwa. Jami'an ƴan sanda sunyi caraf da ɗaliban da ake zargi da hannunsu a rasuwar ɗalibin.

🔊Abdullahi Adamu ya ce bai yi nadama ba kan nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2023.
Tsohon shugaban na APC ya bayyana cewa ya ji daɗi da Tinubu ya gaji Buhari a mulkin ƙasar nan.
Abdullahi Adamu dai yayi murabus ne jim kaɗan bayan Tinubu ya zama shugaban ƙasa.

🔊Shugaba Tinubu yace ya kamata 'yan Najeriya su zama masu juriya.
Yace dole za a sha kebura kafin ya iya gyara kasar nan yadda ya kamata.
'Yan Najeriya naci gaba da karbar kebura tun bayan cire tallafin man fetur.

🔊Kotun suararen kararrakin zabe a jihar Sokoton Najeriya, ta tabbatar da nasarar gwamna Ahmad Aliyu na jam'iyyar APC. Kotun dai tayi watsi da karar da jam'iyyar adawa ta PDP ta shigar da ke kalubalantar zaben na shekarar 2023.
𝗠𝗮𝘀𝘂 𝘀𝗮𝘂𝗿𝗮𝗿𝗼 𝗮𝗻𝗮𝗻 𝗺𝘂𝗸𝗮

03/09/2023

Saura Mako daya gwamnatin shugaba Tunubu da ta gwamnonin Najeriya su cika kwana 100 akan mulki.

Yaya kwana 100 na farkon mulkin Shugaba Tunubu yake a wajenku ?sannan a wanne ma'auni kuka dora gwamnan garinku a cikin kwana 100 yana jagorantar jihar da kuka fito .

Zamu karanto ra'ayoyinku a labarnmu da Radio da Talabijin .

A kyuata Lafazi🙏🏻

KIBIYA ONLINE RADIO KANO STATE   MAI GABATARWA ASHIRU GAMBO TAKUR.*Gwamnan Kano ya naɗa Engr. Yakubu Umar  Mai Ɗauko Rah...
03/09/2023

KIBIYA ONLINE RADIO KANO STATE

MAI GABATARWA ASHIRU GAMBO TAKUR.
*Gwamnan Kano ya naɗa Engr. Yakubu Umar Mai Ɗauko Rahoto na Musamman daga Ma'aikatar Yaɗa Labarai jihar kano.

*Gwamnan Kano ya naɗa Abdullahi I. Ibrahim da aka fi sani da Kwankwason Twitter a Babban Mai Taimaka Masa Kan Sabbin Hanyoyin Sadarwa na Zamani.

*Gwamnan Kano ya naɗa Nanu Kankarofi a Mai Ɗauko Rahoto na Musamman daga Ma'aikatar Ƙasa.

*Gwamnatin jihar Kano za ta kafa Cibiyar ba da horo akan ayyukan samar da ruwa domin magance matsalar rijiyoyin burtsatse a jihar kano.

*Manajan Daraktan Hukumar Samar da Ruwa a karkara da Tsafta ta jahar kano Alh. Shamwilu Abdulkadir Isa Gezawa ya bayyana haka a cikin wani shiri na musamman kai tsaye a gidan rediyon Aminci dake nan Kano.
Yace cibiyar za ta rika horar da mutanen da zasu shiga aikin gyaran rijiyoyin burtsatse da famfuna domin dogaro da kansu a sana'o'in tare taimakawa al'umma, Alh. Shamwilu Abdulkadir Gezawa ya bayyana cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince hukumar ta gyara rijiyoyin burtsatse Dubu Daya da Dari Biyar (1,500) a fadin jihar kano Kafin ta fara gina sababbin rijiyoyin.
Ya bukaci mutane su kare ayyukan da Gwamnati ta samar musu tare da kokarin gyara su da kansu domin amfanin su.
Manajan daraktan RUWASA ya kara da cewa shirin wayar da kan jama’a akan samar da ruwa da tsafta da yaki da yin bahaya a waje a kananan hukumomi takwas na da nufin tabbatar da kare lafiyar al'umma.
Kananan hukumomin da ake aiwatar da shirin sun hada da Rano da Albasu da Ajingi da Gezawa da Rimin Gado da Karaye da Kuma Kura.
Daga nan sai yayi kira ga al’ummar jihar nan su marawa manufofin gwamna Abba Kabir Yusuf baya domin ci gaban jihar kano baki daya.
Gwamnatin jahar kano ta yi alkawarin sake gina gadar Sitti zuwa Zamba dake karamar Hukumar Sumaila.
Kwamishinan ma'aikatar raya karkara da cigaban al'umma Ambasada Hamza Safiyanu Kachako ya bayyana haka a ganawarsa da al'ummar yankin a ofishinsa.
Amba

BREAKING NEWS
14/08/2023

BREAKING NEWS

12/07/2023

𝗞𝗜𝗕𝗜𝗬𝗔 𝗢𝗡𝗟𝗜𝗡𝗘 𝗥𝗔𝗗𝗜𝗢 𝗞𝗔𝗡𝗢

Newly Jigawa State Commisioners and their Portfolio:
-
1. Ibrahim Babangida Umar = Budget & Economic planning.
2. Prof. Hannatu Sabo Muhammad = Finance
3. Dr. Muhammad Abdullahi Kainuwa = Health.
4. Aminu Kanta = Commerce and industry.
5. Ahmed Garba MK = Local government.
6. Ibrahim Garba Hannun Giwa = Water resources
7. Dr. Lawan Yunusa Danzomo = Basic Education.
8. Dr. Isah Yusuf Chamo : High Education.
9. Sagir Musa Ahmed = Information.
10. Hadiza Abdulwahab = Woman Affairs
11. Col. Muhammad Alhassan (rtd) = Land and regional plannig
12. Dr. Nura Ibrahim Dandoka = Environment.
13. Engr. Gambo Shu’aibu Mallam = Works.
14. Auwal Danladi Sankara = Special Duties.
15. Musa Adamu Aliyu = Justice
16. Muttaka Namadi = Agric

11/07/2023

𝐊𝐈𝐁𝐈𝐘𝐀 𝐎𝐍𝐋𝐈𝐍𝐄 𝐑𝐀𝐃𝐈𝐎 𝐊𝐀𝐍𝐎
.
𝐘𝐀𝐔 𝐌𝐔𝐍𝐀 𝐓𝐀𝐋𝐀𝐓𝐀 11-07-2023.
𝐓𝐀𝐑𝐄 𝐃𝐀 𝐀𝐒𝐇𝐈𝐑𝐔 𝐆𝐀𝐌𝐁𝐎 𝐓𝐀𝐊𝐔𝐑.

Shugaba Bola Tinubu ya yi sabon nadin mukami daga dawowarsa daga Guinea Bissau.
Tinubu ya nada Dada Olusegun a matsayin mashawarci na musamman kan kafafen sada zumunta.
Olusegun sanannen mai goyon bayan jam'iyyar APC ne a kafafen sada zumunta.

# Ministocin Tinubu! Yayin da ake ta hankoron jiran jerin sunayen ministocin Shugaba Tinubu, alamu sun fara bayyana wadanda ke ciki.
Ta tabbata cewa tsohon gwamnan jihar Enugu na jam'iyyar PDP, Ifeanyi Ugwanyi ya samu shiga jerin sunayen ministocin.
Bayan Ugwuanyi, ana sa ran 'yan jam'iyyar adawa da dama ka iya shiga jerin sunayen ministocin da ake tsammani.

# Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mayar da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa kan kujerarsa.
Daurawa yace ya sake karbar shugabancin hukumar Hisbah ta Kano a karo na biyu saboda ya ga cewa da gaske gwamnati mai ci take za ta yi aiki.
Shehin malamin yace abun da zasu fi mayar da hankali a kai yanzu shine auren zawarawa.

. Hon. Femi Gbajabiamila da tsofaffin Gwamnoni su ka tarbo Bola Ahmed Tinubu a tashar jirgin sama.
Mai girma shugaban Najeriyan ya na tare da su tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
Jama’a sun huro wuta, su na kira ga Tinubu cewa ka da ya ba Dr. Ganduje mukami a gwamnatinsa.

jam’iyyar adawa ta PDP ta kira taron gaggawa a Abuja.
Kungiyar gwamnonin PDP za su yi wata ganawa a Abuja domin tattauna halin da kasar ke ciki a hannun gwamnatin APC.
Za kuma a yi sulhu tsakanin manyan ‘ya’yan jam’iyyar da s**a raba gari tun bayan zaben fidda dan takarar shugaban kasa.
𝗄𝖺𝗋𝗌𝗁𝖾𝗇 𝗍𝖺𝗄𝖺𝗂𝗍𝖺𝗍𝗍𝗎𝗇 𝗅𝖺𝖻𝖺𝗋𝖺𝗂 𝗒𝖺𝗆𝗆𝖺
𝖺 𝗆𝖺𝖽𝖺𝖽𝗂𝗇 𝖾𝖽𝗂𝗍𝗈𝗋 𝗆𝖺𝗋𝗒𝖺𝗆 𝗎𝗌𝗆𝖺𝗇 𝗌𝖺𝗋𝗄𝗂, 𝖺𝗌𝗁𝗂𝗋𝗎 𝗀𝖺𝗆𝖻𝗈 𝗄𝖾 𝖼𝖾𝗐𝖺 𝖻𝗂𝗌𝗅𝖺𝗆.
@𝖪𝖨𝖡𝖨𝖸𝖠 𝖮𝖭𝖫𝖨𝖭𝖤 𝖱𝖠𝖣𝖨𝖮

𝗞𝗜𝗕𝗜𝗬𝗔 𝗢𝗡𝗟𝗜𝗡𝗘 𝗥𝗔𝗗𝗜𝗢 𝗞𝗔𝗡𝗢 𝗦𝗧𝗔𝗧𝗘𝗕𝗥𝗘𝗔𝗞𝗜𝗡𝗚 𝗡𝗘𝗪𝗦 𝗙𝗘𝗗𝗘𝗥𝗔𝗟 𝗨𝗡𝗜𝗩𝗘𝗥𝗦𝗜𝗧𝗬 𝗗𝗨𝗧𝗦𝗘.
26/06/2023

𝗞𝗜𝗕𝗜𝗬𝗔 𝗢𝗡𝗟𝗜𝗡𝗘 𝗥𝗔𝗗𝗜𝗢 𝗞𝗔𝗡𝗢 𝗦𝗧𝗔𝗧𝗘
𝗕𝗥𝗘𝗔𝗞𝗜𝗡𝗚 𝗡𝗘𝗪𝗦

𝗙𝗘𝗗𝗘𝗥𝗔𝗟 𝗨𝗡𝗜𝗩𝗘𝗥𝗦𝗜𝗧𝗬 𝗗𝗨𝗧𝗦𝗘.

25/06/2023
Gwamnatin Jihar Kano Za Ta Sake Fasalin Kasuwannin Kano Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ba da tabbacin g...
25/06/2023

Gwamnatin Jihar Kano Za Ta Sake Fasalin Kasuwannin Kano

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ba da tabbacin gwamnatinsa na shirin sake fasalin kasuwannin Kano ta hanyar daukar kowa da kowa.

Gwamnan ya kuma yi alkawarin samar da sahihin wakilci na ‘yan kasuwa a kwamishinonin sa, inda ya kara da cewa kwamishina zai fito daga cikinsu da sauran mukamai da za su baiwa al’umma kyakkyawan wakilci.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran gwamnan Hisham Habib, ta ce gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da ‘yan kasuwa a lokacin da ya karbi bakuncinsu a gidan gwamnati.

A cewar sanarwar gwamnatin mai ci za ta bunkasa harkokin kasuwanci a jihar tare da tabbatar wa yan kasuwar kudirinsa na tallafawa hanyoyin kasuwanci na zamani musamman ta fasahar zamani.

Gwamnan ya kuma shaidawa ‘yan kasuwar shirin sake fasalin kasuwannin Kano tare da tafiya da kowa.

Ya ce gwamnati za ta kuma rage cunkoso a birnin ta hanyar bude sabbin wuraren kasuwanci, ya kuma bukaci matasan ‘yan kasuwa da su yi amfani da wannan damar dan bunkasa cigaban Kano..

20/06/2023

KIBIYA ONLINE RADIO KANO STATE
BREAKING NEWS TODAY.
.
A yau ne Talata Wanda jaridar Alfijir Labarai ta rawaito, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sake turawa majalisar dokokin jihar Kano sunayen mutane 19, da yake son na dawa kwamishinoni
Cikakkun jerin sunayen da Gwamna ya aika wa majalisar domin neman mukamin kwamishinoni sune:
1- Comrade Aminu Abdulsalam
2- Hon. Umar Doguwa
3- Hon. Ali Haruna Makoda
4- Hon. Abubakar Labaran Yusuf
5- Hon. Danjuma Mahmoud
6- Hon. Musa Shanono
7- Hon. Abbas Sani Abbas
8- Haj. Aisha Saji
9- Haj. Ladidi Garko
10- Dr. Marwan Ahmad
11- Engr. Muhd Diggol
12- Hon. Adamu Aliyu Kibiya
13- Dr. Yusuf Kofar Mata
14- Hon. Hamza Safiyanu
15- Hon. Tajo Usman Zaura
16- Sheikh Tijjani Auwal
17- Hon. Nasiru Sule Garo
18- Hon. Haruna Isa Dederi
19- Hon. Baba Halilu Dantiye
Sauran bayanai na nan tafe…

Dauke da rahotanni.
ONLINE RADIO KANO STATE.

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kibiya Online Radio posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Kibiya Online Radio:

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share