20/07/2025
Kabiru Haske ya fice daga jam'iyyar PDP, yayin da ya rubuta takardar ficewar zuwa ga Shugaban Jam'iyyar PDP a mazabar Ganye II.
A cikin wasikar tasa Kabiru Chiroman Haske ya rubuta cewa "Ina so in sanar da hukuma cewa na ajiye mukamina na kasancewa memba a jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) daga yau.
Wannan matsaya ta biyo bayan dogon tunani na kaina da kuma shawarar da na yanke tare da shuwagabanni daban-daban a matakai daban-daban na shugabanci. Kafin in yanke wannan hukunci, na samu damar ganawa da Mai Girma Gwamna Ademola Adeleke, wanda ya nuna girmamawa da goyon baya sosai ga ra’ayina da manufofina na siyasa. Kaskantar da kai da niyyarsa na gaskiya wajen jagoranci sun kara tabbatar min da darajar wannan tafiya, kuma ina matukar godiya da wannan karamci.
Kabiru Haske ya Kara da cewa "A tsawon shekaru, na bayar da gudummawa ta bangaren tasiri, kuzari, da lokaci na ga jam’iyyar PDP, ina aiki kafada da kafada da mutane da gungun da ke da kishin cigaba da ci gaban kasa. Ina alfahari da irin aikin da muka aiwatar tare da kuma dangantaka mai kyau da na samu a cikin wannan tafiya.
Don haka, ina rokon ku da ku karɓi wannan wasiƙa a matsayin rubutacciyar takardar saukewa daga jam’iyyar, tare da sabunta bayanan da s**a shafe ni a cikin kundin jam’iyyar.
Na gode ƙwarai da goyon bayan ku.