New Africa Hausa OnlineTv

New Africa Hausa OnlineTv Ku kasance tare da tashar New Africa Hausa da bibiyar shafukan mu na zumunta don kasancewa tare da mu

Yanzu mace sai ta zaɓi ayi mata kishiya da bi ta cikin wannan lungu ta fita....Amma shin da gaske ne kuwa...?
27/06/2026

Yanzu mace sai ta zaɓi ayi mata kishiya da bi ta cikin wannan lungu ta fita....

Amma shin da gaske ne kuwa...?

Hanyar Abuja tayi tsayuwar gwamin jaki.!Tun daga JERE har gaban kauyen GADAJARA iya ganin idon dan Adam cunkoso manya da...
25/05/2026

Hanyar Abuja tayi tsayuwar gwamin jaki.!

Tun daga JERE har gaban kauyen GADAJARA iya ganin idon dan Adam cunkoso manya da ƙananan motoci ne dauke dandazon matafiya amma hanyar ta tsaya cak, tun karfe 6 na safe na baro cikin Abuja awa 4 amma bamu yi tafiya kilo mita 50 ba.

Malam Abul-Banāt

Innalillahi wa inna ilaihi rajiu'n... Jarumar fina-finan Hausa na Kannywood Wasila Isma'il ta rasu, kamar yadda makusant...
24/05/2026

Innalillahi wa inna ilaihi rajiu'n...

Jarumar fina-finan Hausa na Kannywood Wasila Isma'il ta rasu, kamar yadda makusantanta s**a tabbatar.

Makusantan marigayiyar sun ce ta rasu ne a jihar Kaduna da safiyar yau Lahadi bayan fama da rashin lafiya, inda ta bar ƴaƴa hudu - mata uku da namiji ɗaya.

Kotu ta daure tsohon ministan wutar lantarki ta Najeriya Saleh Mamman na tsawon shekaru 75 a gidan yari bisa zargin almu...
13/05/2026

Kotu ta daure tsohon ministan wutar lantarki ta Najeriya Saleh Mamman na tsawon shekaru 75 a gidan yari bisa zargin almundahana ta kuɗi Naira biliyan 33.8.

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke wa tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman, daurin shekaru 75 a gidan yari bayan samunsa da laifukan da s**a shafi zamba da kuma karkatar da kudade da s**a kimanin Naira biliyan 33.8.

Kotun karkashin jagorancin mai shari’a James Omotosho, ta samu tsohon ministan ne da laifin kunshin tuhume-tuhume har guda 12 da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa (EFCC) ta shigar.

A hukuncin da kotun ta yanke, kotun ta bayar da umarnin a ci gaba da gudanar da bincike tare da zartar hukunce-hukunce a jere, wanda hakan ke nufin cika umarnin kotu na wa'adin gidan yari, sai dai a cikin kunshi wasu tuhume-tuhume da aka yi masa kotu tace zai biya tarar Naira miliyan 10.

Ana dai kallon wannan hukunci a matsayin daya daga cikin manyan mafi munin laifukan cin hanci da rashawa da aka samu wannan tsohon minista da aikatawa a cikin 'yan shekarun nan.

Me zaku ce...?

LABARI MAI DAUKE DA TAQADDAMA: Budurwa Ta Nuna Sha’awarta Ga “Abun Al’ajabin Zazzau”Wata matashiya mai suna Fatima Hassa...
13/05/2026

LABARI MAI DAUKE DA TAQADDAMA: Budurwa Ta Nuna Sha’awarta Ga “Abun Al’ajabin Zazzau”

Wata matashiya mai suna Fatima Hassan ta jawo hankalin mutane a kafafen sada zumunta bayan bayyana cewa tana da cikakkiyar niyyar auren Mahmud Sadis Buba, wanda aka fi sani da “Abun Al’ajabin Zazzau”.

Matashiyar, wacce ta bayyana hakan a shafinta na sada zumunta, ta ce ta dade tana sha’awar samun miji na gari, amma yanzu ta ga lokaci ya yi da za ta bayyana wanda zuciyarta ke muradi.

A cewarta, duk da matsin lambar da wasu ke mata kan batun aure, ta yanke shawarar tsayawa kan zabinta, tana mai cewa Mahmud Sadis Buba ne wanda take gani ya dace da ita a matsayin abokin rayuwa.

Ta kuma bayyana cewa aure ba wai sai mutum mai tarin dukiya ko wata babbar gata ba, illa fahimta da hakuri tsakanin ma’aurata. A cewarta, za ta iya rayuwa da duk abin da Allah Ya h**e musu cikin soyayya da juna.

Lamarin dai ya haifar da cece-kuce da ra’ayoyi mabanbanta a tsakanin jama’a, inda wasu ke yaba mata da jajircewa da bayyana ra’ayinta ba tare da tsoro ba.

Ku kuwa, wace fata za ku yi mata?

Alhamdulillah!!"Muna miƙa saƙon jinjina da godiya ga Mai Girma Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, bisa amincewa da ƙari...
13/05/2026

Alhamdulillah!!

"Muna miƙa saƙon jinjina da godiya ga Mai Girma Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, bisa amincewa da ƙarin albashin fansho ga masu ritaya na jiha da ƙananan hukumomi. Wannan babban namijin ƙoƙari ne da ke nuna kulawa, tausayi da karrama waɗanda s**a sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa jihar hidima.

Haƙiƙa wannan aiki abin tarihi ne da ba a taɓa ganin irinsa ba a Jihar Zamfara, kuma zai taimaka matuƙa wajen rage wa masu ritaya raɗaɗin rayuwa tare da inganta walwalarsu. Allah Ya ƙara wa Mai Girma Gwamna lafiya, hikima da nasara wajen ci gaba da gudanar da mulki nagari".

Nura Suraj Gusau
Special Adviser
Human Capital Development

How could be this happen again.Not every mistake is a mistake. This was not a mistake, it was done intentionally. Enough...
13/05/2026

How could be this happen again.
Not every mistake is a mistake. This was not a mistake, it was done intentionally. Enough is enough. We cannot quit on this matter, and the federal government must provide compensation to the families of the victims.

They did it for innocent maulud people
They did it in village market in maiduguri
Now zamfara
Cc
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
General CG Musa
Dr Bello Matawalle
Dauda Lawal
Nigerian Senate
House of Representatives, Republic of Nigeria
NSA - National Security Agency

Abdulmalik Lamido Abagus

Shirin ANA WATA GA WATA na isar muku da sakon Abdulmalik Lamido Abagus Bisa Rahoton Jaridar The Sun wanda ya bayyana cew...
13/05/2026

Shirin ANA WATA GA WATA na isar muku da sakon Abdulmalik Lamido Abagus

Bisa Rahoton Jaridar The Sun wanda ya bayyana cewa Sojojin Najeriya sunyi sanadin salawantar rayukan wasu mutane har su 70 a jahar

"Ta yaya hakan ke sake faruwa da maimaituwa...?

Ba kowane kuskure ne kuskure ba.!!!

Wannan ba kuskure ba ne, an yi shi da gangan ne, To hakika ya isa ya isa haka. Ba za mu iya yin watsi da wannan batu ba, kuma dole ne gwamnatin tarayya ta biya diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa.

Sun yi wa masu mauludi marasa wa'yanda basu da laifin komai irin wannan a wata kasuwar kauye a maiduguri, ga shi yanzu sun sake yi a Zamfara".

Kuma kuyi tagging na New Africa Hausa OnlineTv domin isar da naku sakwanni ga Hukumomi, Kamfanoni, Ƙungiyoyi, Ma'aikatu, 'Yan kasuwa da Masana'antu.

DA DUMI-DUMI: Kotu ta samu tsohon Ministan Wutar Lantarki na lokacin Buhari, Saleh Mamman da laifin almundahanar kuɗiBab...
07/05/2026

DA DUMI-DUMI: Kotu ta samu tsohon Ministan Wutar Lantarki na lokacin Buhari, Saleh Mamman da laifin almundahanar kuɗi

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta samu tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, da laifin almundahanar kuɗi.

Mai shari’a James Omotosho ne ya yanke hukuncin bayan ya same shi da laifi a kan dukkan tuhume-tuhume guda 12 da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta shigar a kansa.

Kotun ta bayyana cewa EFCC ta gabatar da hujjoji masu gamsarwa da s**a tabbatar da laifin tsohon ministan ba tare da wata shakka ba.

Saleh Mamman ya taba zama Ministan Wutar Lantarki a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari daga ranar 21 ga watan Agustan 2019 zuwa 1 ga watan Satumban 2021, kafin a cire shi daga mukaminsa yayin garambawul din majalisar ministoci.

Ana sa ran samun karin bayani kan hukuncin da kuma matakin da kotu za ta dauka a gaba.

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Masud Kurfi, Auwal Haruna Lowel Haruna, Basheer Hassan Su...
06/05/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Masud Kurfi, Auwal Haruna Lowel Haruna, Basheer Hassan Suleiman, Mustapha Abdulkareem Abubakar, مدثرمحمد محمدعثمان, Mubarak Nasir, Abdullahi Lawali, Nuraddeen Y Randagi, Jabir Aminu Aliyu, Abdullahiisakogi Kantama

Address

Kano
700231

Opening Hours

Monday 06:00 - 21:00
Tuesday 06:00 - 21:00
Wednesday 06:00 - 21:00
Thursday 06:00 - 21:00
Friday 06:00 - 18:00
Saturday 06:00 - 18:00
Sunday 06:00 - 21:00

Telephone

+2349078780740

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when New Africa Hausa OnlineTv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to New Africa Hausa OnlineTv:

Shortcuts

Share