
21/09/2025
Shugaban Hukumar NAHCON da Tawagarsa Zasu Tafi Saudiyya Don Kammala Shirye-shiryen Hajjin 2026
Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da cewa Shugabanta, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, tare da wasu kwamishinoni da sakataren hukumar, Dakta Mustapha M. Ali, zasu tafi kasar Saudiyya a ranar Litinin, 22 ga Satumba, 2025.
Ziyarar na da nufin kammala yarjejeniyoyin da ake yi da masu yiwa alhazai hidima a Saudiyya, musamman kan harkokin sansanoni alhazai a Mina da Arfat, da sufuri da kuma masauki, domin tabbatar da shirye-shirye tun kafin lokacin gudanar da Hajjin shekarar 2026.
Hakan na zuwa ne bisa ga jadawalin da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta fitar, wanda ya kayyade cewa daga ranar 6 zuwa 23 ga Satumba, 2025 (15–29 Safar 1447H) za a kammala saka hannu a kan yarjejeniyar da biyan kuɗin farko na sansanonin Hajji. Haka kuma an sanya ranakun 23 zuwa 24 ga Satumba, 2025 (1–2 Rabi’ul Awwal 1447H) a matsayin wa’adin ƙarshe na yin kammala yarjejeniyar kan muhimman ayyuka irin su sufuri da masauki.
A cewar sanarwar, Ma’aikatar ta kuma bayyana ranar 12 ga Oktoba, 2025 (20 Rabi’ul Thani 1447H) a matsayin wa’adin ƙarshe na shigar da bayanan alhazai da kuma rabonsu cikin rukuni ta hanyar manhajar Nusuk.
Daga ɓangaren Najeriya kuwa, NAHCON ta saka ranar 8 ga Oktoba, 2025 a matsayin ƙarshe ga hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi da kamfanonin hajji masu lasisi su mika kuɗaɗen hajjin 2026.
Hukumar ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki su yi biyayya da waɗannan wa’adin domin gudanar da shirye-shiryen Hajji cikin sauƙi tare da tabbatar da nasarar aikin Hajji ga alhazan Najeriya.